Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 25/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Mota ta kaɗe masu bikin Kirsimeti 22 a Gombe

    Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaha
    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaha

    Wani hatsarin mota ya yi sanadin raunata mutum 22 waɗanda ke tattakin bikin kirsimeti a Gombe, babban birnin jihar Gombe da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da mabiya addinin Kirista ke wani tattaki a cikin garin na Gombe, kamar yadda suka saba a kowace shekara.

    Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya a jihar, ASP Buhari Abdullahi ya ce "wata mota ƙirar sharon, maƙare da kayan hatsi ce ta afka cikin masu jerin gwanon ta baya, inda ta buge mutane da dama".

    "Wasu daga cikin waɗanda aka bugen sun samu raunuka har da karaya, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa."

    ASP Abdullahi ya ce jami'an tsaro sun samu nasarar ceto direban motar wanda mutane suka hau shi da duka, lamarin da ya so ya haifar da hatsaniya.

    Duk da haka, jami'in ya ce masu tattakin sun kammala ziyarar da suka shirya yi a ranar bikin na kirsimeti.

    A yau Laraba ne mabiya addinin Kirista a faɗin duniya suka yi bukukuwan Kirsimeti domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Yesu Almasihu.

    Za a iya cewa bukukuwan sun gudana a faɗin Najeriya cikin lumana ba tare da samun wani rahoto na hatsaniya ko tashin hankali ba.

    Sai dai gabanin ranar ta Kirsimeti an samu asarar rayukan mutane waɗanda suka halarci wuraren da aka yi rabon abinci a Abuja, babban birnin ƙasar, da jihohin Anambra da kuma Oyo.

    Inda turmutsutsun da aka samu a garin Okija na jihar Anambra ya haifar da mutuwar mutum 22, a Abuja kimanin mutum 10 ne suka mutu, sai kuma yara 35 da aka tabbatar sun mutu a turmutsutsun na garin Ibadan da ke jihar Oyo.

  2. 'Harin jiragen soji ya kashe mutum 10 a Sokoto'

    Jirgi

    Asalin hoton, NAF

    Wasu hare-haren da sojojin Najeriya na sama da na ƙasa suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.

    Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da jami'an sojin suka kai hari kan ƙauyukan, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC.

    A tattaunawarsa da BBC, Abubakar Muhammad ya ce "Tun da safe aka kira ni aka shaida min cewa an ji saukar bama-bamai, inda na bincika na tabbatar da faruwar hakan."

    Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce "jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai" a kan ƙauyukan.

    "Wani wuri ne da ake kira Gidan Bisa da kuma Runtuwa waɗanda ke a mazaɓata."

    "Hare-hare ne babu ƙaƙautawa," waɗanda Abubakar ya bayyana cewa sojojin ba su tsaya da kaiwa ba har sai da gwamnatin jihar ta sanya baki.

    Ya ƙara da cewa "Sojojin sama ne da na ƙasa suka kai harin, sojojin sama sun shiga yankin da manyan tankokin yaƙi."

    Shugaban ƙaramar hukumar ya ce baya ga mutum 10 da suka mutu, akwai kuma mutum shida da suka samu raunuka.

    Ƙauyukan na kusa da jejin Surame da ake ganin maɓuyar mayaƙan ƙungiyar Lakurawa da ta ɓulla a ƙasar a baya-bayan nan.

    A lokuta da dama sojojin Najeriya kan yi kuskuren kai hare-hare kan fararen hula, lamarin da a wasu lokutan ke haddasa mummunan asarar rayuka.

    Ko a watan Disamban 2023 ma, wani jirgin sojin ƙasar maras matuƙi ya kai hari kan masu Mauludi a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, lamarin da ya haifar da asarar gomman rayuka, da jikkata wasu da dama.

    ...
    ...
  3. Isra'ila da Hamas sun zagi juna da jan ƙafa wajen cimma tsagaita wuta a yaƙin Gaza

    Isra'la da hamas sun zargi juna da da laifin kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta don kawo ƙarshen yaƙin Gaza domin sakin mutanen da ake tsare da su.

    Hamas ta ce Isra'ila na neman ƙaƙaba wasu sabbin sharaɗa, yayin da Benjamin Netanyahu ya zargi ƙungiyar da rashin gaskiya da kuma komawa kan tsofaffin sharuɗa.

    Bayanan baya-bayan nan da ɓangarorin biyu suka yi ya sake kawo sauyi a fatan.

    A lokacin wata ziyara da ya kai mashigar Philadelphi Corridor da ke kan iyakar Gaza da Masar, ranar Laraba, ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce sojojin Isra'ila ba za su janye daga mashigar ba, wani sharaɗi mai muhimmanci a yarjejeniyar.

