Ba mu kama Dadiyata ba – DSS

Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Asalin hoton, TWITTER/ DADIYATA

Bayanan hoto, Dadiyata wani jigo ne a matasan shafin sada zumunta na Twitter wajen kare siyasar kwankwasiyya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta musanta rahotannin da ke cewa tana tsare da wasu 'yan Najeriya da suka hada har da matashi Abubakar IDRIS da aka fi sani da Dadiyata wanda ya yi batan dabo har yanzu ba a sake jin duriyarsa ba.

Hukumar DSS ta karyata labarin da ta ce wasu jaridun Najeriya sun wallafa cewa tana tsare da mutum kusan 50 kuma wadanda kuma take azabtar da su.

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar ya fitar Peter Afunanya, ta ce don wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da Dadiyata, ba zai zama dalilin da za a ce jami'an hukumar ba ne.

Sanarwar ta ce babu dalilin da zai sa DSS ta musanta wadanda ta kama ko take tsare da su idan har kuma ta kaddamar da samame har ta kai ga kama wani.

A ranar 1 ga watan Agusta da daddare wasu mutane wadanda ba a san ko su wane ne ba suka je har gidansa da ke Kaduna suka dauke Dadiyata wanda ya yi fice a kafofin sadarwa na intanet.

Batun sace shi ya ja hankali, inda aka samar da maudu'ai daban-daban kamar su #FreeDadiyata da #WhereIsDadiyata da sauran su.

Yanzu an shafe watanni da sace Abubakar Dadiyata, kuma har yanzu babu wani labarinsa.