Me ya sa tsofaffi suka fi haɗarin kamuwa da cutar kansa?

Asalin hoton, Getty Images
Labarin kamuwar Sarkin Ingila, Charles da cutar kansa ya yi tasiri sosai a fadin duniya, tun daga sanarwar da fadar masarautar (Buckingham Palace) ta yi.
Shekarar Sarkin 75, wannan ya sa kwararru da dama suka yi amfani da wannan dama wajen kara fadakar da jama'a a kan yadda tsofaffi ke fuskantar hadarin kamuwa da cutar ta daji.
An dade da sanin cewa yawan shekaru na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cutar kansa.
Babbar cibiyar nazarin cutar kansa ta Amurka ta nuna cewa yawanci ana kamuwa da cutar a shekara 66 - kuma sama da rabin yawan sababbin wadanda suka kamu da cutar a Birtaniya, mutane ne da suka kai shekara 70 zuwa sama.
Akwai dalilai da dama da ke da alaka da kuma bayyana hakan.
Abu na farko kuma mai sauki shi ne, yayin da muke tsufa, sannu a hankali jikinmu yana lalacewa, inda kwayoyin halittarmu ke lalacewa saboda abubuwa da dama.
Wasu daga cikin abubuwan su ne yadda jikinmu ke gamuwa da tururin hasken rana da na maganadisun na'urori da sauran tarkace na duniya da abubuwan da ke gurbata muhalli da shan taba da shan barasa da raguwar karfin garkuwar jiki da ahrbuwa da kwayoyin cuta.
To a irin wannan yanayi yayin da muke kara shekaru na girma sai jikinmu ya kasa gyara kwayoyin halittar da suke lalacewa, wanda a dalilin hakan sai wasu kwayoyin halittar su rika sauya yanayi tare da hayayyafa a jikinmu - wanda wannan shi ne a karshe ka zama cutar ta daji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanayin aikin jikinmu da ke gyara kwayoyin halittar da suka lalace da kuma hana wannan rikida da hayayyafa ta kwayoyin shi ne ke kare mu daga kamuwa da kansa yayin da muke shekaru, kamar yadda Richard Siow, daraktan bincike a bangaren tsufan jiki a King's Kwalej da ke London.
''Yayin da muke tsufa, abubuwan da ke tabbatar da aikin kwayoyin halittarmu sai su fara rauni su rage aiki,'' in ji shi.
Bincike ya kuma nuna cewa karuwar wannan sauye-sauye na kwayoyin halittar jikinmu na dakile karfin da garkuwar jikinmu ke da shi na yakar kwayoyin cutar kansa.
Masashi Narita, wanda ke gudanar da bincike a kan kansa da tsufa a Jami'ar Cambridge ta Ingila, ya yi nuni ga wata fitacciyar hanya da aka sani kan yadda kwayoyin halitta ke aiki - wadda ake kira p53.
Wannan aiki ne da kwayoyin halitta ke yi wajen yi wa jiki garkuwa. To amma tasirinsa na raguwa yayin da jikin mutum ko dabba ke tsufa, saboda yawan sauyin yanayin kwayoyin halittar da ke wannan aiki.

Asalin hoton, FRANCIS CRICK INSTITUTE
A lokacin da aka samu sauye-sauye a kwayoyin halittarmu na jini, sai su rika sanya kwayoyin na kara girma da fadada yayin da mutum ke shekaru.
To wannan ba kasafai yake faruwa ba a tsakanin matasa, amma abu ne da ya zama ruwan-dare a jikin tsofaffi, wanda kuma yana da illa sosai.
Daya daga cikin illolin ita ce hadarin kamuwa da cutukan kansar jini.
Wata matsalar kuma ita ce ta samun sauyi a aikin kwayoyin halitta na garkuwar jiki da ke cikin jini.
Narita da abokanan aikinsa na bincike a kan cutar daji suna ta gudanar da nazari a kan sauye-sauyen kwayoyin halitta da ke haifar da cutar daji, da ke yawan kama tsofaffi.
Abin da ake burin ganowa a nan shi ne, me yake faruwa da jikin mutum ne.
Ya ce, ''mun dauke daya daga cikin wadannan kwayoyin halitta, muka sanya ta a jikin dabba muka duba abin da zai faru a tsakanin kwayoyin halittar dabbar.''
Ta wannan hanya mai binciken da abokanan aikinsa sun gano cewa, abin ya haddasa karuwar rauni ko raguwar aikin kwayoyin halittar, wanda kuma wannan ne daman ke faruwa idan kwayar halitta da ta ji rauni ko ta tsufa ta daina rarrabuwa da kuma girma.
