Harbin zuma 'na kashe kwayoyin halittar kansar mama' - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
Masana kimiyya a Australia sun ce bincike ya gano dafin harbin zuma yana kashe ƙwayoyin halittun kansar mama.
Dafin - na dauke da wasu sinadarai da ake kira melittin - wanda ake amfani kan kansa nau'uka biyu masu wuyar sha'ani.
Gano hakan ba boyayye ba ne, sai dai masana kimiyya sun yi gargadi cewa akwai bukatar sake inganta gwaji.
Kansar mama cuta ce da galibi ke adabar mata da dama a fadin duniya.
Yayin da ake da dubban sinadarai da ke iya yakar cutar a gwaje-gwajen da ake yi, masana na cewa kalilan ne kawai za a iya sarrafa su domin yi wa dan adam magani.
Harbin zuma a baya an taba gano yana dauke da sinadaran yaki da wasu rukunai na kansa kamar melanoma.
Wannan bincike na cibiyar lafiya ta Harry Perkins a yammacin Australia an wallafa shi a mujallar Nature Precision Oncology domin nazari a kai.
Me binciken ya gano?
An gwada dafin zuma sama da 300.
Dafin zuman an gano cewa yana da ''matukar ƙarfi'', a cewar Ciara Duffy, ƴar shekara 25 mai digirin-digirgir kuma ƙwararriyar da ta jagoranci binciken.
Akwai wani sinadari cikin dafin da ake gani yana kashe kansa a cikin sa'a guda, ba tare da wata illa mai ƙarfi kan ƙwayoyin halitta ba.

Asalin hoton, HARRY PERKINS INSTITUTE
Binciken ya kuma nuna cewa sinadarin melittin na iya daƙile da lalata sake girman kansar a ƙwayoyin halittu.
Yayin da ake samun wannan sinadari a dafin zuma, ana kuma iya samar da shi cikin ƙwarewa.
A al'adance, nau'i na uku na kansar mama - wanda shi ne mafi haɗari - ana iya maganinsa ta hanyar tiyata da gashi. Yana aukuwa ne cikin kashi 10 zuwa 15 na cutar kansa.
Za a iya amfani da shi nan gaba?
A ranar Laraba, daya daga cikin jagororin kimiyya ya bayyana binciken a matsayin wani abu na ''farin ciki fiye da kima.''
''Yana sake bayar da misali mai kyau yadda sinadarai da ake samu daga jinsin kwaro ke iya maganin cututtukan da ke adabar dan adam,'' a cewar Farfesa Peter Klinken.
Amma masu bincike sun gargadi cewa akwai bukatar su sake aiki domin ganin ko dafin zuma da gaske zai kawo karshen kansar.
Wasu masu binciken sun amince da hakan. ''Abu ne mai kyau,'' a cewar Farfesa Alex Swarbrick, daga cibiyar binciken lafiya ta Garvan da ke Sydney.
''Sinadarai da dama na kashe ƙwayoyin halittun kansar mama wanda ake iya samu daga jinsin ƙwari ko dabobbi.
''Amma akwai sauran aiki gaba domin sake tantance wadannan bincike,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.











