Alamomin kamuwa da cutar ƙyanda

Child's stomach with a measles rash

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar kariya da dakile yaduwar cututtuka sun yi gargadi tun karshen shekarar 2023 cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara. Sun fitar da sanarwar hadin gwiwar saboda raguwar da aka samu tsawon shekaru wajen yin rigakafin cutar.

A yanzu, cibiyar CDC mai dakile bazuwar cututtuka a shafinta na intanet ta ce barkewar cutar kyanda na faruwa a kowane yanki na duniya. Yemen da Indiya da Kazakhstan sune kasashen da ke da yawan mutanen da suka kamu da cutar.

Rahoton hadin gwiwar na WHO da CDC ya nuna cewa a 2022, mutanen da suka kamu da kyanda sun karu da kashi 18 cikin 100 yayin da mace-macen da ke da nasaba da cutar suka daga zuwa kashi 43 cikin 100 a fadin duniya sabanin adadin da aka samu a 2021.

Adadin ya kara yawan masu cutar zuwa miliyan tara sai 136,000 na mutanen da suka mutu - galibi tsakanin yara kanana.

WHO ta kuma ce a Turai, an samu karuwar cutar kyanda da ninki 30a bara. Fiye da mutum 30,000 ne aka ba da rahoton sun kamu da cutar a sassan yankin a 2023 sabanin 941 a shekarar 2022.

..
Bayanan hoto, Alamomin ƙyanda

Alamomin cutar ƙyanda

Sanannun alamomin cutar kyanda sun hada da:

  • zazzabi mai zafi
  • ido ya rika zafi da kaikayi ya kuma yi ja
  • tari da atishawa
  • rashin jin dadin jiki
  • bayyanar fari-farin abu kan harshe
  • kuraje a jiki wanda galibi ba su cika yin kaikayi ba amma suna bayyana bayan alamomin farko
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kurajen kyanda na fitowa a sassan jiki yan kwanaki bayan sauran alamominta sun bayyana

Kurajen na fitowa a kan fuska da bayan kunnuwa kafin su bazu zuwa sassan jiki.

Suna wahalar gani a bakar fata.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jetro Gonese ya rasa ganinsa saboda cutar kyanda a lokacin da yake da shekara biyu yayin da yake zama a Zimbabwe

Matsalolin da suka fi tsananta sakamakon kyanda akwai ciwon kunne da gudawa.

Wasu mutanen na iya fama da matsalolin da suka tsananta kamar cutar sanyi ta pneumonia da kumburin kwakwalwa da ake kira encephalitis a Ingilishi da kuma makanta.

Ta yaya ƙyanda ke yaduwa?

Kwayar cutar na bazuwa ne idan mai dauke da cutar ya yi tari ko attishawa.

Mutum na iya kamuwa da kyanda ta iska ko taba kwayoyin cikin iska sannan ka sa hannu kusa da hanci ko baki.

Mutane masu kyanda na iya yada cutar har sai akalla kwana hudu idan kurajen sun bayyana.

...

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Kyanda na halaka miliyoyin mutane kowace shekara kafin a samar da rigakafin cutar a duniya

Rigakafin MMR

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar WHO da CDC ta Amurka da Hukumar lafiya ta Burtaniya da sauran hukumomin lafiya a sassan duniya, kyanda cuta ce da ke saurin yaduwa. Cibiyar CDC ta ce kusan tara cikin mutum 10 da ba su samu kariya ba za su kamu da cutar saboda zama inda kwayar cutar take.

Ana iya kare kamuwa da cutar ta hanyar yin alluran rigakafi biyu na cututtukan da ke saurin yaduwa na MMR (Measles da Mumps da Rubella). Allurar na kare mutum daga kamuwa da cututtukan uku.

WHO ta ba da shawarar yara su karbi allurar rigakafin MMR na farko idan suna wata tara da haihuwa a kasashen da aka fi samun cutar. Ta ce ana ba da rigakafin na biyu yawanci daga wata 15 zuwa 18 da haihuwa.

Ta ce "Kafin a samar da rigakafin a 1963 da rigakafin da ya bazu ana samu barkewar manyan cututtuka duk shekara biyu zuwa uku da kehaifar da akalla mace-mace miliyan 2.6 kowace shekara."

