Hushpuppi: Da gaske Abba Kyari ya karɓi rashawar $1.1m daga hannun ɗan damfarar?

h
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan wata dambarwa da ta barke tsakanin matashin ɗan Najeriya da ke fuskantar tuhuma a Amurka bisa hannu a manya-manyan ayyukan zamba na duniya Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi da kuma shahararren dan sanda Abba Kyari kan zargin bayar da cin hanci.

Ana dai zargin Hushpuppy ne da zambatar manyan kafanonin da ƙungiyoyin kwallon ƙafa da kuma ɗaidaikun mutane a ƙasashensu na fadin duniya.

Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taɓa bai wa jami'in ɗan sanda Abba Kyari wasu kuɗaɗe domin a daure wani abokin huldarsa. Zargin da Kyari ya musanta.

Menene gaskiyar bai wa Abba kyari rashawa?

Jami'in ɗan sanda Najeriya, Abba Kyari ya musanta karba rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas.

Sashen shari'a na Amurka ya ce ya kama wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da suka taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1.

Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli, ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet.

Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin kama takwaransa Kelly Vicente mai shekara 40 da haihuwa.

Bayanin sahsen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da suka yi masa.

"A cewar sanarwar, Abba kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa kama Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas.

"Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan kama Vicent tare da tusa keyarsa gidan yari,"kamar yadda bayanin kotun ya bayyana.

Amma Abba Kyari ya musanta zargin yana cewa bai karbi ko sisi ba daga Hushpuppi.

Martanin Abba Kyari

A

Asalin hoton, POLICE

Bayanan hoto, Abin da muka mayar da hanakli akai shi ne mu ceci rayuwar mutane," in ji Abba Kyari.

Zargin da ake yi wa Abba Kyari ya biyo bayan bayanan da Hushpuppi ya gabatar wa kotu a wani bangare na hujjojin da aka bayyana na zambar da ya yi.

Da yake mayar da martani kan wannan zargi, Abba Kyari ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce: "Wani jami'in ɗan sanda ya tabbatar da cewa Hushpuppi ya tuntube shi - amma ba gaskiya ba ne cewa an yi wa Vicent barazanar mutuwa.

Kyari ya ce daga baya ƴan sanda sun saki Vicent bayan bincikensu ya tabbatar da ba shi da laifi.

"Abokai: Abbas wanda muka fi sani da Hushpuppi ya kira ofishinmu kamar shekara biyu baya, yana cewa wani mutum a Najeriya yana masa barazanar cewa zai kashe masa iyali, ya kuma aiko lambar waya yana cewa ɗan Allah mu yi wani abu kafin wannan mutum ya kashe masa iyali.

"Mun bi diddigin wanda ake zargi bayan gudanar da bincike mun gano cewa babu wanda yake wa wani barazana, kuma ya ce su biyun abokai ne tun da dadewa amma sai suka samu matsala a kan kudi. Daga baya muka ba da belin wanda ake zargi.

"Babu wanda ya nemi naira ɗaya daga wajen Hushpuppi. Abin da muka mayar da hanakli akai shi ne mu ceci rayuwar mutane," in ji Abba Kyari.

Wannan layi ne

Abin da Amurka ta ce kan Hushpuppi

A wata sanawarwa muƙadashin baban alkalin Amurka, Tracy Wilkinson ya ce Hushpuppi ya aikata damfarar dala miliyan 24.

Daga ciki akwai wanda ya aikata ta sama da dala miliyan 1.1 kan wani mutum da yake son kai yaransa makaranta a Qatar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa Hushpuppi da tawagarsa sun yi kutse a shafin intanet din makaranta da "karbe kuɗaɗensa ta hanyar adireshin boge na biyan kuɗi".

Sannan sun bai wa wani "jami'in ƙetare cin hanci domin ya taimaka musu wajen cimma manufarsa ta damfara".

Hushpuppi wanda ya taka muhimmiyar rawa a damfara, na rayuwar ƙasaita irin ta hamshakai ta hanyar "kuɗaɗe da yake samu ta haramtattun hanya tare da muƙarabansa".

Kristi Johnson na hukumar FBI a Amurka, ta shaida cewa Hushpuppi ya kasance "ɗaya daga cikin kasurgumin mai damfara a duniya".

Rayuwarsa ta fitaccen attajiri ta ba shi kafa wajen kula alaƙa da kamfanoni halatattu wanda hakan ya taimaka masa wajen samun damar hanyoyin damfara daban-daban a Amurka da sauran ƙasashen ƙetare", a cewarta.

Amsa laifin da ya yi a wannan lokaci zai kasance baban "koma baya ga sauran abokan damfarasa a duniya".

Sammaci

A yanzu dai wata kotu a Amurka ta bayar da umarnin kamo mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriyan Abba Kyari.

Sanarwar da kotun ta fitar tace ta bai wa sashen bincike na ƙasar umarnin kamo Kyari tare da gurfanar da shi a Amurka bisa rawar da ya taka a zambar da Raymond Abbas ya yi da abokan cin mushensa.

Wannan layi ne

Rayuwar Hushpuppi

h

Asalin hoton, INSTAGRAM/HUSHPUPPI

Hushpuppi mai shekara 37, an san shi sosai ta hanyar hotunan rayuwarsa da yake yi ta bushasha wadda yake sanya wa a shafinsa na Instagram inda yake da mabiya 2.5m.

Wani bayanin kotu ya ce Hushpuppi ya damfari mutane kudi da suka kai dalar Amurka miliyan 24, kwatankwacin fan miliyan 17.

A wata harkalla, Hushpuppi ya yi kokarin sace wa wani mutum sama da dala miliyan 1.1 wanda ya so ya kafa wata sabuwar makarantar yara a Qatar, in ji sanarwar.

A wannan makon kuma ta ambato cewa ya amince da laifukan da ya tafka wadanda aka zarge su da shi a ranar 20 ga watan Afrilu.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Sanarwar ta ce tsakanin 18 ga watan Janairun 2019 zuwa 9 ga watan Yunin 2020, Hushpuppi da abokan harkallarsa sun yi koarin cutar mutane masu yawa tare da halasta kuɗaɗen haram da kuma kwashe kuɗi daga banki a duk faɗin duniya.

Sun kara da cewa zai fuskanci zaman gidan yari har na tsawon shekara 20, kuma ya biya duk abin da ya cuci mutane.

An kama Hushpuppi ne a Dubai inda ya ke zaune a watan Yunin 2020.