Yadda ƙyandar biri ke yaɗuwa tsakanin al'umma

Ƙyandar biri

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka ta ayyana ƙyandar biri a matsayin cuta mai matuƙar haɗari a nahiyar, bayan ɓullar sabon nau’in cutar da ke yaɗuwa cikin sauri.

Cutar na ƙara yaɗuwa cikin sauri a bana, tun bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Cibiyar ta yi gargaɗi kan yadda cutar za ta iya yaɗuwa sosai idan har aka gaza ɗaukar ƙwararan matakai.

An dai riga an fargar da likitoci game da yadda sabon nau’in cutar ta ƙyandar biri ke yaɗuwa cikin saurin.

Cutar na yaɗuwa ne a tsakanin mutanen da suka yi cuɗanya, kuma tana da alamomi masu kama da na mura, sai dai na ƙyandar biri ya fi tsanani.

A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda cutar ke yaɗuwa sosai, mutum 27,000 aka tabbatar sun kamu da ita a bara, daga cikin su kuma fiye da dubu sun mutu.

Cutar ta kuma yaɗu zuwa ƙasashe da suka haɗa da Kenya da Rwanda da Burundi da kuma jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Ana dai sa ran cewa ayyana dokar ta ɓaci a kan ƙyandar biri zai taimakawa gwamnatoci wajen tsara ayyukan gaggawa domin kai ɗauki, da kuma ƙara inganta hanyar shigar da tallafin magunguna a wuraren da aka samu ɓulluar ta.

Cibiyoyin kula da lafiya a wajen Afirka ma za su sanya ido a kan yadda lamarin zai kasance, da kuma hasashen abin da zai faru nan gaba.

Ya girman cutar ƙyandar biri, sannan kuma a wadanne ƙasashe tafi yaɗuwa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cutar ƙyandar biri wato Mpox, wata ƙwayar cuta ce ke haifar da ita da ake kira da monkeypox.

Ta na daga cikin nau'ikun cutuka irin na cutar farankama, kodayake ita farankama bata illa kamar Mpox.

Ƙwayar cutar na ta samo asali ne daga dabbobi inda ta ke yaɗuwa zuwa bil adama, to amma yanzu abin ya zarta hakan.

An fi samun cutar a ƙauyukan da ke kusa da manyan dazuka a Afirka, misali kamar a ƙasashe irinsu Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

A irin wadanna yankuna, akwai ɗaruruwan mutanen da suka kamu da wannan cuta harma da wanda suka mutu ciki har da yara 'yan kasa da shekara 15 wanda su tafi shafa.

Nau'uka biyu na cutar na yaɗuwa.

Nau'in farko shi ne mai suna "Clade 1" ya fi yaɗuwa a tsakiyar Afirka.

Sai nau'i na biyu na cutar kuma shi ne "Clade 1b", wato shi ne sabon nau'in cutar mai matukar haɗari da ya kuma ya janyo kara yaɗuwar cutar a yanzu.

Cibiyar CDC, ta ce akwai an samu mutum 14, 500 da suka kamu da cutar ƙyandar biri, sannan akwai mutum fiye da 450 da suka mutu sakamakon cutar a tsakanin farkon shekarar 2024 zuw watan Yuli na shekarar.

Hakan ya nuna cewa an samu ƙaruwa da kashi 160 ciki 100 na masu cutar, sannan waɗanda suka mutu kuma sun ƙaru da kashi 19 ciki 100 idan aka kwatanta da irin lokacin a shekarar 2023.

Yayin da kashi 96 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ta ƙyandar biri ke a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, cutar na yaɗuwa zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda.

Wani nau'in cutar marar illa sosai da ake kira " Clade ll" na yaɗuwa a ƙasashen yammacin Afirka, wadda ta ɓarke a 2022.

Ita wannan nau'in cuta ta yaɗu a kusan ƙasashe 100 ciki har da wasu a Turai da Asiya, inda da wuya a samu cutar, to amma an shawo kanta ta hanyar yi wa waɗanda ke da yiwuwar kamuwa da cutar allurar rigakafi.

