Kotun Ƙolin Faransa ta amince da tsarin fansho da ake zanga-zanga a kai

Masu zanga-zanga

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun lashi takobin ci gaba har sai an soke dokar

Kotun kolin Faransa ta zartar da hukuncin amincewa da shirin gwamnatin Shugaba Macron na sauya fasalin tsarin fansho na kasar, wanda ake ta zanga-zanga a kansa.

Da wannan hukunci ana sa ran cikin sa'o'i 48, Shugaban zai sa hannu kan dokar, wadda ta kara yawan shekarun ritaya daga aiki daga 62 zuwa 64.

Haka kuma alkalan sun yi watsi da bukatar 'yan hamayya ta neman a yi zaben raba-gardama ko rafaranda kan batun, amma dai sun soke wasu bangarori na sauye-sauyen da dokar ta tanada bisa dalilai na saba doka;

Wannan hukunci a yanzu ya kara karfafa wa Shugaba Macron gwiwa da kuma dama ta doka domin rattaba hannu a kan tsarin, abin da ake sa ran ya yi nan da wasu sa’o’ duk kuwa da zanga-zangar da ake ta yi a kasar ta kin yarda da tsarin, wanda ya kara shekarun barin aiki daga 62 zuwa 64.

A Paris babban birnin kasar inda masu zanga-zangar ke tayar da wuta a sassa daban-daban, jami’an tsaro sun damke sama da mutum dari.

An yi zanga-zanga ta kwana 12 tun watan Janairu kan kin sauyin na tsarin na fansho.

Shi dai Shugaba Macron ya kafe cewa sauye-sauyen sun zama wajibi domin kare tsarin fanshon daga durkushewa.

A watan Maris gwamnatin ta yi amfani da wani ikon a musamman na tsarin mulki ta aiwatar da sauye-sauyen ba tare da majalisar dokoki ta kada kuri’a ba a kan batun.

A ranar Juma’a kungiyoyin kwadago suka yi yunkuri na karshe na neman kada shugaban ya sa hannu a dokar.

Kungiyoyin sun nuna cewa kotun ta yi watsi da wasu tanade-tanade shida da aka kara a tsarin, inda suka ce hakan ya sa abin da a da ya kasance babu adalci a cikinsa yanzu kuma ya ma kara rashin daidaito.

Daga cikin abubuwan da alkalan kotun su tara suka soke, har da wani tsari da ya bukaci kamfanonin da suke da ma’aikata sama da 1,000 da su dauki ma’aikatan da suka zarta shekara 55 aiki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ministan kwadago Olivier Dussopt ya yi alkawarin inganta tsarin daukar aikin mutanen da suka zarta shekara 50 a kokarin ganin ya kawar da damuwar da ake nunawa a game da tashin sabon tsarin kan albashi.

Hukumomi sun haramta zanga-zanga a gaban ginin kotun kolin a Paris har zuwa Asabar da safe, amma duk da haka tarin masu zanga-zangar sun kasance a kusa da harabar, inda jin hukuncin ke da wuya suka kara harzuka.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun lashi takobin ci gaba da bijirewa har sai an janye tsarin.

Bayan hukuncin an rika tayar da wuta a sassan birnin na Paris yayin da ‘yan sanda ke ta kokarin shawo kan lamarin, inda a wani lokacin har suna ma amfani da hayaki ma isa hawaye domin tarwatsa jama’a.

Kamar yadda masu tarzomar suka ja daga a Paris haka can ma a wasu sassan kasar ta Faransa irin su birnin Rennes da Nantes, da Lyon lamarin yake wani lokaci inda ake dauki-ba-dadi tsakanin jama’a da ‘yan sanda.

Duk da cewa fadar gwamnatin Faransar Élysée Palace ta ce shugaban a shirye yake a tattauna da shi kan batun domin samun maslaha.

To amma ana sa ran ya rattaba hannu kan dokar cikin kwana biyu da yanke hukuncin, inda ake saran ta fara aiki a farkon watan Satumba.

Shugabar jam’iyyar masu ra’ayin kawo sauyi ta La France Insoumise Mathilde Panot, ta ce za su ci gaba da zanga-zangar:

Ta ce, ‘’ Ba shakka a bangaren hadakar masu ra’ayin kawo sauyi za mu ci gaba da mara baya ga dukkanin gangami, dukkanin zanga-zanga, ta fannin kudi da kuma kasancewarmu a wurin.

Za mu mara baya ga gamayyar kungiyoyin kwadago mu jadda fiye da a baya cewa za mu ci gaba da fafutuka.

Kuma muna rokon Shugaban Kasa da kada ya ayyana wannan doka saboda idan ya yi wannan doka ,kamar yadda ita kanta kungiyar kwadago ta ce, to shugaban kasa ba zai kuma iya mulkin kasar nan ba.’’

Firaminista Élisabeth Borne ta rubata a shafinta na Twitter bayan hukuncin kotun cewa ba wanda ya yi nasara ba kuma wanda ya yi rashin nasara a kan batun.

Kungiyoyin kwadago sun yi kira ga ma’aikata a fadin Faransar da su sake fitowa su kwarara a tituna ranar 1 ga watan Mayu domin ci gaba da zanga-zanga ta kasa a kan sabon tsarin na fansho.

Mai fashin baki na siyasa a Faransar Antoine Bristielle ya gaya wa BBC cewa ba ya jin nan da wani lokaci za a kawo karshen zanga-zangar da ake ta yi a fadin kasar tun wata uku baya.

Domin sama da kashi 70 cikin dari na jama’ar na kin jinin sauyin.