DCP Abba Kyari: Abin da ke faruwa da ɗan sandan izina ce ga sauran 'yan sanda – CP Mohammed Wakili

Abba Kyari

Asalin hoton, Facebook/Abba Kyari

Bayanan hoto, An dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin ɗan sanda har an sai an gama binciken zargin cin hanci a kansa
Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da hukumomi suka ɗauki matakin dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin ɗan sanda bisa zargin karɓar cin hanci 'yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu, ciki har da tsofaffin jami'an rundunar.

Tsohon Kwamishinan 'Yan Sanda CP Mohammed Wakili ya faɗa wa BBC cewa halin da ofisan ya tsinci kansa "ya kamata ya faɗakar da 'yan baya su san cewa akwai gobe ta duniya kuma akwai gobe ta lahira".

Kafin yanzu, abu ne sananne cewa ɗan sanda Abba Kyari mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP) kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT) na shan yabo kan yadda yake yaƙi da gawurtattun 'yan fashi a Najeriya, har ma ake yi masa laƙabi da "ɗan sanda na musamman".

Abba Kyari na da mabiya fiye da 445,000 a dandalin Facebook da kuma wasu 78,000 a Instagram, inda ya saba bayyana kusan dukkan ayyukansa - na gida da na ofis.

Sunan babban jami'in ɗan sandan mai shekara 46 ya shiga wani hali ne a makon da ya gabata bayan wasu takardun kotu a Amurka sun zarge shi da karɓar cin hanci daga hannun Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi. Sai dai Kyari ya musanta zargin cikin wannan sanarwar.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) na tuhumar Hushpuppi - wanda shahararre ne a shafukan sada zumunta - da zargin damfarar mutane da kamfanoni kuɗin da suka kai dala miliyan 24.

Duk da cewa Abba Kyari ya musanta zargin, hakan bai hana Hukumar Kula da Harkokin 'Yan sanda ta Najeriya ta dakatar da shi ba, tana mai cewa sai an kammala bincike.

'Izina ce ga sauran 'yan sanda'

CP Wakili

Cikin wata hira da BBC Hausa, CP Mohammed Wakili ya bayyana cewa matakin da hukumar 'yan sanda ta ɗauka na dakatar da Kyari shi ne mafi dacewa "saboda shi ma [Abba Kyari] ya samu adalci".

"Shi wannan lamari na Abba Kyari zai iya zama gaskiya, zai kuma iya yiwuwa cewa wani ne ba ya son sa ya samu dama yake neman ya gama da shi - Allah kaɗai ya sani.

"Saboda haka wannan binciken da za a yi shi ne zai tabbatar [gaskiya ko akasin haka]. To su 'yan baya su sani cewa akwai gobe ta duniya kuma akwai gobe ta lahira, ko me za ka yi ka yi gaskiya. An ce duk mai gaskiya yana tare da Allah, Allah kuma ba ya barin bawansa."

Ko za a yi adalci a binciken?

CP Wakili
Bayanan hoto, CP Mohammed Wakili ya yi kwamishinan ɗan sanda a jihohin Najeriya da dama ciki har da Jihar Kano

IGP Usman Alkali ya kafa kwamati na mutum huɗu ƙarƙashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari.

CP Wakili ya ce za a yi adalci saboda miliyoyin mutane suna sa ido kan batun "kuma suna sane da duk abin da ake yi saboda samuwar shafukan sada zumunta."

A cewarsa: "Za a yi adalci mana, ai mutanen kirki ba sa ƙarewa yallaɓai. Babu wani abu da za a yi a ɓoye, kuma kowa ya gyara ya sani.

"In an yi gaskiya an sani, in ba a yi gaskiya ba kowa ya sani saboda ilimi ya yawaita. Mutane da yawa na da sha'awa kan wannan matsala kuma suna sa ido.

"Ka ga kuwa idan ba a yi adalci ba za a ɗauri kashi ko kuma a ɓata igiya."

Tsawon wane lokaci aka dakatar da Abba Kyari kuma yaushe ta fara aiki?

Abba Kyari

Asalin hoton, Facebook/Abba Kyari

Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda ta ɗauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli.

"Matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka [FBI] ke yi masa," a cewar sanarwar.

Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ɗaukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.