Yaushe rayuwar ma'aikacin Najeriya za ta inganta?

Ma'aikatan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da duniya ke murnar Ranar Ma'aikata a kowace ranar 1 ga watan Mayu, ma'aikatan Najeriya na cikin wani hali na damuwa da tashin hankali.

An ware wannan ranar ne domin girmama ƙoƙarin ma'aikata a duniya, amma ga ma'aikatan Najeriya, wannan rana na tuna musu da matsalolin da suke fuskanta a kowace rana.

Waɗannan matsaloli sun haɗa da ƙarancin albashi da wahalar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi da wahala wajen aiki da kuma rashin ingantattun yanayin aiki da dai sauran su.

Yawanci ma'aikata a Najeriya suna bayyana takaicinsu dangane da yanayin da suke ciki a ƙasar.

Albarkacin ranar ta ma'aikata, BBC ta tattauna da wasu ma'aikatan ƙasar domin jin irin yanayin da suke ciki da kuma fatan da suke da shi.

Yadda nake rayuwa - Malamin makaranta

...

Asalin hoton, Innocent Frimpong

Faruk Yahaya, wani malamin makaranta ne da ke koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta a jihar Legas inda ya shaida wa BBC cewa Ranar ma'aikata ta duniya tana tuna masa da yadda yake bayar da lokacinsa da ƙarfinsa da lafiyarsa wajen aiki amma kuma albashinsa ba ya isar sa gudanar da rayuwar da yake so.

"Na shafe shekaru 13 ina koyarwa, amma gaskiya har yanzu ina samun ƙasa da Naira dubu sittin a wata. Wani lokacin ma ba na samun albashin kan lokaci, amma duk da haka, kowacce safiya ina tashi na shirya na fita zuwa makaranta in koyar da ɗalibai sama da 20 a aji ɗaya domin idan ban yi ba, wa zai koyar da waɗannan yaran?", malamin ya ce.

Farouk ya kuma bayyana yadda yake kashe albashinsa idan aka biya shi inda ya ce akwai abin al'ajabi a ciki.

"Yadda nake kashe albashina gaskiya sai a hankali, yawanci ma a kafa nake zuwa aiki, ina da babur amma ba kodayaushe nake samu na saka masa fetur ba. Idan na sami albashin,ina sayen kayan abinci amma kuma ba ya wani daɗewa, a cikin albashin nake biyan wasu kuɗaɗen hidimar gida."

"Biyan kuɗin haya kuma, hmmmm, wannan abun al'ajabi ne, a hankali nake biya, ga kuɗin makarantar 'ya'yana, shi ma Wata babbar matsala ce." In ji Farouk Yahaya.

Yahaya ya ce mafi yawanci, rancen kuɗi yake yi wanda shi ma da ƙyar yake samun wanda zai bashi rancen kuma wajen biya ma da wahala.

"Babu wani tallafi n da muke samu, akwai ranakun da na kan ji kamar na hakura, amma ina zan je, aiki na wahala yanzu sosai. gaskiya sai an sake duba wannan lamarin." In ji Malamin.

Rayuwar likitoci a Najeriya

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga likitoci kamar Dr Nura Badamasi wanda shi likita ne a asibitin gwamnati na jihar Kaduna ya ce Ranar Ma'aikata ta Duniya kamar alama ce kawai, babu wani abun murna a ciki.

"A matsayinmu na likitoci, an horar da mu yi wa mutane hidima da kuma ceton rayuka, amma halin da muke aiki a ciki abin taƙaici ne."

"Ban cika samun albashina da wuri ba, wani lokacin yana ɗaukan makonni, kuma a haka nake zuwa aiki kullum, ina amsa kiran gaggawa ko da ba ranar aiki na ba ne, ina yin aikn dare da rana, amma kuma ba kodayaushe ba ne, wasu lokutan gaskiya ina samun albashina da wuri. Wallahi abin akwai gajiya", ya ƙara da cewa.

Dr Nura ya ce akwai wasu abokan aikinsa da ba sa iya biyan haya, wasu ma sai sun dinga karɓar rance domin ciyar da iyalinsu duk dan saboda ƙarancin albashi da kuma rashin samun albashin da wuri.

Ya ƙara da cewa "gajiyar da ke kanmu ba ƙarama ba ce. Sau da yawa na kan yi aiki har tsawon sa'o'i 72 ba tare da cin abinci mai kyau ba ko samun isasshen bacci."

"Duk da haka, muna ci gaba da aiki, ba dan mun fi kowa ƙarfi ba amma saboda marasa lafiya suna bukatarmu, kuma barin aikin kamar rashin tausayi ne." in ji shi.

Lkitan ya ƙara da cewa suna fama da ƙarancin ma'aikata da ƙarancin albashi, da kuma gajiya ta jiki da zuciya da kuma rashin girmamawan da ake musu.

Daga ƙarshe Dr Nura ya ce yana fatan wannan Rana za ta haifar da tattaunawa ta gaskiya kan halin da ma'aikatan lafiya ke ciki.

