Waiwaye: Martanin Najeriya ga Tchiani, da harin soji a Sokoto

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Babu gaskiya a zargin da shugaban sojin Nijar ya yi wa Najeriya - Ribadu

Malam Nuhu Ribaɗu

Asalin hoton, NUHU RIBADU

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗu, ya nuna takaicinsa kan wasu zarge zarge, da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdulrahman Tchiani ya yi yayin hirarsa da kafar talabijin ɗin kasar ranar Laraba.

Shi dai Janar Tchiani ya zargi Najeriya da ba ƙasar Faransa haɗin kai wajen bai wa ƴan bindiga mafaka da kuma ƙoƙarin kafa sansani a arewacin Najeriya, don shirya yadda za su far wa ƙasarsa.

To sai dai a hirarsa da BBC Hausa, mai ba Shugaban Najeriyar shawara kan sha'anin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya ce dukkan waɗannan maganganu ba su da tushe, ballantana makama, kuma Najeriya ba za ta taɓa yi wa Nijar zagon ƙasa ko ta bari wata masifa ta auka mata ba.

Ya ce ''Ko Ingila da ta mulki Najeriya ba ta taɓa kawo sojojinta ƙasarmu ba, sai da suka yi dukkan mai yiwuwa muka ƙi yarda sannan suka kai su Nijar ɗin, ita kuma ta yadda ta karɓa, haka ita ma Faransar da ta mulke su ta so ta kawo mana sojojinta, muka ce ba mu amince ba, me ya sa sai yanzu za mu sake shawara?''

Harin jiragen soji ya kashe mutum 10 a Sokoto

Jirgin soji

Asalin hoton, NAF

Wasu hare-haren da sojojin Najeriya na sama da na ƙasa suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da jami'an sojin suka kai hari kan ƙauyukan, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC.

A tattaunawarsa da BBC, Abubakar Muhammad ya ce "Tun da safe aka kira ni aka shaida min cewa an ji saukar bama-bamai, inda na bincika na tabbatar da faruwar hakan."

Harin jirgin soji

Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce "jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai" a kan ƙauyukan.

Babu hujjar kashe mutanen da babu ruwansu - Atiku

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce babu wata hujjar da za a bayar kan kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Atiku ya bayyana haka a saƙonsa na jaje game da ibtila'in da ya auku a jihar Sokoto, inda hare-haren sojoji 'bisa kuskure' ya yi ajalin aƙalla mutum 10, ya jikkata wasu.

Atiku ya ce yadda kuskuren ke maimaituwa ya sa ake tambayar wane darasi aka ɗauka a baya.

A cewarsa, "A ranar 3 ga Disamban 2023, gomman mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba ne suka rasu a Tudun Biri da ke Kaduna. Shin mutum nawa za su ƙara mutuwa kafin a ɗauki mataki? Duk da cewa yana da kyau a ƙaddamar da hare-hare kan ƴanbindiga, amma ai akwai buƙatar a yi amfani da ƙwarewa."

"Babu wata hujjar da za a bayar kan kashe mutanen da babu ruwansu. Irin haka na nuna rashin ƙwarewa da tauye haƙƙin ɗan'adam."

Muna buƙatar addu'o'inku domin jagoranci nagari - Tinubu

Shugaba Bola Tinubu

Asalin hoton, Tinubu Facebook

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu'a, inda ya ce su ma suna buƙatar hakan tare da goyon baya domin ƙasar ta ci gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti, inda ya taya al'ummar Najeriya murna, tare da kira ga Kiristoci su yi amfani da ranar domin sabunta burinsu na samun ingantacciyar Najeriya.

Shugaban ya sake jajanta wa waɗanda suka rasu a turmutsutsun Oyo da Anambra da Abuja, inda ya ce shugabanni ma suna buƙatar addu'o'in domin su yi jagoranci nagari.

Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar su tuna marasa ƙarfi, musamman maƙwabta da ƴan'uwa da abokai da sauran abokan hulɗa.

"Shugabanni ma suna buƙatar addu'o'i da goyon baya. Idan muka samu goyon bayanku, za mu yi mulki nagari. Najeriya ta kama hanyar inganci domin alamu suna nuna cewa akwai haske a gaba."

Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka a rubu'i na uku na 2024 - CBN

CBN

Asalin hoton, CBN X

Babban bankin Najeriya ya ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu'i na uku na shekarar 2024, daga kashi 3.19 a rubu'i na biyu na shekarar.

CBN ya bayyana hakan a cikin rahotonsa, inda ya ƙara da cewa yawanci an samu cigaban ne daga wasu ɓangarorin daban da na albarkatun man fetur.

Rahoton ya kuma ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a ɗan tsakanin nan.

A ɓangaren man fetur, rahoton ya ce man da ake fitarwa a Najeriya ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.33 a kullum, daga ganga 1.27 da ake fitarwa a rubu'i na biyu na shekarar, wanda rahoton ya ce bai rasa nasaba da tsaro da aka samu a yankin Neja Delta.

CBN ya ce haɓakar da ake samu na da nasaba ne da ƙoƙarin inganta harkokin kasuwanci a ƙasar.

Kirsimeti: Remi Tinubu ta buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri

Oluremi Tinubu

Asalin hoton, Oluremi Tinubu/facebook

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga ƴan Najeriya su ƙara haƙuri, inda ta ce lallai akwai haske a gaba.

Oluremi ta bayyana haka ne a saƙonta na Kirsimeti ga ƴan Najeriya, inda ta ƙara da godiya da ƴan Najeriya bisa haƙurinsu da goyon bayan da suke bayarwa wajen gina Najeriya.

A cewarta, "ina tabbatar muku cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a shirye yake ya kawo gyare-gyare da za su inganta rayuwar ƴan Najeriya, waɗanda tuni wasu daga cikin sun fara nuna alamar nasara.

"Mu cigaba da ƙarfafa gwiwar juna, da haɗin kai domin inganta ƙasarmu."

'Ƴansanda sun kama mutum fiye da dubu 30 tare da ƙwato makamai a 2024'

Ƴan sanda

Asalin hoton, Nigeria Police Force/Facebook

Babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya ce jami'an rundunar sun kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban har mutum 30,313, sannan sun ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar 2024.

Shugaban ƴansandan ya bayyana haka ne a taron ganawa manema labarai a ranar Talata, 24 ga watan Disamba a Abuja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce sun bayyana nasarar da suka samu ne domin nuna irin shirin fuskantar baɗi da suke yi.

Shugaban ƴansandan ya yaba da ƙokarin jami'ansa da sadaukarwar da suka yi a shekarar, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar ce tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro, inda ya ƙara da cewa ana buƙatar hakan domin tabbatar da tsaro mai inganci.