Ranar Kansa Ta Duniya: Cutukan kansa mafiya haɗari shida da suka kamata ku sani

Kansar bakin mahaifa

Asalin hoton, Getty Images

Masana harkar lafiya sun yi ittifakin cewa kwayoyin halittun cutar kansa kan rarrabu, su girma su kuma yadu a sassan jiki, wanda muddin likitoci suka kasa gano hanyoyin da za su hana su yaduwa akan rasa rayuka.

Akwai dalilai da dama da masana suka bayyana cewa suna haifar da cuttukan kansa daban-dan a sassan jikin dan adam, da suka hada da shan taba sigari, cin abinci maras kyau, har ma da rashin motsa jiki.

Amma kuma sun ce yakan dauki shekaru da dama kafin wadannan abubuwa su haifar da cutar ta kansa.

Kamar yadda kungiyar lura da masu cutar kansa ta Amurka ta bayyana, a shekara 2020 an kididdige cewa za a samu sabbin masu kamuwa da cutar kansa kimanin miliyan daya da dubu dari takwas a Amurka, kuma kimanin mutane 606,520 ne za su mutu da cutar ta kansa.

Ga cutukan kansa biyar mafi hadari da suka kamata ku sani:

  • Kansar bakin mahaifa
  • Kansar hanji
  • Kansar mama
  • Kansar mafitsara
  • Kansar kwakwalwa
  • Kansar huhu
Short presentational grey line

1. Kansar bakin mahaifa

Kansar bakin mahaifa

Asalin hoton, Getty Images

Kansar bakin mahaifa kan tsiro ne a bakin mahifar mata. Kuma takan fi shafar matan da ke kan ganiyarsu, wato daga shekara 30 zuwa 45.

Masana sun ce yawancin matsalolin cutar kansar bakin mahaifa na faruwa ne sakamkon kamuwa da nau'in kwayar cutar da ake kira HPV, wacce galibi kan yadu ta hanyar ko wace irin mu'amalar jima'i tsakanin mace da namiji.

Amma kuma akwai irin nau'ukan wannan kwayar cuta ta HPv guda 100 da akasari ba su da hadari. Sai dai wasu nau'ukan sukan haddasa wasu sauye-sauye a cikin kwayoyin halittar bakin mahaifar da ka iya haifar da cutar kansar.

Amma kuma wadannan kwayoyin cuta ba sabbin abu ba ne, kana akasarin mata ba su cika kamuwa da kansar a dalilinsu ba.

'Alamomi'

Alamun kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa ba su cika bayyana ba, kuma ba sa haddasa wata matsala har sai ta kai makura.

Akwai alamu kamar fitar jini lokacin ko bayan saduwa, ko kuma a tsakanin jinin al'ada ko kuma wani sabon fitar jini bayan mace ta wuce lokacin yin jinin al'adar.

Duk da cewa jinin da ba na al'ada ko na haihuwa ba, ba yana nufin cutar kansar bakin mahaifa ba, amma yana da muhimmanci mace ta je ta ga likita.

'Matakan kariya'

Hanyoyin da suka kamata a bi wajen daukar matakan kariya daga cutar kansar bakin mahaifa su ne zuwa ganin likita aka akai don bincika bakin mahaifar da aka fi sani da "smear test".

Lokacin yin wannan bincike, za a dauki wani samfuri na kwayoyin da ke jikin bakin mahaifar sannan a auna su da madubin likitoci da ke gano cuta.

Mace za ta iya rage kaifin yiwuwar kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa ta hanyar daina shan taba sigari, saboda a cewa masana mutanen da ke shan taba sigari na da wahalar samun kariya daga kamuwa da kwayar cutar HPV da ka iya haddasa kansar bakin mahaifa.

Akwai kuma riga-kafin kamuwa da kwayar cutar ta HPV da ake kira Gardasil, da ke bayar da kariya daga nau'ukan kwayar cutar HPV hudu da akasari ke haddasa kansar.