Akwai ƙarancin allurar rigakafin cutar ƙyandar biri da magungunanta a Congo, sannan kuma jami'an lafiya a ƙasar na nuna matuƙar damuwa a game da yaɗuwar cutar.

Mene ne alamomin cutar ƙyandar biri?

Alamomin farko sun haɗar da zazzabi da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da kuma ciwon gaɓoɓi.

Idan aka fara zazzabi, sai ƙuraje su fito a fuska daga nan sai su yaɗu zuwa sassan jikin mutum yawanci tafin hannu da kuma tafin ƙafa.

Ƙurajen wanda ke da ƙaiƙayi sosai ko kuma zafi, na sauyawa a hankali su zama maruru, daga na sai su fashe.

Ƙurajen na zama a jikin mutum tsawon makonni biyu ko uku, daga nan sai su washe.

To amma idan cutar ta yi tsanani ƙurajen kan yaɗu zuwa dukkan jikin mutum musamman baki da idanu da kuma gaban mutum.

Ta yaya cutar ke yaɗuwa?

Cutar ƙyandar biri na yaɗuwa tsakanin mutum da mutum ta hanyar haɗa jiki da wanda ke da ita ciki har da ta hanyar jima'i da numfashi da kuma sumbata.

Sannan ana daukar cutar ta hanyar taba abubuwa da mai cutar ya yi amfani da su kamar zanin gado da kayan sawa da ma tawul.

Sannan mu'amala da dabbobin da ke da cutar kamar biri da ɓera da kuma kurege ma na sanya wa a kamu da cutar.

A lokacin da aka samu ɓarkewar cutar a 2022, yawanci cutar ta yaɗu ne ta hanyar jima'i.

Yaɗuwar cutar da aka samu ma a yanzu a Congo ana alaƙanta ne da ta hanyar jima'i.

Su waye suka fi haɗarin kamuwa da cutar?

Yawanci ana samun cutar ne a tsakanin mutanen da suke yawan jima'i da kuma zaman da ke neman 'yan uwansu maza.Mutanen da ke jima'i da mutane da dama sun fi haɗarin kamuwa da cutar.

To amma duk wanda ya yi alaƙa da wanda ke da alamomin cutar ma zai iya kamuwa da ita ciki har da jami'an lafiya da kuma iyalan mutum.

Shawara ita ce a rinƙa kaucewa alaƙa ta ƙut da ƙut da duk wanda ke da cutar, sannan a rinƙa wanke hannaye da sabulu da ruwa idan akwai cutar a gida ko unguwa ko kuma garin da aka samu bullar cutar ta ƙyandar biri.

Abu na biyu kuma ga waɗanda ke da cutar to su killace kansu daga shiga mutane har sai sun warke.

sannan ga wanda ya warke daga cutar idan zai yi jima'i to ya yi rinƙa amfani da kororon roba har sai ya yi makonni 12 da warkewa, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ta yaya za a magance cutar?

Za a iya amfani da hanyar da ake bi wajen magance cutar farankama domin maganin cutar ƙyandar biri, to amma ba lallai a warke ba.

Za iya shawo kan ɓarkewar cutar ƙyandar biri ta hanyar yaɗuwar cutar musamman yin rigakafi.

Akwai alluran rigakafi uku da ake yi, to amma ana yi wa mutanen da ke da yiwuwar kamuwa da cutar ne rigakafin ko kuma waɗanda suka yi alaƙa ta ƙut da masu cutar.

Har yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya bata bayar da shawarar a yi wa kowa rigakafin ba.

A baya-bayannan Hukumar Lafiya ta Duniya ta buƙaci masu yin magunguna da su ƙara samar da rigakafin cutar saboda amfanin gaggawa, koda kuwa alluran rigakafin ƙasashe ba su amince da su ba a hukumance.