Yadda cutar kansar mahaifa ta yi basaja a matsayin jinin al’ada

Kelly Pendry

Asalin hoton, Family Photo

Bayanan hoto, Kelly Pendry

Wata dattijuwa wadda ta ke fama da cutar kansa wadda a yanzu ba za a iya maganin ta ba, tana bai wa mata masu matsalar rashin lafiya shawarar su rinka tsananta bincike kan matsalar tasu.

An dai kwashe shekaru ba tare da an iya gano cutar kansar da ake addabar ta ba.

Kelly Pendry, mai shekara 42 da ke zaune a Birtaniya, an gano a shekara ta 2021 cewa tana fama da wata nau’in kansar bakin mahaifa mai wuyar sha’ani.

To amma ta fara fuskantar zubar jini mai yawa na tsawon kwanaki a lokacin jinin al’ada da kuma ciwo mai tsanani ne a shekarar 2016.

Kelly na tunanin cewa kila da cutar ba ta yi muni ba a yanzu inda an gano ta da wuri.

‘Leiomyosarcoma’ wata nau’in cutar kansa ce da ba a cika samun ta ba, wadda ke kama mutum 600 cikin kowace shekara a Birtaniya.

Kelly, wadda ke da yara biyu, ta ce a lokacin farko da ta farko shaida wa likita halin da take ciki, ya ce mata “jikinki zai ɗauki lokaci (bayan juna-biyu) kafin ya dawo daidai.”

Ta ce an shawarce ta ta yi amfani da kwayoyin tsarin iyali. A wani lokacin kuma ta ce an rubuta mata wasu magunguna na rage damuwa.

Ta ce “sai na ji kamar na zama wata ƴar wasan kwaikwayo, na ji kamar ina yawan yin munanan tunani game da lamarin, na ji kamar ko dai ba na da hankali ne?”

...

Asalin hoton, Family Photo

To amma lafiyar Kelly ta ci gaba da taɓarɓarewa.

Ta ce “wani lokaci nakan shiga cikin matsanacin ciwo.”

“Kwanakin da nake samun zuban jini sun fi waɗanda ba na zubar da jini yawa. Sai kuma na rinƙa yin ƙibar da ban san daga ina na samo ta ba. Sai cikina ya yi katoto.”

‘Ta yaya kika daure?”

A watan Afrilun 2020 ne wani ƙwararren likita – wanda Kelly ta bayyana a matsayin ‘jarumi’ – ya yarda cewa lallai tana fama da lalura bayan da ya ji wasu ƙululai a cikinta.

“A karon farko na samu wanda ya gaskata cewa akwai wani abu,” in ji ta. “ya ce min ‘yaya kika jurewa?’ na ce masa ba na iya jurewa.”

Kelly da mijinta Pendry
Bayanan hoto, Kelly da mijinta Pendry
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Nuwamban 202, an gano cewa Kelly na ɗauke da wani abu da ke girma a bangon mahaifarta.

An fada mata cewar cire mahaifarta ne kawai mafita, to amma annobar korona ta sa an rinka ɗage lokutan da suka kamata ta ga likita har ta kai ga ba a samu yi mata aikin cire mahaifar ba.

Ya zuwa watan Yunin 2021, Kelly ta rinƙa samun zubar jini a kowace rana babu ƙaƙƙautawa, sannan cikinta ya yi girma “kamar mai ɗauke da juna-biyu ɗan wata tara.”

A wannan lokacin ne wani likita ya ce akwai yiwuwar tana da ɗauke da wata nau’in kansa da ake kira ‘sarcoma’ a turance, to amma ba a tabbatar da hakan ba har sai watan Nuwamban 2021 bayan da aka yi mata wasu gwaje-gwaje.

A wannan lokaci ne aka tabbatar wa Kelly cewa cutar kansar da take fama da ita ta kai mataki na huɗu, kuma ba za a iya magance ta ba.

“Wata malamar jinya ta ce mini kada na shirya wa bukin kirsimeti,” in ji Kelly.

Daga nan sai aka tura Kelly zuwa wurin likitan kansa a cibiyar kansa ta Clatterbridge Cancer Center da ke Liverpool, wanda ya ce mata zai yi bakin kokarin shi wurin ba ta kulawa duk da cewa ba za a iya magance cutar da ke damun ta ba.

Ta ce “ya ce mana mene ne muke so, muka ce masa yadda za a a tsawaita lokacin rayuwarta, iyakar yadda za a iya.”

Gashin kansa mai gajiyarwa

“Na ce ba zai yiwu a ce ba na nan ba a lokacin da yarana suka kai wani mataki, kamar lokacin da za su yi samarinsu na farko, ko samun budurwa ta farko da sauran su.