Short presentational grey line

2. Kansar mama

Likita na duba hoton kansar mama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Likita na duba hoton kansar mama

Galibi an fi samun cutar kansar mama a tsakanin mata kamar yadda bincike ya nuna, kuma an fi samu galibi daga matan da shekarunsu suka kama daga 50 zuwa sama.

Amma kuma akwai yiwuwar warkewa idan aka gano cutar da wuri, in ji kwararru.

Don haka yake da matukar muhimmaci mata su rika zuwa ganin likita akai-akai ana duba lafiyarsu don gano idan akwai wasu sauye-sauye a jikin maman nasu.

Akan samu cutar kansar mama a tsakanin maza, amma ba kasafai ba.

'Matakan kariya'

Baya ga cewa har yanzu ba a gano dalilan da ke haddasa cutar kansar mama ba, ba zai yiwu kai tsaye a san ko za a iya daukar wasu matakan kariya ba.

Idan mutum na cikin hadarin kamuwa da kansar mama, akwai wasu hanyoyin matakan kariya da akan dauka don rage hadarin.

Bincike ya nuna cewa akwai alaka tsakanin cutar sankarar mama da kuma cin abinci mara gina jiki.

Duk da cewa babu takamaimen sakamakon binciken da ya bayyana hakan, amma kuma akwai ci gaba ga matan da suka kiyaye ta wasu hanyoyi kamar haka:

  • Rika cin abinc mai gina jiki
  • Motsa jiki
  • Rage kiba
  • Rage cin maiko
  • Rashin shan barasa

Bayanai sun kuma nuna cewa yawan motsa jiki kan rage hadarin kamuwa da cutar kansar mama. Haka kuma zai saukakawa wadanda suka riga suka kamu da cutar.

Short presentational grey line

3. Kansar huhu

Cutar kasar huhu nau'in kansa ce da aka fi yawan samu a fadin duniya.

A Amurka kansar huhun ita ce kan gaba wajen haddasa asarar rayuka.

An kuma fi danganta shan taba sigari wajen haifar da cutar, amma kuma za ta iya kama wadanda ba sa shan taba sigarin.

'Alamomi'

Ba kasafai kansar huhu ke saurin nuna alamu ba har sai ta girma a kusa da huhun sannan ta kara bazuwa a sauran sassan jiki.

Alamun farko-farko na cutar kansar huhu kan iya kasancewa yawan tari, da sarkewar numfashi da kuma tarin jini. Kana ana samun wasu alamu kadan kamar su ciwon baya, da ciwon kafada har ma da ciwon gwiwa.

Haka kuma, alamun cutar ka iya bambanta, wanda ya danganta ko mace ne ko namiji ya kamu da ita, ko mai shan taba sigari ko kuma wanda bai taba sha ba, har ma da batun yawan shekaru.

Kowa za iya kamuwa da cutar kansar makogwaro, kuma ko ba tare da yin gwaji ba akwai bukatar wayar da kai game da alamominta don gano cutar da wuri.

Akwai alamu da dama na cutar kansar makogwaro ta aka fi samu, duk da cewa za a iya danganta ta da wasu abubuwa.

Tari babu kakkautwa shi ne alamar da aka fi samu na cutar kansar makogwaro kuma zai iya kasancewa busasshen tari ko kuma mai majina, kana ya kan faru a ko wane lokaci a rana.

Mutane da dama kan yi watsi da yawan tari, su kan danganta shi da irin murar da aka saba yi lokacin sanyi, ko kuma kura da makamantansu.

Amma kuma, duk tarin da ya wuce fiye da 'yan makonni kan iya kasancewa alamun cutar kansar makogwaro.

'Sarkewar numfashi yayin motsa jiki'

Wannan ma wata alama ce da galibi ake dangantawa da cutar kansar huhu, (musamman ma ga wadanda ba su taba shan taba ba)

A lokuta da dama ba a cika kulawa sosai ba, akan danganta hakan da tarin tsufa ko kuma kiba.

Da zarar ka fahimci cewa kana gaza yi wani aiki ko kuma da zarar ka fara yi kana saurin gajiya, ka yi sauri ka ga likita.