WHO ta kara da cewa a yanzu an samu raguwar mace-mace sabanin lokacin da ba a samu rigakafi ba. A 2021, mutum 128,000 sun mutu saboda kyanda.

Sai dai ta ce galibin mace-macen yara ne yan kasa da shekara biyar duk da an samar da rigakafi mara hadari kuma mai karfi cikin farashi mai sauki.

Labaran ƙarya kan rigakafin MMR

An yi ikirarin karya da ke alakanta rigakafin MMR da matsalar galahanga.

Wani mai nazari na Burtaniya, Andrew Wakefield ya yi kuskure a ikirarin da ya yi na alakanta cutukan biyu a 1998.

Daga baya an yi watsi da bincikensa inda hukumar kula da aikin likita ta Burtaniya ta cire Mr Wakefield daga cikinta a 2010.

Babu wata hujja da ke nuna cewa rigakafin MMR na haifar da matsalar galahanga.

Wata yarinya 'yar gudun hijira daga Rohingya ta runtse idanunta lokacin da ake mata rigakafin MMR

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 2021, an bayar da rahoton kimanin yara miliyan 40 ba su samu rigakafin kyanda ba

Shakku kan rigakafin

Matasa da kuma manyan mutane ya kamata a yi musu rigakafin MMR idan ba a yi musu a baya ba.

Ko shakka babu, an samu raguwar rigakafin kyanda ta CDC da ta WHO tun bayan bullar annobar korona.

WHO ta ce: ''Annobar korona ta janyo koma baya wajen bibiya da kuma ƙoƙarin da ake na rigakafi. Dakatar da aikin rigakafin da kuma raguwar mutanen da ake yi wa da sanya idanu da ake yi kan al'uma, ya janyo miliyoyin yara da suka rasata na zaune cikin haɗarin kamuwa da cutar da ake iya magancewa.''

A 2021, rahotanni sun nuna kimanin yara miliyan 40 ne a faɗin duniya ba su samu rigakafin ba: miliyan 25 ba su samu wadda ake yi ba a karon farko, yayin da ƙarin wasu 14.7 ba su samu ta biyu ba.

Rabin waɗanda ba su samu wadda ake yi a karon farko ba, sun fito ne daga ƙasashe 10 da suka hada da: Angola, Brazil, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Habasha, India, Indonesia, Madagascar, Nijeriya, Pakistan, da kuma Philippines.

Manya za su iya kamuwa da ƙyanda?

A woman with measles rash on her face lies in bed in Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata da kyanda ta kama a Brazil

Kowa zai iya kamuwa da kyanda idan ba a yi rigakafin ba ko kuma ba a yi a baya ba. Sai dai ta fi zama ruwan dare tsakanin ƙananan yara.

A cewar WHO, CDC, NHS da dai sauran masu ruwa da tsaki, kyanda na yin illa ga mutanen da ke da mabanbatan shekaru.

Ko da akwai 'yan shekarun da ake ganin sun fi wahala idan ta kama su.

  • yara 'yan shekaru 5
  • mutanen da suka haura shekara 20
  • Mata masu ciki
  • Mutanen da ba su da sinadaren kariya mai ƙarfi a jikinsu, kamar masu fama da Cuta mai karya garkuwar jiki ko kansar jini.
A gloved hand drawing the MMR vaccine out of a bottle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samu raguwar rigakafin kyanda tun bayan bullar annobar korona.

Ana iya yin ƙyanda sau biyu?

Abu ne mai yiwuwa, amma ba sosai ba, kamar yadda hukumomi irinsu CDC da NHS da irin su Mayo Clinic suka bayyana.

Mayo Clinic ya ce kimanin kashi 93 na mutanen sun samu rigakafin kyanda kashi farko wadda ke ƙara ƙarfin garkuwar jiki. Bayan kashi na biyu, kimanin kashi 97 sun samu kariya.

Ga mutanen da ba su da tabbacin an yi musu rigakafin kyandar, gwajin jini zai iya tabbatar da haka.

A Amurka, manyan mutanen da ba su da garkuwar jiki mai ƙarfi, ana ba su shawara su je a yi musu rigakafin ko da guda ce.

A Burtaniya mutanen da aka haifa a 1970 za su iya kamuwa da kyandar, saboda sai a shekarar 1988 aka samar da rigakafin MMR.