Zaben Faransa : Shugaba Macron na neman mafita daga 'yan hamayya

Asalin hoton, Getty Images
A yanzu dai Mista Macron na cikin matsi na ya samu goyon baya daga abokan hamayyarsa domin samun damar aiwatar da tsari ko manufar sauye-sauyen gwamnatinsa.
Sai dai kuma babu daya daga cikin manyan jam'iyyun hamayya ta Marine Le Pen mai tsattsauran ra'ayin rikau ko kuma ta hadaka ta Jean-Luc Mélenchon mai ra'ayin kawo sauyi ta kare muhalli da ke da zakuwar aiki da shugaban.
Samun gwamnatoci na jam'iyyu marassa rinjaye ba abu ne da aka saba gani ba sosai a Faransa, kuma ga shi hadakar gwamnatin da Mista Macron ke jagoranta ta gamu da gibi na kujeru 44 da za su ba ta damar kasancewa da rinjaye.
Wannan ke nan na nufin dole ne Mista Macron ya nemi goyon bayan 'yan majalisa na manyan jam'iyyu daga masu ra'ayin rikau da kuma masu ra'ayin kawo sauyi, da za su taimaka wajen samar da rinjayen da yake bukata, wanda zai kasance abokin aiki.
Wani jami'i ya ce, wakilan jam'iyyu za su ziyarci fadar gwamnatin Faransar a yau Talata da kuma gobe Laraba, kowane daban-daban domin yin wannan babbar tattaunawa.
Masu sharhi na cewa watakila shugaban ya karkata wajen neman cimma yarjejeniya da masu ra'ayin rikau ‚yan Republican, kuma daman jagoran jam'iyyar, Christian Jacob, zai halarci tattaunawar.
Sai dai kuma kamfanin dillancin labarai na Faransar AFP wanda ya ruwaito cewa Ms Le Pen mai tsattsauran ra'ayin rikau za ta halarci taron amma Mista Mélenchon, mai ra'ayin kawo sauyi ba zai halarta ba.
Haka shi ma Olivier Faure na jam'iyyar Socialist da kuma Fabien Roussel na jam'iyyar Kwaminis tare kuma da 'yan hadakar masu ra'ayin kawo sauyi karkashin jagorancin Jean-Luc Mélenchon za su gana da shugaba Macron din.

Asalin hoton, OTHERS
Gwamnatin Faransar dai na ha-maza-ha-mata ta kauce wa samun nakasu bayan da ta rasa rinjayen da take da shi, inda wasu masu sharhi ke gargadin kasar kar ta kai ga shiga wani yanayi na wuyar mulka.
Haka kuma dole ne sai Mista ya sauya ministocinsa uku, wadanda suka rasa kujerunsu a zaben da aka yi ranar Lahadi.
Bugu da kari ga kuma barazanar da makomar Firaminista Elisabeth Borne ke ci gaba da fuskanta.
Zaben na karshen mako ya gamu da matsalar rashin fitar jama'a sosai abin da ya sa aka samu kauracewar masu kada kuria' da kashi 53 cikin dari.
Shugaba Macron ya fitar da jerin tsare-tsare da manufofi na magance matsalar tsadar rayuwa da ke karuwa.
Wani babban sauyi ma kuma shi ne na kara yawan shekarun ritaya daga aiki daga 62 zuwa 65, abin da yawancin masu zabe bas u yi maraba da shi ba.
'Yan hamayya daga bangaren masu ra'ayin rikau da kum masu ra'ayin kawo sauyi sun lashi takobin nuna tirjiya ga sauye-sauyen shugaban, kodayake bangaren Ms Le Pen, ya ce kila zai iya mara baya ga matakan domin kawar da matsalar tsadar rayuwar idan har za a yarda da shawarwarinsu