Yana faruwa ne a lokacin da cutar kansar ta fara tsanani, da dama wadnda suka kamu da cutar kan fara ganin jini kadan na fita a cikin majina a lokacin da suka yi tari.

Alamun cutar kan kara tsanani inda maras lafiya kan yi tarin jinin da kan iya cika cokalin shan shayi biyu.

Haka kuma, alamun cutar ka iya bambanta, wanda ya danganta ko mace ne ko namiji ya kamu da ita, ko mai shan taba sigari ko kuma wanda bai taba sha ba, har ma da batun yawan shekaru.

Kowa za iya kamuwa da cutar kansar makogwaro, kuma ko ba tare da yin gwaji ba akwai bukatar wayar da kai game da alamonminta don gano cutar da wuri.

Akwai alamu da dama na cutar kansar huhu da aka fi samu, duk da cewa za a iya danganta ta da wasu abubuwa.

'Tari babu kakkautawa'

Tari babu kakkautwa shi ne alamun da aka fi samu na cutar kansar huhu kuma zai iya kasancewa busasshen tari ko kuma mai majina, kana ya kan faru a ko wane lokaci a rana.

Mutane da dama kan yi watsi da yawan tari, su kan danganta shi da irin murar da aka saba yi lokacin sanyi, ko kuma kura da makamantansu.

Ko kuma aka riga tunanin tari ne na mai shan taba sigari.

Amma kuma, duk tarin da ya wuce fiye da 'yan makonni kan iya kasancewa alamun cutar kansar huhun.

'Ciwon kirji'

Ciwon kirji kamar yadda wasu ke bayyana shi da ciwon huhu kan faru ne bayan mutum ya kamu da cutar kansar huhun; galibi an fi samu a farko-farkon kamuwa da da cutar.

Kuma wanda ya kamun kan rika jin zafi da kuma ciwo a zagayen mazaunin huhun, kana ciwon yakan kasance kamar yana fitowa daga cikin huhun ne.

'Ciwon baya'

Ko shakka babu ciwon baya kan faru a lokacin da mutum ya kamu da cutar kansar huhu, kuma yana dana cikin alamomin farko.

Hakan na faruwa ne saboda tsiron da cutar ke yi a mazauni da kuma gefen huhun wanda kan bazu zuwa sauran sassan da ke kusa da koda. Matsalar

Kumburin fuska da wuya

Da zarar cutar kansa ta kara tsananta ta kan haifar da kumburin fuska da na wuya har ma da kafadu.

Short presentational grey line

4. Kansar kwakwalwa

Kansar kwakwalwa kan faru ne a lokacin da kwayoyin halittar kansar suka yadu fiye da kima ta yadda ba za a iya dakatar da su ba.

Nau'ukan irin wannan cuta sun danganta ne ga yanayin yadda suke sake saurin yaduwa bayan yi wa wanda ya kamu magani.

Don haka akwai nau'uka masu saurin yaduwa da kuma wadanda ba su da karfin saurin yaduwar.

Kansar kwakwalwa kan shafi ko wadanne mutane- babu babba babu yaro, duk da cewa an fi samu a tsakanin wadanda suka manyanta.

Masana sun bayyana cewa mutane fiye da 11,000 ne aka gano kan kamu da matakin frako na cutar kansar kwakwalwa a Birtaniya a ko wace shekara,yayin da rasbi daga ciki ne ke kamuwa da matsananciyar cutar,

Cutar ta danganta ga shekarun mutum, da irin nau'in cutar a cikin kwakwalwar, da kuma yanayin lafiyar jikin mutum.

Galibi in ji masana, kusan mutane 15 cikin ko wane 100 da ke dauke da cutar kansar kwakwalwa kan rayu har na tsawon shekara 10 bayan kamuwa da it

'Alamomi'

Alamomin cutar kansar kwakwalwa sun danganta ne ga yanayi bangaren kwakwalwar da ta shafa.

