Kwankwaso ya bukaci DSS su nemo Dadiyata

Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Asalin hoton, TWITTER/ DADIYATA

Bayanan hoto, Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta na Twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, da ta zurfafa bincike don gano matashin nan Abubakar Idris Dadiyata, wanda ya yi batan dabo bayan wasu mutane da ake zargi jami'an tsaro ne sun dauke shi daga gidansa.

A ranar 1 ga watan Agustan 2019 ne da daddare aka je har gidansa da ke Kaduna aka dauke Dadiyata, wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta wajen sukar gwamnatin jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Dadiyata ya kuma yi suna wajen goyon bayan kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya, wadda tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya assasa.

A wata hira da ya yi da 'yan jarida a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis da daddare, Sanata Kwankwaso ya ce batan Dadiyata abin damuwa ne matuka.

Ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi kokarin gano Dadiyata, wanda malamin jami'a ne a kasar, inda ya ce "muna fatan Allah ya bayyana shi cikin lokaci mafi kankanta."

"Muna nan muna ci gaba da tausayawa da jajanta wa iyayensa da iyalinsa da abokansa da dukkanin mutanen da suka shafe shi," in ji Kwankwaso.

Kwankwaso
Bayanan hoto, Kwankwaso ya ce yana fatan Allah ya bayyana Dadiyata cikin kankanen lokaci

Da ma dai 'yan kasar sun dade suna fafutikar ganin jami'an tsaro sun gano Dadiyata, inda aka kaddamar da kamfen a shafukan sada zumunta da zummar matsa lamba kan gwamnatin najeriya ta nemo matashin.

Mai dakinsa Khadija ta bayyana wa BBC Hausa yadda aka dauke shi da halin da suke ciki a yanzu.

Ta ce: "A ko da yaushe yaransa suna tambayata ina Abbanmu yake?

A farkon watan da muke ciki, hukumar tsaro ta DSS ta musanta rahotannin da ke cewa tana tsare da Dadiyata wanda ya yi batan dabo har yanzu ba a sake jin duriyarsa ba.

Hukumar DSS ta karyata labarin da ta ce wasu jaridun Najeriya sun wallafa cewa tana tsare da mutum kusan 50 kuma wadanda kuma take azabtar da su.

Sai dai har yanzu 'yan Najeriya basu gamsu da matakin da hukomomin tsaro suke dauka ba wajen gano matashin dan siyasar.