  4. Mutum 38 ne suka mutu a hatsarin jirgin Kazakhstan - jami'ai

    Jirgi

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai a Kazakhstan sun ce mutum 38 ne suka mutu a hatsarin jirgin da ya auku a kusa da birnin Aktau na ƙasar.

    Jirgin saman, wanda na kamfanin Azerbaijin ne, ya kama da wuta ne, sannan ya faɗo a kusa da birni Aktau.

    Kusan mutum 67 ne da suka haɗa fasinjoji da ma'aikatan jirgin ne suka tsira daga hatsarin.

    Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa birnin Grozny na yankin Chechnya a ƙasar Rasha, kafin a karkatar da shi saboda hazo.

    Kamfanin Azerbaijan Airlines ya dakatar da jigilar jiragensa a yankin, har zuwa lokacin kammala bincike.

  5. Hotunan yadda aka gudanar da jana'izar mahaifiyar Gwamnan Jigawa

    Jigawa

    Asalin hoton, Abubakar Auwal

    Bayanan hoto, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne tare da wasu waɗanda suka halarci jana'izar

    An gudanar da jana'izar mahaifiyar gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Maryam Namadi Umar, wadda ta rasu yau Alhamis da safe.

    Jigawa

    Asalin hoton, Abubakar Auwal

    An gudanar da jana'izar ne a garin mahaifar gwamnan da ke Kafin Hausa.

    Gwamna Umar Namadi dai yana ƙasar China domin ziyarar aiki, lokacin da aka yi rasuwar, sai dai sakataren yaɗa labaransa ya tabbatar da cewa yana kan hanyar koma wa gida.

    Jigawa

    Asalin hoton, Abubakar Auwal

    Bayanan hoto, Nan ma wani sashen waɗanda suka raka gawar maƙabarta ne

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na daga cikin mutane da suka halarci jana'iza.

    Jigawa

    Asalin hoton, Abubakar Auwal

    Bayanan hoto, Wasu mutane da suka raka gawar maƙabarta
    Jigawa

    Asalin hoton, Abubakar Auwal

    Bayanan hoto, Lokacin da ake sanya gawar a ƙabari
  6. An samu tsaikon sufurin jiragen ƙasa bayan mutuwar direba a faransa

    Hoton jirgin ƙasa

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu tangarɗar zirga-zirgar sufurin jiragen Faransa bayan da wani diraban jirgin ƙasa ya kashe kansa a lokacin da yake tsaka da aiki.

    Bayanai sun ce direban ya yi tsalle sanna ya fita a daidai lokacin da jirgin da yake tuƙawa ke tsaka da gudu, abin da ya sa jirgin ya rage gudu bayan da nan take tsarin kulawar gaggawa na jirgin ya karɓe iko da shi.

    An samu gawarsa a kusa da titin jirgi, lamarin da ya faru a jajiberin bukukuwan Kirsimeti ya haifar da tsaiko a ɗaya daga cikin ranakun tafiye-tafiye na shekara.

  7. Syria ta gargaɗi Iran kan zargin kunna rikici a ƙasar

    Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon ministan harkokin wajen Syria ya gargaɗi Iran kan zarginta da yunƙurin haddasa husuma a ƙasar.

    Asaad Hassan al-Shibani ya buƙaci Tehran ta mutunta zaɓin al'ummar Syria, da suka zaɓi kawo ƙarshen mulkin Assad da kuma mutunta ƴancin ƙasar da tsaronta.

    A ranar Litinnin da ta wuce, ministan harkokin wajen Iran ke cewa bai samu ganawa da sabbin shugabannin Syria ba, tare da kiran kada su bari ƙasar ta kasance wani sansanin ƴan ta'adda.

    Ana dai ganin kifar da gwamnatin Assad babban koma baya ne ga siyasar Iran da ƙawancenta na soji da ke yaƙi da Isra'ila da tasirin Amurka a Gabas ta Tsakiya

  8. Ƴansandan ƙasa da ƙasa na neman ƴan Najeriya 14 ruwa a jallo

    Interpol

    Asalin hoton, PA Media

    Aƙalla ƴan Najeriya 14 ne Rundunar ƴansanda na ƙasa da ƙasa ke nema ruwa a jallo saboda laifuka daban-daban da suka haɗa da sata da zamba da safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.

    BBC ta kalato labarin ne daga sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na intanet, inda ta ce ƙasashe daban-daban ne suke neman ƴan Najeriyan saboda zarginsu da aikata laifuka daban-daban.

    Daga cikin waɗanda aka ambata sunansu akwai Felix Omoregie da Jessica Edosomwan da Uche Egbue da Jude Uzoma da Chinedu Ezeunara da Benedict Okoro da Ikechukwu Obidiozor da Alachi Stanley.