Amma kuma alamun da aka fi sani su ne:

Ciwon kai

Suma

Yawan jin rashin lafiya da tashin zuciya, da amai da kuma jiri

Sauye-sauyen halayya, kamar saurin mantuwa da tabuwar kwakwalwa

Kasala ko kuma a wasu lokuta shanyewar barin jiki

Matsalar gani da kuma magana

Amma a wasu lokutan ba lallai ne a ji alamunba, ko kuma sukan bayyana ne sannu a hakali.

Short presentational grey line

5. Kansar hanji

Wani bincike da masana suka gudanar ya nuna cewa akwai akan samu babban tsaiko a tsakanin lokacin da mutane kan gano alamun cutar kansar hanji da kuma lokaci da aka ainihin gano cutar.

Wannan tsaiko da galibi ya kan kai watanni biyar, da hakan kan haifar da bazuwar cutar ta yadda kan iya kawo cikas waje warkarwa.

Yayin da gaskiya ne akasari mutanen da suke da alamun cutar ta kansar hanji ba su dauke da ita, amma akwai hadari tattare da tunanin cewa ba itan ba ce.

Don haka yana da matukar muhimmanci a san cewa alamomin cutar kansar hanjin don saboda mutum ya san hanyoyin daukar matakan gaggawa a daidai lokacin da za a iya warkarwa kafin ta bazu zuwa wasu sassan jiki.

'Alamomi'

Wasu daga cikin alamomin sun hada da murdawar ciki, yin bayan gida mai launin baki ko kuma ja, ko kuma sauyi a yanayin yadda mutum yake yin bayan gida, kamar yin gudawa ko kuma bayan gida akai akai.

Sauran alamomin sun hada da:

Ramewa

Rashin cin abinci

Kasala

Cutar shawara

Rashin isasshen jini a jiki.

Short presentational grey line

6. Kansar mafitsara

Masana sun bayyana cewa galibi wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar kansar mafitsara maza ne.

Akan kuma samu namiji daya cikin tara da ke kamuwa da cutar, amma kuma mutum daya kadai cikin 39 kan mutu da cutar.

Kusan kashi 80 bisa dari na mazan da suka kai shekara 80 na da kwayoyin halittar kansar a mafitsararsu.

Bayan kasancewa maza, akwai wasu dalilai da kan haifatr da cutar ta kansar mafitsara.

Akwai dalilai kamar na shekaru, da yanayin abinci, da kiba da tarihin cutar daga cikin dangi, da kuma yadda mutum yake tafiyar da rayuwarsa.

'Alamomi'

Ba a cika samun alamu kansar mafitsara na bayyana ba.

Akan yi tiyata ko kuma gashi iri daban-daban ne ga wadanda suke fama da cutar kansar mafitasara yayin da likitoci ke cigaba da sa ido kan marar lafiyar.

Babu wasu alamun gargadi na farko-farkon kamuwa da cutar kansar mafitsara.

Ba za ka ji alamun wani tsiro da ke girma ba saboda haka nba a jin wani ciwo. Zaka iya kamuwa da cutar har na tsawon shekaru ba tare da ka sani ba.

Don haka yake da muhimmanci a rika zuwa gawaji a kai a kai.

Da zarar girman tsiron ya haddasa kumburi a jikin hanyoyin jijiyoyin mafitsarar, kansar ta kan bazu a sassan da ke kusa da su, za ka iya jin alamu kamar:

Yawan jin fitsari da dare

Matsala wajen rike fitsar

Zubar fitsari da mutum ya yi dariya

Rashin iya yin fitsari a tsaye

Jin zafi lokacin yin fitsari

Fitsari da jini a ciki

Ciwon baya da kwibi da cinyoyi da kuma kugu

Ba wai su ne ainihin alamun cutar kansar mafitsarar ba, amma suna faruwa ne saboda cutar ta kai girma da ta toshe hanyar mafitsarar.

Amma kuma masana sun ce wadannan alamomi ba a kodayaushe ba ne suke nufin mutum yana da cutar kansar mafitsara ba, akwai wasu cutuka masu irin wadannan alamu.

Wannan layi ne