“A lokacin nan na yi tunanin cewa zan mutu kafin su kai shekara 10.”

An gudanar da gashi mai tsauri da matuƙar gajiyarwa sau uku, wanda hakan ya ƙara min lokacin rayuwa.

Shekara guda bayan gashin da aka yi, har yanzu tana fuskanta matsalolin da suka shafi gashin, kamar mummunar gajiya, da ciwo da kuma zafi.

Ta ce amma waɗannan matsaloli ko kusa ba su kai raɗaɗin ciwon da ta fuskanta ba a baya.

Sai dai har yanzu tana nan ɗauke da cutar kansa wadda take a mataki na huɗu.

Ta ce “mun ɗan samu sauƙi na shekara ɗaya, to amma mun san cewa a kowane lokaci ciwon zai iya ƙazancewa cikin ƙanƙanin lokaci.”

Kelly na son a cire mata mahaifa, to amma a yanzu ba a wannan batun.

“Halin da ake ciki shi ne ina da cutar kansa da ke a mataki na huɗu, kuma ba a yin aikin kansa domin tsawaita lokacin rayuwar mutum.”

A yanzu mijin Kelly na fatan zai samu kuɗi har fan 50,000 domin biyan kuɗin da za a yi mata aiki a Amurka.

Mijin Kelly, Michael Pendry na sa ran tara kudin da za a yi mata aiki

Asalin hoton, Family Photo

Bayanan hoto, Mijin Kelly, Michael Pendry na sa ran tara kudin da za a yi mata aiki

Ya ce “a can aiki na cikin kula da maras lafiya.”

Kelly ba ta son ta soki Hukumar Inshorar Lafiya ta Birtaniya, sai dai tana jin cewa an “hana ta amfani da wasu hanyoyin da za a kula da lafiyarta, waɗanda ana amfani da su a wasu ƙasashen.”

Michael zai gudanar da wani tattaki daga ƙauyen Ewloe zuwa garin Hanham da ke kusa da Bristol (nisan kilomita 290), a wani yunƙuri na tara kuɗin da ake buƙata domin yi mata aiki.

‘Ina gudu ina kuka’

Ya ce “idan na bari abin ya dame ni sosai...to zan iya yin gudu domin na samu sassauci.”

Jiya abin na ta damu na a zuciya “ina gudu ina yin kuka. Daga baya sai na ji sauƙi a zuciyata.”

Kelly na sane da abin da zai iya faruwa da ita a nan gaba, koda kuwa an yi mata aiki.

“Mun san cewa za a iya yin aiki a ciro cutar gaba ɗaya, amma mun kuma san cewa za ta iya dawowa.” In ji ta.

“Kawai dai muna son ƴaƴanmu su san cewa mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu. Ina ganin wannan zai kwantar musu da hankali.”

Kelly na sa ran cewa bayyana labarinta zai iya taimaka wa wasu.

Ta ce tana sa ran labarinta “ya kai ga wata, wadda tata cutar ba ta yi muni ba, yadda za ta buƙaci a ƙara tsananta bincike, ko kuma ta buƙaci a tura ta zuwa wurin babban likita.”

“Mukan tattauna kan lafiyar mata, da lokacin daina jinin al’ada, da haila, abin da nake fata shi ne za a samu ci gaba.”

A wata sanarwa da Hukumar lafiya ta jami’ar Betsi Cadwaladr ta fitar ta ce: “Muna jajanta wa Ms Pendry kan abubuwan da suka faru da ita, kuma za mu ƙarfafa mata gwiwa kan ta tuntuɓi likitanta, wanda mai zaman kansa ne wanda hukumar ta ɗauka haya, ta yadda za a yi bincike kan lamarinta.”

Cibiyar kula da masu cutar kansa ta Clatterbridge Cancer Centre ta ce ba za ta iya cewa komai ba kan lamarin da ya shafi marasa lafiya ba. Ta ce: “kasancewar kansar tata ta yi nisa har ta yadu zuwa wasu sassan jiki, gashi wanda zai taɓo kowane ɓangare na jiki shi ne kulawa mafi dacewa a maimakon yin aikin tiyata.”

“Muna aiki tare da masu aikin tiyata da ke yankinmu. Idan har tiyata za ta yi amfani, to za mu iya yi ga masu cutar kansa, koda kuwa irin wadda ba za a iya magancewa ba ce.”

“Mun san cewa rayuwa da cutar kansa wadda ta yi nisa sosai ba abu ne mai sauki ba, muna ƙarfafa wa Kelly gwiwa ta yi magana da masu lura da lafiyarta idan har akwai wani abu da ya shige mata duhu.”