    Sauran su ne Bouhari Salif da Timloh Nkem da Austine Costa da Okromi Festus da Akachi Vitus da Mary Eze.

  9. Abubuwa takwas da suka ɗauki hankalin arewacin Najeriya a 2024

    Ndume

    Asalin hoton, NIGERIA SENATE

    Al'amura da dama sun faru a shekarar 2024 da suka ɗauki hankalin mutane musamman a arewacin Najeriya kama daga fagen siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa har ma da batun tsaro.

    A iya cewa 2024, za ta zama shekarar da zai yi wuya a iya mantawa da ita a arewacin Najeriya la'akari da yadda abubuwan da suka faru suka shafi rayuwarsu kai tsaye har ma a ka yi ta tafka muhawara a kai a shafukan sada zumunta.

    A wannan maƙala, mun tattaro maku muhimman abubuwan da suka faru da suka ja hankalin arewacin Najeriya.

  10. Rasha ta ce 'kwalliya ta biya kuɗin sabulu' a hare-harenta a Ukraine

    Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ɗauki alhakin hare-haren da aka kai a ƙasar Ukraine a ranar Kirsimeti a cibiyoyin makamashi.

    Ma'aikatar ta ce ta kai hare-hare manya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a cibiyoyin makamashin Ukraine.

    "Kwalliya ta biya kuɗin sabulu a hare-haren."

  11. Tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi a shekarar 2024

    Tinubu

    Asalin hoton, Presisency

    Galibi shugabannin ƙasashen duniya kan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare domin tafiya ta aiki ko ta ƙashin kai.

    Waɗanann tafiye-tafiye kan haɗa ta taruƙan ƙungiyoyin ƙasashe da bisa gayyatar shugaban wata ƙasa ko tafiya hutu, ko neman lafiya.

    A nasa ɓangare shugaban Najeriya, Bola Tinubu, kamar sauran takwarorinsa shugabannin ƙasashen duniya, ya yi bulaguro da dama zuwa ƙasashen daban-daban a shekarar mai ƙarewa.

  12. Hare-haren Rasha a Ukraine a ranar Kirsimeti dabbanci - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce hare-haren da Rasha ta kai ƙasarsa a ranar Kirsimeti dabbanci.

    "Duk wani hari da Rasha za ta kai sai ta shirya masa. Ba ta wayan gari kawai ta kai hari. Don haka da gangan ta kai waɗannan hare-haren a ranar Kirsimeti.

    "Da gangan Putin ya zaba ranar Kirsimeti domin kai waɗannan hare-hare. Wane irin dabbanci ne kai harba makamai sama da 70, ciki har da makami mai linzami, da kuma jirage marasa matuƙa sama da 100. Cibiyoyin makamashinmu suke hara, burinsu su katse wuta a Ukraine."

  13. Muhimmancin Ranar Kirsimeti ga mabiya addinin Kirista

    Fasto Joseph Gad ya bayyana mana muhimmancin ranar ga mabiya addinin Kirista da kuma abubuwan da suka kamata su yi a ranar.

    Mataimakin Babban Fasto a Cocin Hosanna Glory, Fasto Joseph Gad ya ce al'umma Kirista su yi amfani da wannan ranar don yi wa kansu hisabi da kuma gyara ibada.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  14. Kwastam ta dakatar da sintirin bakin iyakokin Najeriya saboda zargin cin zarafi

    Kwastam

    Asalin hoton, NIGERIA CUSTOMS

    Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da dakatar da aikin sintirin haɗin gwiwar jami'an tsaro na bakin iyakokin ƙasar, wato Joint Border Patrol Team (JBPT).

    Kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

    A ranar 11 ga Disamba ne majalisar wakilai ta ba kwamitinta na kwastam umarnin gudanar da bincike kan ayyukan jami'an kwastam a bakin iyakokin ƙasar bayan zarge-zargen almundahana da cin zarafin ƴanƙasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Amma kakakin rundunar ya ce hukumar ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na inganta tsaron bakin iyakokin domin fuskantar 2025.

    Maiwada ya ƙara da cewa dakatar da jami'an ba zai zama barazana ga tsaron bakin iyakokin ƙasar ba, inda ya ƙara da cewa za su ɗauki matakin zamanantar da ayyukan hukumar domin tabbatar da tsaron ƙasar.

    Asali an kafa dakarun haɗin gwiwar ne a ƙarƙashin kulawar ofishin NSA domin yaƙi da fasaƙauri da kwarorowar baƙin haure da wasu manyan laifuka.

  15. Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

    Jigawa

    Asalin hoton, Namadi/Facebook

    Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi Umar ta rasu.

    Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, inda ya ce mahaifiyar gwamnan ta rasu ne a ranar Laraba, 25 ga Disamban 2024.

