Yadda murnar mutanen Gaza ta fara komawa ciki bayan ganin yadda gidajensu suka ɗaiɗaice

    • Marubuci, Rushdi Abu Alouf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent
    • Aiko rahoto daga, Istanbul
    • Marubuci, André Rhoden-Paul
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
  • Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da Falasɗinawa suke rububin shiga Gaza tare da murnar tsagaita wuta, da dama cikinsu murnar tana komawa ciki ne da zarar sun ga yadda gidajensu suka zama kufai.

A Jabalia da ke arewacin Gaza, inda nan sansanin ƴan gudun hijira mafi girma yake a zirin, hotuna da bidiyon da ƴan ƴankin suka fitar sun nuna yadda yankin ya zama babu komai sai baraguzai.

Bayan komawa al-Faluja da ke yankin Jabalia, Duaa al-Khalidi ta shaida wa BBC cewa, "na tsira ne da ƴaƴana mata biyu. A ƙarƙashin baraguzanan ginin akwai gawarwakin mijina da surukata bayan ginin ya faɗo ya danne su a ranar 9 ga Oktoba."

Matar mai shekara 28 ta ƙara da cewa, "babu abin da nake buƙata yanzu fiye da a ciro min gawarwakinsu, mu samu mu musu sutura cikin mutunci."

Sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia, wanda a da yake cike da Falasɗinawa 250,000, ya kasance inda sojojin Isra'ila suka tsanta hare-hare a lokacin yaƙin, inda aka kashe Falasɗinawa kusan 4,000, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana.

Wani ƙwararren mai ɗaga ƙarfe, wanda ya sha wakiltar mutanen yankin Falasɗinu a gasannin duniya, ya rasa mutum 10 daga cikin danginsa a yaƙin.

"Abun farin ciki yau bayan kusan kwana 100, na samu damar ziyartar ƙaburburan ƴanuwana na musu addu'a," in ji shi.

Ya wallafa wani bidiyo, wanda ke nuna yadda gidansu mai hawa uku ya ɗaiɗaice.

"A nan ne aka kashe mutanen da na fi ƙauna a zuciyata - ƙannai da yara da hanyar cin abincina. Yaƙin ya cinye duk wani abu da ke kawo mana farin ciki."

A kudancin birnin Khan Younis, an ga yadda mutanen yankin suke ta ɗaga hannu tare da ƙwarzanta mayaƙan Hamas da suka ratsa ta cikin garin.

Ƴansandan Hamas, sanye da kakinsu sun fito a wasu wuraren, bayan kwashe watanni suna ɓuya saboda fargabar hare-haren Isra'ila.

Wani mazaunin Gaza, Ahmed Abu Ayham, ya bayyana wa Reuters cewa birnin ya zama tamkar kufai.

A birnin, wanda masana suka ce ya fi kowanne fuskantar ragargaza, an ga Falasɗinawa suna ɗaga tutar ƙasar suna naɗa da wayoyinsu.

Amma a wurinsa, shi bai ga abun farin ciki ba, duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, wadda za ta taƙaita kashe mutane.

"Muna cikin jimami ne, yanzu lokaci ne da ya kamata mu riƙa rumgumar junanmu muna kuka," in ji shi.

An kuma ga wasu ƴan Gazan suna tafiya birnin Rafah na kudanci, kusa da bakin iyakar Masar.

Mohammed Suleiman ya shaida wa BBC cewa: "muna godiya ga Allah da samun labarin tsagaita wuta.

"Da yardar Allah, abubuwa za su sauya komai ya yi kyau, kuma za mu koma Rafah. Ina fata duk wani wanda ya bar gidansa zai koma lafiya."

Mutane da dama sun tsere daga birnin ne bayan Isra'ila ta buƙace su da hakan saboda za su fara aiki a birnin da ke kudancin Gaza.

A Rafah, Muhammad al-Jamal, wanda ɗanjarida ne da ke aiki da jaridar Al-Ayyam ta yankin Falasɗinu ya bayyana yadda aka tarwatsa su, "komai ya zama baraguzai," in ji shi.

An samu nasarar cimma yarjejeniyar ce bayan lokacin da aka ɗauka ana tattaunawa, wanda ya jawo ƙarin kwana uku daga ranar da aka yi tsammani, inda a ɗan tsakankakin aka kashe Falasɗinawa 19, a wani hari da Isra'ila ta ce ta kai kan "ƴanta'adda."

A yammcin ranar ne Hamas ta saki mata guda uku cikin fursunonin yaƙi 33 da ke hannunsu da za su saka a matsayin matakin farko na tsagaitar wutar, wanda za a ɗauki mako shida ana yi.

Sai dai mutanen Gaza sun fargabar zai a iya samun matsala wajen tabbatar da yarjejeniyar.