Rikicin Ukraine: Trump ya goyi bayan mamayar Rasha a Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana umarnin Vladimir Putin na tura sojoji cikin Ukraine a matsayin farar dabara.
Da yake magana a wani shirin rediyo, Mista Trump ya ce ba karamar dabara bace, yadda Mista Putin ya kira sojojin da ya tura yankunan a matsayin masu wanzar da zaman lafya.
Mista Trump ya ce ya yi imanin Amurka za ta iya amfani da ta ta rundunar wanzar da zaman lafiyar irin ta Rasha domin kare kan iyakarta da ke kudanci.
A shekara ta 2014 ne kasashen Donetsk da Luhansk suka fara shelanta 'yancin kai jim kadan bayan da Rasha ta mamaye yankin kudancin Crimea na Ukraine.
Ukraine da kawayenta na Yamma sun sha zargin Rasha da tayar da tarzoma tare da aikewa da makamai da mayaka zuwa ga 'yan tawayen, wadanda a yanzu ke rike da yankuna da dama da ake kira Donbas.
Moscow ta sha musanta zargin.
Wakilin BBC a Ukraine ya ce matakin ya zuwa yanzu ba shi ne cikakken harin da mutane da yawa ke fargaba ba, amma ya nuna wani gagarumin ci gaba na rikicin da ke da hadari.