    Sanarwar ta ƙara da cewa za a jana'izarta ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a Kafin Hausa.

  16. Rasha ta kai hare-hare a Ukraine a ranar Kirsimeti

    Ukraine

    Asalin hoton, X

    Rasha ta kai hare-hare masu girma a wasu biranen Ukraine a safiyar Kirsimeti.

    Ministan makamashin Ukraine, German Galushchenko ya ce: "maƙiyanmu suna kai mana hare-hare a cibiyoyin makamashinmu."

    Ya ce an rage rarraba lantarki a ƙasar saboda rage illar hare-haren.

    Magajin Garin Kharkiv, Ihor Terekhov, ya ce aƙalla makamai masu linzami 12 aka harba a birnin, wanda shi ne na biyu mafi girma a ƙasar.

  17. Hatsarin jirgin sama ya yi ajalin gomman mutane a Kazakhstan

    Jirgi

    Asalin hoton, Reuters

    Gomman mutane sun mutu bayan da wani jirgin sama mai ɗauke da fasinjoji 67 ya yi hatsari a Kazakhstan, kamar yadda rahotanni daga ƙasar suka nuna.

    Hukumar agajin gaggawa ta ƙasar ta ce mutum 25 sun tsira daga hatsarin.

    Jirgin saman, wanda na kamfanin Azerbaijin ne, ya kama da wuta ne, sannan ya faɗo a kusa da birni Aktau. Amma har yanzu ba a san dalilin hatsarin jirgin ba.

    Jirgin mai lamba J2-8243 ya taso ne daga birnin Baku na Azerbaijani zuwa birnin Grozny na Rasha, amma rahotanni sun ce an juya akalar jirgin saboda hazo.

    Wani faifan bidiyo da Reuter ta tantance ya nuna jirgin yana faɗowa ƙasa, sannan wuta ta turnuƙe.

  18. Kirsimeti: Muna buƙatar addu'o'inku domin jagoranci nagari - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Facebook

    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu'a, inda ya ce su ma suna buƙatar hakan tare da goyon baya domin ƙasar ta ci gaba.

    Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti, inda ya taya al'uumar Najeriya murna, tare da kira gare ga Kiristoci su yi amfani da ranar domin sabunta burinsu na samun ingantacciyar Najeriya.

    Shugaban ya sake jajanta wa waɗanda suka rasu a turmutsutsun Oyo da Anambra da Abuja, inda ya ce shugabanni ma suna buƙatar addu'o'in domin su yi jagoranci nagari.

    Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar su tuna marasa ƙarfi, musamman maƙwabta da ƴan'uwa da abokai da sauran abokan hulɗa.

    "Shugabanni ma suna buƙatar addu'o'i da goyon baya. Idan muka samu goyon bayanku, za mu yi mulki nagari. Najeriya ta kama hanyar inganci domin alamu suna nuna cewa akwai haske a gaba."

    Ya kuma ce za su tabbatar dukkan masu tafiye-tafiye sun je inda za su je lafiya, ta hanyar tabbatar da tsaro da kuma samar da hanyoyin sufuri kyauta.

  19. Kirsimeti: Remi Tinubu ta buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri

    Oluremi

    Asalin hoton, Oluremi Tinubu/facebook

    Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta yi ga ƴan Najeriya su ƙara haƙuri, inda ta ce lallai akwai haske a gaba.

    Oluremi ta bayyana haka ne a saƙonta na Kirsimeti ga ƴan Najeriya, inda ta ƙara da godiya da ƴan Najeriya bisa haƙurinsu da goyon bayan da suke bayarwa wajen gina Najeriya.

    A cewartsa, "ina tabbatar muku cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a shirye yake ya kawo gyare-gyare da za su inganta rayuwar ƴan Najeriya, waɗanda tuni wasu daga cikin sun fara nuna alamar nasara.

    "Mu cigaba da ƙarfafa gwiwar juna, da haɗin kai domin inganta ƙasarmu."

  20. Ana bikin Kirsimeti lami a Bethlehem saboda yaƙin Gaza

    Kirsimeti

    Asalin hoton, Getty Images

    Yaƙin Gaza ya haifar da Kirismeti lami a Bethlehem, karo na biyu a jere.

    Ba a gudanar da bukukuwa ba a dandalin cocin da aka gina a wurin da aka haifi yesu Almasihu, ba kuma a kunna kyandura ko ajiye bishiyar Kirsimeti ba.

    Wakiliyar BBC ta ce an dai hango yara suna tattaki ɗauke da rubutu a takardu da ke kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Babban limamin mabiya katholika a birnin Ƙudus, ya ce duk da halin taɓarɓarewa da Gaza ke ciki, ya umarci jama'a su kasance da ƙwarin gwiwa da kyakyawar fata.