Kwayoyin halitta da dama wadanda suka gaji ko suka tsufa za su iya sauya yanayin muhallin da suke ta hanyoyi da dama masu hadari, inda za su iya rage garkuwar jiki tare da kara hadarin kamuwa da cutar kansa.
To amma wadannan abubuwa kadan ne daga cikin misalan hanyoyin da tsufa zai iya haddasa hadarin kamuwa da cutar daji.
Akwai wasu sabbin bayanan da suka fara fitowa, na hanyoyi ma su ban mamaki da kuma hadari da ake ganin cutukan dajin na samuwa, kodayake har yanzu suna mataki ne na nazari ba a tabbatar da su ba.
Kwayoyin halittar da suka manta aikinsu
Kamar dai yadda mutum ke gamuwa da mantuwa yayin da yake tsufa, wanda hakan ke sa ya kasa wasu abubuwan, wasu masana a kan cutar kansa suna zargin cewa wasu kwayoyin halittar na jikin mutum su ma watakila suna gamuwa da mantuwa idan sun tsufa, ta yadda suke manta yadda suke rayuwa da kyau.
Kwararriya a cibiyar bincike kan cutar kansa a Ingila, Luca Magnani, ta ce wannan abu ne da ake bincike a kai a game da cutar kansar nono, wadda kila sauyin yanayin sinadarin da jiki ke fitarwa a lokacin da mace ta girma ta daina al'ada ke faruwa.
Hukumar lafiya ta Birtaniya (NHS) ta ce takwas daga cikin mata goma da ke da cutar kansa nono wadanda suka zarta shekara 50 ne.
Daya daga ckin dalilan da ke hadasa hakan, ba kawai a kan cutar kansar nono ba har ma yawancin cutukan daji da ke da alaka da yawan shekaru shi ne, yayin da ake girma ana samun rauni ko raguwar musayar sakonni a tsakanin kwayoyin halittarmu.
Farfesa Andy Feinberg na Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka ya ce, ''ana samun raguwar aikawa da sakonni sannan sakonnin na zuwa a daburce, kuma ba yadda za a iya dogaro da su ba a tsakanin sassan jikin mutum, yayin da muke tsufa.''
Masanin ya ce, ''ana samun karuwar surutu ko hayaniya wanda hakan ke haifar da rashin tabbas ko kara rikitarwa a kan sanin wace kwayar halitta jiki zai sa aiki ko kuma wacce zai dakatar.''
Ya kara bayanin da cewa, '' an gano cewa sassan kwayoyin halittar da ke gamuwa da wannan matsala ta surutu ko hayaniya kusan su ne suka fi hadarin haifar da kansa.''
To amma wannan binciken ka iya taimakawa wajen samar da sabbin hanyoyin yaki da cutar ta kansa.
Daya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen samar da maganin cutar daji ita ce ta yadda sinadaran da ke cikin magani za su iya sauya yadda kwayoyin halitta ke sauyawa su kai ga haifar da cutar, maganin ya mayar da kwayoyin halittar su koma aikinsu irin na da, na dakile kumburin da ke haifar da cutar ta kansa.
Kwararrun masana kimiyya a fannin magance yadda jiki ko mutum ke tsufa, a yanzu suna wani gwaji na sinadaran magungunan da za su iya zabar duk wata kwayar cuta mai illa, su kashe ta ba tare da sun yi illa ga abin da ke da amfani ga jikin ba.
A yanzu haka ana gwajin irin wadannan sinadari a jikin mutanen da suka tsufa jikinsu ya yi rauni, wadanda kuma suka tsira daga wasu cutukan na kansa, domin sanin ko sinadaran za su kara musu garkuwar jiki da ma lafiyarsu baki daya.
Idan gwajin ya yi nasara za a fadada amfani da sinadaran.
Richard Siow yana da kwarin gwiwa a kan nazarin.
Ya yi amanna cewa bincike kan sababbin hanyoyin ka iya magance illolin da ke da nasaba da tsufa, tare da tsawaita rayuwar mutum cikin koshin lafiya.
Kuma wannan zai iya yin tasiri sosai ga yawan al'umma a tsawon shekaru.
Ya ce, ''bayan wannan burin shi ne rage yawan kudin da ake kashewa wajen maganin cutar ta kansa,''
''Samar da kayayyaki da cibiyoyin kula da masu cutar na da tsada sosai, kasancewar mutane na dadewa suna fama da jinya.''











