Hotunan yadda ake gudanar da zanga-zanga a Faransa kan shekarun ritayar ma'aikata

j

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar farko ta yajin aikin kenan inda makarantu da harkokin sufuri suka tsaya cik, An yi zanga-zangar ce kan manufar gwamnatin Faransa ta sauya fasalin tsarin fansho a kasar wanda yaki karbuwa.Wani mai zanga-zanga dauke da allon da ke bayyana ra'ayinsa kan zanga-zangar da kungiyar 'yan kasuwa ta Faransa ta kira a birnin Toulouse da ke kudu maso yammacin kasar a ranar 19 ga watan 2023.
An dauki wannan hoto a ranar 19 ga watan Janairun 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na ɗaga tutoci da kwalaye tare da wake domin nuna kin amincewa da sabon tsarin da gwamnati ta shigo da shi na fansho
An dauki wannan hoto a ranar 19 ga watan Janairun 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata ɗauke da kwali an rubuta "Tashar jirgin kasa, aiki, kabari" kalaman da suke suka kan tsarin gwamnati da ma'aikata ke ganin ba su yi daidai da su ba.
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai zanga-zanga ɗauke da allon da aka rubuta "ɗaya cikin uku na talakawa na mutuwa ne a shekara 64, Macron sai dai ka ci kanka" wannan na zanga-zanga ne kan nuna adawa da sabuwar dokar yin ritaya daga shekara 62 zuwa 64.
v

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu maci a tsakiyar birnin Toulouse da ke kudu maso yammacin Faransa, macinsu ya haifar da tsaiko ga harkokin sufuri a kasar baki ɗaya.
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsakiyar birnin Toulouse kenan, inda masu zanga-zanga daga dukkan ma'aikatun kasar don nuna kin amincewa da sabon tsarin gwamnatin shugaba Macron.