Abubakar Dadiyata: 'Kullum na tuna shi hawaye ne ke zubo mini'

Bayanan bidiyo, Mahaifiyarsa ta bayyana cewa sace shi ya "tada masu hankali kwarai"
    • Marubuci, Daga Abdulbaki Jari
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja

Mun soma wallafa wannan labari a watan satumba na 2019. Sai dai mun yanke shawarar sake buga shi ne ganin cewa shekara daya bayan dauke Dadiyata, babu wani abu da ya sauya:

A ranar 1 ga watan Agusta da dare, wasu mutane wadanda ba a san ko su wane ne ba suka je har gidansa da ke Kaduna a Najeriya suka dauke wani matashi mai suna Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

An dai dauke shi ne da misalin karfe 1:00 na dare inda aka yi awon gaba da motarsa.

Hakan ne ya sanya masu amfani da kafafen sada zumunta, inda Abubakar din ya yi fice suka fito da maudu'ai daban-daban kamar su #FreeDadiyata da #WhereIsDadiyata da sauran su.

Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Asalin hoton, TWITTER/ DADIYATA

Bayanan hoto, Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta na Twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Wasu na zargin cewa jami'an tsaron kasar ne suka dauke shi bisa la'akari da yadda yake sukar gwamnati, amma su sun musanta zargin.

Na yi tafiya takanas-ta Kano zuwa jihar Kaduna, inda na tattauna da mahaifansa da iyalinsa da kuma 'yan uwansa a kan lamarin da kokarin da ake yi na nemansa da kuma halin da suke ciki.

Yadda aka dauke Dadiyata

Bayan na sauka a jirgin kasa a unguwar Rigasa a Kaduna, kai tsaye na wuce gidan Dadiyata da ke unguwar Barnawa.

Dadiyata da mai dakinsa Khadija da diyarsu

Asalin hoton, FAMILY

Bayanan hoto, Dadiyata da mai dakinsa Khadija da diyarsu

Na iske mai dakinsa Khadija Ahmad Lame tare da 'ya'yansu guda biyu.

Matar Dadiyata da 'ya'yansa mata guda biyu

Asalin hoton, FAMILY

Bayanan hoto, Matar Dadiyata da 'ya'yansa mata guda biyu

Na fara ne da tambayarta yaya aka dauke Dadiyata?

"Bayan ya shigo gida yana waya, bai kashe motarsa ba, ban san me yake fada a waya ba, ban san kuma da wa yake waya ba har zuwa yanzu." a cewarta.

"Wasu sun biyo shi, sun shigo cikin gida, na daga labule na gansu. Amma ban san ko su wane ne ba." a cewar Khadija.

"Sun zo sun tafi da shi" a cewar mai dakin nasa.

Ta kuma shaida mini cewa lokacin da abin ya faru ta kira mahaifansa da yayansa Usman, amma ba ta same su ba sai dai yayarsa ce ta samu, wadda ita ta sanar da mahaifansa da safe.

Dadiyata yana karami

Asalin hoton, FAMILY

Bayanan hoto, Dadiyata yana karami

Yayansa Usman ya shaida mini cewa a cikin dabara aka sanar da mahaifiyarsu aukuwar lamarin domin tana fama da hawan jini.

Me sace shi ta haifar wa iyalinsa da 'yan uwansa?

Sakamakon samun labarin dauke Dadiyata baffansa mai suna Yahaya ya yanke jiki ya fadi, inda barin jikinsa na hagu ya shanye kuma maganarsa ta samu matsala.

Baffan Abubakar Dadiyata Yahaya Usman, wanda ya yanke jiki ya fadi kuma barin jikinsa na hagu ya shanye a lokacin da aka sanar da shi cewa an dauke dan yayansa.

Asalin hoton, Abdulbaki Jari Aliyu

Bayanan hoto, Baffan Abubakar Dadiyata Yahaya Usman, wanda ya yanke jiki ya fadi kuma barin jikinsa na hagu ya shanye a lokacin da aka sanar da shi cewa an dauke dan yayansa

Na samu tattaunawa da shi. Yana kuka ya ce mini "ina rokon hukuma da ta taimaka ta sako mini shi."

"Ana zuwa aka fada mani sai na ce inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" a cewar mahaifinsa Danjuma Yero.

Mahaifiyarsa ta bayyana cewa sace shi ya tada masu hankali kwarai.

" 'Ya'yansa kullum tambayata suke ina Abbansu," a cewar matarsa.

Dadiyata da wasu daga cikin 'yan ajinsu na makarantar Boko

Asalin hoton, FAMILY

Bayanan hoto, Dadiyata da wasu daga cikin 'yan ajinsu na makarantar boko

A cewar abokinsa Ibrahim Mu'azu, dauke shi da aka yi "ba karamin tashin hankali ba ne ga mu abokansa. Saboda ba mu san halin da yake ciki ba."

Me ya sa wasu ke zargin jami'an tsaro da kama shi?

Wasu na zargin jami'an tsaro ne suka dauke shi, sai dai kawo yanzu babu wasu kwararan hujjoji a kasa da za su tabbatar da hakan.

Sai dai jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ya shaida mini cewa ba ya hannunsu, kuma sun tuntubi sauran hukumomin tsaro wadanda suka shaida masu cewa ba ya hannunsu.

Haka zalika da na tuntubi kakakin hukumar DSS ya shaida mini cewa ba ya da wani labari a game da Dadiyata, amma idan ya samu zai tuntube ni.

Na farko

Ganin cewa wadanda suka zo din sun tafi da motarsa. Domin a yadda aka saba masu garkuwa da mutane ba sa tafiya da abin hawa.

An dauke Dadiyata ne a gidansa dake a Kaduna da misalin karfe daya na daren 1 ga watan Agusta

Asalin hoton, FAMILY

Bayanan hoto, An dauke Dadiyata ne a gidansa da ke Kaduna da misalin karfe daya na daren 1 ga watan Agusta

Wasu na ganin mota kamar wani nauyi ce ga masu garkuwa da mutane.

Don kafin su fita su je inda za su aje mutum za a iya kama su.

Ina aka kwana?

Har yanzu dai babu wanda ya fito ya ce Dadiyata na hannunsa.

Shekara guda kenan tun bayan sace Abubakar Dadiyata, amma har yanzu babu wani labarinsa.

Sai dai har zuwa wannan lokaci iyalinsa da 'yan uwansa na fatan zai dawo zuwa wurinsu nan ba da dadewa ba.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wurin yin garkuwa da mutane. Da yawan mutane sun fi so su hau jirgin kasa a yanzu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wurin yin garkuwa da mutane. Da yawan matafiya sun fi so su hau jirgin kasa a yanzu

Matsalar garkuwa da mutane domin kudin fansa da bacewar mutane ba gaira babu dalili na ci gaba da kamari a Najeriya musamman ma a yankin arewacin kasar.

Hukumomin sun bayyana cewa suna iya bakin kokarinsu domin ganin sun magance matsalar, amma har yanzu hakan na ci gaba da aukuwa.