Abubakar Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta ce ba ta san inda yake ba
Gwamnatin jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ba ta da hannu a bacewar matashin nan Abubakar Idris Usman wanda aka fi sani da dadiyata, shekara ɗaya bayan ɓacewarsa.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin. Kwamishinar Shari'a ta Kaduna, Aisha Dikko ta shaida wa BBC "mu bamu san (wata) maganarsa ba gaskiya, muma yadda kuka karanta a cikin jarida haka muka karanta.
Ba mu kai shi kotu ba kuma bamu sa a yi wani bincikensa ba, bamu san komai game da al'amarin nasa ba."
Ta ce a irin wannan yanayin, ana kai wa jami'an tsaro ƙara ne "kuma ina ji iyalinsa sun kai kara wajen jami'an tsaro su yi musu bincike, a kan binciken da 'yan sanda suka yi ne za a ɗauki mataki." in ji kwamishinar.
Game da matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka kan batun ɓatan Dadiyata kuwa, Aisha Dikko ta ce "'yan sanda ne suke bincike ba gwamnati ba, 'yan sanda sai sun fara bincike kafin gwamnati ta shiga maganar. 'Yan sanda suna bincike basu kawo wa ma'aikatarmu ba kan abin da suka gano."
Wasu da ba a san ko su waye ba ne suka yi awon gaba da Dadiyata da tsakar dare daga gidansa da ke birnin Kaduna a watan Agustan bara, kuma tun sannan ba amo ba labarin Dadiyata.
Kwamishinar ta kuma yi bayani game da wasu da gwamnatin Kaduna ta shigar da ƙara kansu, "mun kai su ƙara kan maganganun da suka yi ba gaskiya ba kuma waɗanda ke iya tado rigima a garin."








