Abubuwan da gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya suka cimma a taronsu

Asalin hoton, Mamman Mohammed/X
Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya ta kammala taronta na 11 da ta gudanar a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
A ranar Alhamis ɗin nan ne gwamnonin suka gudanar da taron kan matsalolin da yankin ke fama da su da suka haɗa da na tsaro da kuma tattalin arziƙi.
Taron na zuwa a yayin da yankin ke fama da sabbin hare-haren daga mayaƙan Boko Haram da na ISWAP.
Masana da al'ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Ƙungiyar Gwamnonin yankin ta jaddada ƙudirin aiki tare domin magance matsalolin da ke addabar yankin.
Cikin sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana wasu ta tace ta cimma a taron da yau da suka haɗa da:
- Haɗa kai domin tallafa wa gwamnatin tarayya ta kowane fanni domin magance matsalar tsaro da ke addabar yankinsu.
- Kira ga rundunar sojin Najeriya, da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al'umma domin sake shirin tunkarar matsalar tsaro musamman a yankin.
- Gwamnonin sun ce matsalar tsaro na buƙatar gano abubuwan da ke haddasata, domin maganceta, ba lallai sai da ƙarfin soji kaɗai ba. Gwamnonin sun ce ana buƙatar ɓullo da matakan samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai da ilimin sana'o'i domin rage talauci.
- Haka kuma ƙungiyar ta ce matsalar titunan yankin ta taimaka wajen taɓarɓarewar tsaro a yankin. Inda ta yi kira ga shugaban ƙasa ya magance matsalar, musamman ayyukan titunan da tuni aka bayar da aikinsu amma ba a yi ba.
- Gwamnonin sun kuma amince da samar da hanyoyin zuba jari a yankin, musamman a fannin noma don magance matsalar abinci a ƙasar.
- Sannan kuma gwamnonin sun amince da yin aiki tare da hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ta ƙasar, don taimakawa wajen sanya almajirai da sauran yara a makarantun zamani da samar musu da sana'o'in dogaro da kai.

Shawarwarin Bulama huɗu
Barista Bulama Bukarti wanda masanin tsaro ne kuma mai bincike kuma ɗan asalin yankin ne ya ce dole ne a tunkari ƙungiyar Boko Haram kai tsaye.
"Mun ga manyan hare-hare a jihar Borno da suka haɗa da kan sansanonin soji da ƙauyuka da ke nuna girman matsalar da ke son dawowa."
Barista Bukarti ya zayyana wasu shawari guda huɗu da ya ce idan aka bi su yankin zai samu zaman lafiya:
- Gwamnoni su yi kira da murya ɗaya wajen nuna illar matsalar. Saboda yanzu za ka ji gwamnan jihar Borno ne kawai ke. Ya kamata dukkansu su fito su yi magana ko gwamnatin tarayya za ta fi mayar da hankali domin matsalar nan idan ta ta'azzara to iya jihar Bornon za ta tsaya ba.
- Gwamnonin su yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da batun janye manyan motocin sojoji daga yankin.
- Su yi kira na bai ɗaya ga gwamnatin tarayya wajen neman ƙarin kayan aiki da sojoji domin su tabbatar cewa an tunkari Boko Haram an murƙushe ta.
- Dole ne su yi kira da murya ɗaya ga gwamnatin tarayya domin a toshe duk wata kafar da ƙungiyar ta Boko Haram ke samun kuɗade da kayan yaƙi na zamani domin daƙile kai hare-hare kan al'ummar yankin.
Me ya faru?
A karon farko a tsawon shekaru ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta ɗauki alhakin kisan mutum 26 a wani harin bam da ta dasa a garin Rann a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta yi wannan iƙirari ne a shafinta na Telegram.
Lamarin dai ya faru ne ranar Litinin bayan da wata mota ta taka bam a gefen hanya a garin na Rann da ke iyaka da jamhuriyar Kamaru.
Hakan na zuwa ne kimamin mako biyu bayan da wata motar bas ta taka wani abin fashewa da aka binne a yankin, abin da ya janyo mutuwar fasinjoji takwas da kuma raunata wasu 11.
Ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun shafe tsawon shekara 15 suna kai hare-hare da kuma artabu da jami'an tsaron Najeriya a arewa maso gabas.
Sun sha amfani da abubuwan fashewa wajen afkawa fararen hula da kuma jami'an tsaro.
Matsaloli biyu da yankin ke fama da su baya ga tsaro
Mazauna yankin na arewa maso gabashin Najeriya irin su Kwamared Goni Kolo wanda shi ne kakakin ƙungiyar rundunar adalci na yankin arewa maso gaba sun ce manyan matsalolin yankin nasu guda biyu ne da suka haɗa da talauci da rashin ilimi waɗanda su ne ke haifar da matsalar tsaro da ta lafiya.
"Rashin abin yi ya ƙazanta a tsakanin matasa - maza da mata. Kaso 75 na matasa ba su da aikin yi. Saboda haka ya zama wajibi ga gwamnonin yankin su ƙirƙiri abubuwan da yi ga matasan nan walau dai sana'o'i ko noma ko kiwo - a ba su tallafi ta yadda za su dogara da kansu." In ji Kwamared Goni Kolo.










