Matakan da ƙasashen Afirka ke ɗauka wajen yaƙi da cutar ƙyandar biri

Ƙyandar biri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasar Jamhuriyar Kongo da cutar ta fi ƙamari na da sama da mutum 15,000 da suka kamu da kuma 455 da suka mutu
Lokacin karatu: Minti 3

Rahotonni a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta sun ce ƙasashen Afirka sun ƙara ƙaimi a kan iyakokinsu da zimmar daƙile yaɗuwar annobar cutar ƙyandar biri.

Ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo - da ta fi fama da cutar - ta ce ta tsara shirin rigakafin cutar da take fata zai daƙile ta.

An fara samun sabon nau'in ƙwayar cutar ne mai suna Clade1 MPXV a watan Satumban 2023 a ƙasar ta Kongo.

Ministan Lafiya Roger Kamba ya ce gwamnati na ƙoƙarin kashewa da kuma daƙile yaɗuwar cutar, kamar yadda shafin jaridar Actualite.cd ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa ƙasar, wadda ta gano mutum 15,000 da ke ɗauke da cutar da kuma 455 da suka mutu, za ta ƙaddamar da tsarin rigakafin nan gaba kaɗan.

Rahoton ya ce: "Mataki na gaba shi ne, a cewar ministan lafiya, kare yaɗuwar cutar: fito da tsarin yin rigakafin ƙyandar biri a Kongo wanda aka samar kuma aka amince da shi. Yanzu haka ana aikin inganta bin sawun da kuma tsaron daƙile ta a kan iyakoki."

Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Afirka, Africa Centre for Disease Control (CDC), ta ayyana ƙyandar birin a matsayin larurar da ke buƙatar kulawar gaggawa a nahiyar ranar 13 ga watan Agusta bayan ta karaɗe ƙasashe 16, ciki har da waɗanda ba su taɓa ganin cutar ba kamar Burundi, da Rwanda, da Uganda, da kuma Kenya.

Kwana ɗaya bayan haka, ita ma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ta larurar gaggawa a ƙasashen duniya. Tuni aka gano nau'in cutar a ƙasar Sweden.

Najeriya ta ƙara ƙaimi a kan iyakokinta wajen tantance masu shiga bayan mutum 39 sun kamu a jihohin ƙasar 33 cikin 36, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito ranar Juma'a.

Zuwa yanzu ba a samu rahoton mutuwa ba a ƙasar tun bayan ɓarkewar cutar a wannan karon.

Hukumomin lafiya sun ce za su ƙaddamar da matakai irin waɗanda aka ɗauka a loakcin annobar korona domin daƙile yaɗuwarta a Najeriya. Gwamnati ta ce za a buƙaci duka matafiyan da ke fita daga ƙasar su cike wani fom ta intanet.

Ma'aikatar lafiya ta shawarci jama'a su dinga kula da tsafta, kamar wanke hannu da sabulu, ko kuma amfani da man goge hannu na sanitiser.

Ƙasashen da ba su taɓa ganin cutar ba kafin yanzu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jaridar The Nation ta ruwaito ranar Alhamis cewa hukumomin Kenya sun yi wa mutum sama da 250,000 gwaji tun bayan da cutar ta kama mutum na farko a yankin Taita Taveta ranar 31 ga watan Yuli.

Ma'aikatar lafiya ta ƙara da cewa ta fara bin sawun mutanen da suka yi mu'amala da mutumin, waɗanda aka gano. Babbar Sakatariyar Lafiya Mary Muthoni ta ce ba a sake samun mai ɗauke da cutar ba zuwa yanzu.

"Mun kuma ankarar da duka cibiyoyin aikin gaggawa a ƙasa baki ɗaya, mun shirya ɗakunan gwajin lafiya don yin gwajin ƙyandar birin, tare da aika ƙwararrun ma'aikata 120 don lura da abin da ka iya faruwa," a cewar Muthoni.

Kenya ta saka ƙasahen Uganda, da Rwanda, da Sudan ta Kudu, da Jamhuriyar Kongo a matsayin masu haɗari.

Ministar Lafiya ta Uganda Jane Ruth Aceng ta ce ƙasarta ta samu mutum biyu ɗauke da cutar ta ƙyandar biri kuma an ba su magani har ma an sallame su, a cewar rahoton gidan talabijin na NTV ranar Juma'a.

Aceng ta shawarci 'yan Uganda kada su damu yayin da ma'aikatarta ta shirya tsaf wajen shawo kan cutar. Ta jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace don kare 'yan ƙasar "ba tare da hana su sukuni ba".

Yayin da ta bayyana a gaban wani kwamatin majalisar dokoki ranar Alhamis, Aceng ta ce ma'aikatar ta fayyace gundumomi 23 a matsayin mafiya haɗri, cikinsu akwai 17 da ke maƙwabtaka da Kongo.

A Mozambique, babbar jami'ar lafiya ta Birnin Maputo, Alice de Abreu, ta faɗa wa gidan rediyon Faransa ranar Alhamis cewa hukumomi sun ɗaura ɗamarar shawo kan lamarin idan ta-ɓaci.

Ta shawarci mazauna yankin su bi dokoki da ƙa'idojin yaƙi da cutar, tana mai cewa matakan za su taimaka wajen hana ɓarkewarta.