Da gaske hukumar FBI ta wanke Abba Kyari daga zarginsa a kan Hushpuppi?

Raymond 'Hushpuppi da Abba Kyari

Labarin da ke iƙirarin an wanke shahararren dan sandan Najeriya Abba Kyari da ke fuskantar tuhumar rashawa a Amurka ya mamaye shafukan sada zumunta a ƙasar.

Labarin wanda aka fi yaɗa wa a kafar WhatsApp ya ambaci hukumar bincike ta FBI a Amurka da ke cewa "ba a tuhumar DCP Abba Kyari.

"An ambaci sunansa ne kawai amma ba a tuhumarsa da aikata zamba kuma babu wani laifi da ake tuhumarsa," in ji sanarwar da ake ta yaɗawa a kafofin sada zumuntar.

BBC ta yi bincike domin tabbatar da gaskiyar labarin, ko da gaske ba a tuhumar babban jami'in na ƴan sandan Najeriya.

Kuma binciken da BBC ta gudanar ta gano cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin domin babu wata sanarwa da ta fito daga rundunar ƴan sandan Najeriya da ke tabbatar da hakan.

Haka kuma hukumar bincike ta FBI ta Amurka ba ta wallafa wani sabon bayani ba da ya ambaci Abba Kyari ko kuma batun wanke shi daga zargin alaƙarsa da matashin ɗan Najeriya da ke fuskantar tuhuma a Amurka bisa hannu a manya-manyan ayyukan zamba na duniya Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Ko da yake jami'in ɗan sandan na Najeriya, Abba Kyari ya musanta karbar rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas, amma an dakatar da shi daga muƙaminsa.

Abin da muka sani?

Sashen shari'a na Amurka ya ce ya kama wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da suka taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1.

Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli, ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet.

Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin kama takwaransa Kelly Chibuzo Vincent, mai shekara 40 da haihuwa.

Bayanin sashen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da suka yi masa.

"A cewar sanarwar, Abba Kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa kama Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas.

"Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan kama Vicent tare da tasa ƙeyarsa gidan yari,"kamar yadda bayanin kotun ya bayyana.

Wasu labaran masu alaƙa

Martanin Abba Kyari

Abba Kyari

Asalin hoton, @Abba Kyari

Jami'in ɗan sandan na Najeriya Abba Kyari ya musanta zargin yana cewa bai karɓi ko sisi ba daga Hushpuppi.

Abba Kyari ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: "Wani jami'in ɗan sanda ya tabbatar da cewa Hushpuppi ya tuntuɓe shi - amma ba gaskiya ba ne cewa an yi wa Vicent barazanar mutuwa.

Kyari ya ce daga baya ƴan sanda sun saki Vicent bayan bincikensu ya tabbatar da ba shi da laifi.

"Abokai: Abbas wanda muka fi sani da Hushpuppi ya kira ofishinmu kamar shekara biyu baya, yana cewa wani mutum a Najeriya yana masa barazanar cewa zai kashe masa iyali, ya kuma aiko lambar waya yana cewa don Allah mu yi wani abu kafin wannan mutum ya kashe masa iyali.

"Mun bi diddigin wanda ake zargi bayan gudanar da bincike mun gano cewa babu wanda yake wa wani barazana, kuma ya ce su biyun abokai ne tun da daɗewa amma sai suka samu matsala a kan kudi.

"Daga baya muka ba da belin wanda ake zargi.

"Babu wanda ya nemi naira ɗaya daga wajen Hushpuppi. Abin da muka mayar da hankali akai shi ne mu ceci rayuwar mutane," in ji Abba Kyari.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Tun faruwar wannan lamari kawunan ƴan Najeriya ya rabu, inda mutane suke bayyana mabambantan ra'ayoyi.

Wasu na ganin sharri ne aka yi wa Abba Kyari tare da maƙala masa wannan abu da a ganinsu bai dace da shi ba, musamman ganin cewa shi ɗin haziƙin ɗan sanda ne da ya yi fafutuka sosai ta wajen gano masu laifi.

A hannu guda kuma wasu na ganin babu ko tababa kan wannan zargi da ake yi wa Abba Kyari, inda har suke cewa "a Najeriya dai kowace gauta ja ce," wato ma'ana babu mamaki don an samu mutum irin Abba Kyari da wannan laifi da ake zarginsa.

Sai dai akwai waɗanda suka tsaya a tsakiya, wato masu jajantawa Abban, amma kuma duk da haka suna cewa ya kwantar da hankalinsa a yi bincike, idan har ba shi da laifi suna da tabbacin FBI za ta yi masa adalci.

Idan kuma an same shi da laifi to dama bawa ba ya wuce ƙaddararsa kamar yadda masu wancan ra'ayi ke faɗa.