Abubakar Dadiyata: 'Ba karamin tashin hankali muke ciki ba tun da aka sace mijina'
- Marubuci, Abdulbaki Jari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da mahaifa da iyalin Dadiyata:
Mahaifa da iyalan matashin nan dan jihar Kaduna, Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata, sun ce suna cikin tashin hankali tun bayan sace shi.
A ranar biyu ga Agustan 2019 ne aka bi shi har gidan dai-dai lokacin da ya dawo daga tafiya inda aka sace shi da motarsa.
'Yan uwansa sun ce sun ziyarci ofishin jami'an 'yan sandan farin kaya da sauran hukumomi wadanda suka ce ba ya hannunsu.
A wata tattaunawa da suka yi da BBC Hausa a Kaduna, mahaifa da kuma mai dakin Dadiyata sun ce tun da aka sace shi har yanzu babu wanda ya gan shi ko ya ji labarinsa.
Sun yi roko ga duk wanda ya kama shi da ya taimaka ya sake shi.
"Ba karamin tashin hankali muke ciki ba tun da aka sace shi," in ji mai dakinsa, Khadija.
Abokin aikinmu, Abdulbaki Jari, ya ziyarci gidan su Dadiyata a Kaduna inda ya tattauna da mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa da kuma kawunsa - wanda tun lokacin da aka sanar da shi cewa an sace Dadiyata ya yanke jiki ya fadi kuma rabin jikinsa ya shanye.
Ko akwai labari game da inda Dadiyata yake?
Mahaifiyarsa, Malama Fatima Abubakar, ta ce "har yanzu babu wani labari game da shi".
Mahaifinsa, Malam Danjuma Yero, ya shaida mani cewa sun bibiyi hukumomi da dama, sun yi rubuce-rubuce kuma sun nemi alfarma amma har yanzu babu wani bayani game da shi ko wani wanda ya fito ya gaya masu inda yake.
Mahaifiyarsa ta ce "a da mahafinsa ba ya barin wayarsa tana kwana a kunne, amma tun ranar da aka sace Dadiyata ya ke barin wayar a kunne yana sa ran za a kira a ce masa ga Abubakar ya dawo"
Matarsa Khadija Ahmad Lame ta ce "kullum ina sa rai In sha Allahu wata rana zai dawo", amma har yanzu babu labari. Kullum da daddare idan aka taba kofar shiga gidan sai ta ji kamar shi ne ya dawo.
Ko iyayen gidan Dadiyata na siyasa suna kula da iyalinsa?

Asalin hoton, Dadiyata
Matarsa Khadija ta shaida min cewa "Daga farko muna samu kuma suna nuna mana kulawa sosai. Ba zan ce yanzu ba ma samu ba, amma ba kamar daga farko ba."
Ita kuma mahaifiyarsa ta ce "Da dumi-dumi dai sun dunga zuwa. Amma daga baya sun kwana biyu ba su zo ba."
Daga farkon abin da ya faru dai 'yan siyasa da dama sun nuna damuwarsu inda suka ziyarci iyalinsa suka suka rika yin magana da mahukunta domin gano inda yake.
Matasa 'yan uwansa na shafukan sada zumunta na Kwankwasiyya sun shirya addu'o'i da dama domin Allah ya bayyana shi.
Matarsa ta ce a yanzu ma wat ace ke amfani da layinsa na waya. A da tana kiran layin, amma da aka fada sai ta daina.
Yaya lafiyar 'yan uwansa?
Har yanzu dai kawunsa, Yahaya Usman, wanda samun labarin dauke Dadiyata ya sa ya yanke jiki ya fadi kuma rabin jikinsa ya shanye, yana nan yana fama da jiki.
Dana tambaye shi game da Abubakar sai ya fara kuka maganarsa na hardewa ya ce mani "Allah Ya bayyana shi a duk inda yake". Har yanzu yana nan zaune a kujerar guragu, sai an dauki shi sannan a kai shi daki ko a fitar da shi.