Ma'aikaciyar gwamnatin tarayya

Aisha wadda ba sunanta ba kenan, wata ma'aikaciyar gwamnati ce kuma uwa, ta ce a wajenta, Ranar Ma'aikata ta duniya lokaci ne na tunani da kuma damuwa.

"A matsayina na mace mai aiki, daidaita aikin gida da na ofis ba abu ne mai sauƙi ba. Albashin da nake samu ba ya wadatar da bukatuna gaba ɗaya." in ji ta

"Ina haɗa aikin waje da na cikin gida, kuma wasu ranaku ban san yadda zan cika bukatuna da na yara ba da yake mai gida na ya rasu, kuma ina da yara 4, wanda dole ne na ɗauki nauyinsu ta bangaren tarbiyya, makaranta, abinci, kayan sakawa da dai sauransu."Radiya ta ƙara da cewa.

Dangane da albashi kuma Aisha ta ce "har yanzu albashina bai wuce dubu 80 ba bayan kwashe shekara shida ina aiki. Na fara da diploma shekaru shida da suka wuce wato na fara da matakin aiki na shida kuma lokacin albashina naira dubu 60 ne. Yanzu na zama mai albashi mataki na takwas inda nake ɗaukar naira dubu 80."

Aisha ta ƙara da cewa "albashinna ba ya isa ko ga abubuwan bukata na yau da kullum, kuma hauhawar farashin kayayyaki na ƙara dabula mani lissafi."

"Wasu lokuta har rashin lafiya nake yi saboda gajiya, amma duk da haka dole in je aiki domin ba zan iya rasa kuɗin yini ɗaya ba." in ji ta.

...

Asalin hoton, Getty Images

Aisha ta ce Ranar Ma'aikata ta duniya ya kamata ta kasance lokaci na samun tallafi nƙarin albashi, da samun sassauci wajen aiki.

Irin wannan rayuwa da Aisha take yi da Farouk wanda malamin makaranta ne da kuma likita Dr Badamasi irinta ce rayuwar sauran ma'aikatan Najeriya.

Masana da su kansu ma'aikatan sun sha kiraye-kirayen cewa dole ne a inganta rayuwar ma'aikaci a kasar idan dai ana son samun nagartaccen aiki.

Irin wannan yanayi maras daɗi ne ke tilasta mutane musamman likitoci barin ƙasar, inda suke fita zuwa ƙasashen waje domin samun ayyuka masu tsoka.

Muna neman ƙarin albashi kan mafi ƙaranci - NLC

...

Asalin hoton, NLC X

Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta NLC, Comrade Nasir Kabir a tattaunawarsa da BBC ya ce ma'aikata a Najeriya na cikin matsanancin hali duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.

"Sai ki ga ƙaramin ma'aikaci ba ya iya ciyar da iyalansa ko kuma biyan kudin kantarki da sauransu da ɗan mafi ƙanƙantar albashin da ake ba shi." in ji shi.

Ya ƙara da cewa saboda hakane ƙungiyar ta NLC ƙarƙashin jagorancin comrade Joe Ajoero ke fafutukar ganin an inganta albashin ma'aikata ta hanyar gabatar da wasiƙa da ke buƙatar sabon ƙarin albashi mafi ƙanƙanta kan na 70,000 din da aka amince da shi ga ma'aikatan Najeriya wani sabon ƙarin albash ko kuma gwamnati ta haɗu da fushin ƙungiyar.

"Wannan shi ne abun da muke kai saboda mun duba mun ga cewa manufar gwamnati ba wai ta inganta albashin ma'aikata ba ne sai dai ta daɗa kawo wa ma'aikata wasu ƙarin wahalhalu,"

"Wahalhalun sun haɗa da ƙarin wutar lantarki da ƙarin maganar kuɗin kira na waya da na tura saƙo da charji na bankuna da duk sauran haraje-haraje da babu kai babu gindi."

"Idan an kai matsaya, daga baya ita gwamnatin tarayya sai ta juya tayi wani abu daban wanda hakan bai ba mu tsoro kuma bai sa gwiwarmu yayi sanyi

"Ba za mu zauna mu zuba ido ba, dole sai mun tashi mun yaƙi wannan zalincin da ake wa ma'aikata.

Comrade ɗin ya ƙara da cewa "ko mu ma ƴan ƙwadago muna fuskantar wannan walhalhalun, mu ma muna fama da ƙarancin albashi."

Ya kuma ce ma'aikata su ne waɗanda suke samo arziƙin ƙasa, idan babu su babu Najeriya, amma kuma babu ƙasƙantace kamar ma'aikacin gwamnati a Najeriya.

Comrade Nasir ya ƙara da cewa wannan rana ta ma'aikata ba rana ce ta farin ciki ba a wajensu, rana ce ta a tir da ganin halin da ma'aikata da talakawan Najeriya ke ciki.