Kullum na tuna shi hawaye ne ke zubo mani – Mahaifin Dadiyata
Sama da kwana 45 tun bayan sace Abubakar Idris Dadiyata. BBC ta ziyarci gidansa, inda ta gana da mahaifansa da kuma iyalinsa.
Mai dakinsa Khadija ta bayyana yadda aka dauke shi da halin da suke ciki a yanzu. Ta ce: "a kodayaushe yaransa suna tambayata ina Abbanmu yake?
Mun kuma ji daga Baffansa, wanda ya yanke jiki ya fadi a daidai lokacin da aka fada masa cewa an dauke Dadiyata. Hakan ya yi sanadiyyar shanyewar rabin jikinsa na hagu.