Mece ce cutar kyandar biri, kuma me ke jawo ta?

An samu ɓullar cutar ƙyandar biri a Birtaniya a jikin wani mutum da ya je ƙasar kwanan nan daga Najeriya.
A wannan maƙalar, mun yi duba a kan cutar wacce ba a faye samunta ba, kuma ba a san ta sosai ba.
Yaya girman yaɗuwar cutar ƙyandar biri?
Cutar ƙyandar biri ce tana daga cikin nau'ukan cututtuka kamar su cutar ƴan-rani, duk da cewa ba ta faye yin tsanani ba kuma ƙwararru sun ce yiwuwar kamuwa da cutar ba shi da yawa.
An fi samun ta yawanci a yankunan karkara a ƙsashen Afirka ta yamma, waɗanda ke kusa da yankuna masu zafi da kurmi.
Yankuna biyu da cutar ta fi tsanani su ne - Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya.
Biyu daga cikin masu ɗauke da cutar a Birtaniya sun je ƙasar ne daga Najeriya, don haka da alama suna fama ne da cutar da aka ɗan samu ɓullar annobarta a Afirka ta yamma, wacce ba ta cika yin tsanani ba, kuma har yanzu ba a tabbatar da ita ba.
Mutum na uku da ya kamu wani ma'aikacin lafiya ne da ya ɗauki cutar a jikin ɗaya daga cikin marasa lafiyar.
Huɗu daga cikin waɗanda suka kamu da cutar a baya-bayan nan - uku a Landan suke, ɗaya kuma a arewa maso gabashin Ingila - kuma ba su da wata alaƙa da juna kuma ba su yi wata tafiya kwanan nan ba.
GA alama dai a Birtaniya suka kamu da cutar.
Hukumar lafiya ta UKHSA ta ce duk wanda yake da damuwa kan tsoron kamuwa da cutar to ya je ya ga likita, amma ya tabbatar ya tuntuɓi asibitin ya sanar da su zuwansa.
Mene ne alamunta?

Alamun farko-farko sun haɗa da masassara da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da ciwon gaɓɓai.
Da zarar an fara zazzaɓi sai ƙuraje su fesowa mutum, su kan fara fesowa ne a fuska, daga nan sai su yaɗu a sauran sassan jiki, musamman tafin hannu da hannu da ƙafa.
Ƙurajen, waɗanda sukan yi ƙaiƙayi sosai, da sukan sauya ne mataki-mataki, har sai sun yi saɓa, sannan a warke. Amma sunkan bar wa mutum tabo a jiki.
Cutar kan ɗauki tsawon kwana 14 zuwa 21 kafin ya warke.
Ta yaya ake kamu da ita?
Cutar ƙyandar biri na yaɗuwa ne idan wani ya yi alaƙa da mai cutar. Ƙwayar cutar kan shiga jiki ne ta fatar jiki, da wuraren shaƙar numfashi da kuma ta ido da hanci da baki.
Har yanzu ba a bayyana ta a matsayin wacce ake kamuwa da ita ta hanyar jima'i ba, amma ana iya yaɗa ta kai tsaye ta wajen jima'in.
Sannan kuma tana iya yaɗuwa idan aka yi mu'amala da dabbobi kamar su biri da ɓera da kurege, ko kuma wani abu da mai cutar ya yi amfani da su kamar kayan sakawa ko gadon kwanciya.
Yaya munin cutar yake?

Yawancin nau'ukan cutar ba su da tsanani, wasu lokutan ta kan yi kama da farankama, kuma cikin makonni ko kwanaki sai ta warke da kanta.
Cutar ƙyandar biri a wasu lokutan ta kan yi tsanani, kuma an ruwaito cewa ta sha jawo mace-mace a yankin Afirka ta yamma.
Yaya girman ɓarkewar cutar?

An fara gano cutar ne tun shekarar 1970 kuma tun daga sannan an sha samun waɗanda suka kamu da cutar a ƙasashen Afirka 10.
A shekarar 2003 ma an samu ɓarkewar cutar a Amurka, karo na farko da aka samu ɓullarta kenan a wajen Afirka.
Waɗanda suka kamu da cutar sun kamu da ita ne a jikin wasu karnuka da su kuma suka ɗauka a jikin wasu ƙananan dabbobi a ƙasar. A jumulla an samu mutum 81 da suka kamu, amma babu wanda ya mutu a cikinsu.
A 2017 kuma, an samu ɓarkewar cutar sosai a Najeriya, kusan shekara 40 bayan da ƙasar da samu ɓullar cutar. An samu mutum 172 da suka kamu da ita, kuma kashi 75 cikin 100 maza ne ƴan tsakanin shekara 21 zuwa 40.
Mene ne maganinta?
Babu wani taƙamaiman magani na cutar, amma ana iya shawo kan ɓarkewarta.
Sannan an tabbatar cewa allurar riga-kafin farankama na yin aikin kare ta da kashi 85 cikin 100, kuma a wasu lokutan ana amfani da ita.