Mahaifinsa kuma ya ce kodayaushe idan ya tuna da shi yana yin kuka. Ya ce suna daurewa ne saboda mahaifiyar Dadiyata tana fama da hawan jini, sai ya sa ba su so suna yin abin da zai daga mata hankali.
Matarsa Khadija ta ce karamar 'yarsa kullum tana kuka tana tambaya ina mahaifinta yake? Ta ce wani lokacin sai dai ta rarrashe ta ta nuna mata hotonsa ta ba ta hakuri.
Mahaifiyarsa ta ce a kwanakin baya karamar 'yarsa ba su mamaki domin tana ta kuka sai ta ga mahaifinta. Da aka bai wa kanin Dadiyata suka yi magana sai ta sake fashewa da kuka ta ce ba wannan ba, ita "Abbanta take nema."
Fatan ilansa
"Fatana ai kullum ba zai wuce in gan shi an sako shi ya dawo ba," a cewar mahaifiyarsa.
Mahaifinsa ya ce "Addu'a muna nan muna yin ta, dare da rana, safe da yamma. Muna yi, muna sa 'yan uwa suna yi. Muna sa sauran almajiran da muke tare da su suna addu'a Allah Ya kubutar mana... da wannan yaro a duk inda yake. Kuma duk inda yake Allah Ya sa yana cikin aminci.
Wannan addu'o'in da muke yi kenan. Amma ina roko da wanda ya san inda yake da wanda ya san halin da yake ciki, da wanda ya sa aka yi, da wanda ya yi, da wanda ke tare da shi, muna rokonsu don Allah don son Annabi Muhammad SAW a yi hakuri a yafe ma shi wannan al'amari."
Matarsa ta ce " muna rokon duk wanda yake da iko, da wanda zai iya... da wanda ke da hannu ko halin da zai iya, su taimaka mana, su tausaya mana da yaran shi... da iyayen shi da 'yan uwa duka da abokan arziki, su tausaya mana su dawo da shi.
Har yanzu muna sa rai. Ba mu taba fidda rai a kanshi ba. Kullum muna sa rai wata rana in sha Allahu zai dawo."
Wane ne Dadiyata?
Asalin sunansa Abubakar Idris, sunan mahaifinsa Danjuma Yero, mahaifiyarsa kuma Fatima Abubakar. Ana kiransa Daddy a gida saboda yana da sunan kakansa na wajen mahaifiyarsa. Abokansa kuma suna kiransa Dadiyata.
Matashi ne wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman ma a Twitter inda yake da dubunnan mabiya.
Shi malamin Jami'ar Dutsan-ma ne da ke jihar Katsina kafin a sace shi.
Abubakar jigo ne cikin tafiyar Kwankwasiyya kuma a nan ne yafi yin suna saboda yana kare muradun tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso.
Abubakar kuma mutum ne mai tsokaci a shafukan sada zumunta inda a wasu lokuta yakan soki ayyukan wasu shugabannin siyasa da masu mulki.
Dadiyata kuma uba ne ga 'ya'ya mata biyu, karamar tana wata takwas aka sace shi. Miji ne ga Khadija Ahmad Lame.
Ta yaya aka sace Dadiyata?
Matarsa ta ce ya dawo gida ne daga tafiya da misalain karfe 12:30 a ranar 2 ga watan Agusta. Daidai lokacin da ya shigo gida da motarsa sai wasu mutane suka biyo shi a baya inda suka kama shi da kokowa suka sanya shi cikin motar tasa suka yi gaba da shi.
Ta ce ta daga labula a lokacin da al'amarin ke faruwa inda ta gansu sanye da takunkumin rufe fuska.
A cikin daren ta yi kokarin kiran mahaifansa amma bata same sub a, sai yayarsa ta samu ta shaida masu halin da ake ciki. Ita kuma tun da Asuba ta je gidan ta sanar da su halin da ake ciki.
Hakan ya sanya matasa da dama wadanda suka san shi a shafukan sada zumunta suka fito da maudu'in kamar #FreeDadiyata da #WhereIsDadiyata? Da dai sauransu domin daga murnarsu da kira ga mahukunta da a gano inda yake.












