Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakan da ake bi wajen zaɓen sabon Jagoran Addinin Iran
Kundin tsarin mulkin Iran da kuma dokokin Majalisar Masana ta Jagoran Addini sun fitar da tsarin da za a bi bayan rasuwar Jagoran Addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Majalisar mutum uku
Sashe na 111 na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa, daga lokacin rasuwar jagoran addini zuwa lokacin da Majalisar Masana za ta sanar da sabon Jagora, Majalisar wasu mutane guda uku ne za su tafiyar da ayyukan ofishin Jagora.
Wakilan wannan majalisa su ne Shugaban ƙasa, da Babban alƙalin ƙasa da kuma wakilin Majalisar Magabata wanda Majalisar lura da buƙatun gaggawa ke zaɓa.
Sai dai, wannan Majalisa ta Mutane uku ba ta da cikakken iko, kuma tana buƙatar amincewar kashi uku cikin huɗu na Majalisar lura da buƙatun gaggawa kafin aiwatar da abubuwa kamar haka:
- Yanke hukunci kan manufofin gwamnati
- Sanar da batun yin ƙuri'ar jin ra'ayi
- Ayyana yaƙi ko tsagaitawa
- Tsige shugaban ƙasa
- Cirewa ko naɗa babban kwamandan dakrun juyin juya hali ko shugabannin hukumomin tsaro ko na soji
Idan jagora ya shiga cikin wata lalauran da ba zai iya gudanar da ayyukansa ba saboda ciwo ko hatsari, wannan majalisar ce tafiyar da lamurra.
Zaɓen sabon jagora
Zaɓen sabon jagoran addinin Iran aiki ne da ya rataya a kan Majalisar Masana, wadda ke da kujeru 88 (idan akwai waɗanda suka mutu ana barin kujerarsu haka nan har sai lokacin zaɓe na gaba).
Shugaban wannan majalisa shi ne Mohammad Ali Movahedi Kermani. Hashem Hosseini Bushehri da Alireza Aarafi su ne mataimakansa.
Babu wanda yake shiga wannan majalisa har sai Majalisar Magabata ta Iran ta tantance shi.
Aikin wannan majalisa ne ta zauna da zaran aka samu giɓi a muƙamin Jagoran Addini.
Doka ta ce majalisar za ta iya zama matuƙar aka samu halartar kashi biyu bisa uku (wakilai 59) na jimillar wakilanta.
Zaɓen sabon Jagoran addini na buƙatar amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na wakilan majalisar da ke halartar zaman.
Hakan na nufin idan mutum 59 ke zama, dole a samu amincewar mutum 40 kafin a amince da zaɓen sabon Jagora, duk da cewa ana sa ran akasarin wakilan majalisar su halarci zaman saboda muhimmancinsa.
Wajibi ne dukkanin wakilan da suka zauna su sanya hannu kan takardar amincewa da abubuwan da suka faru a lokacin zaɓen sabon Jagoran.
Wane ne za a iya zaɓa a matsayin Jagoran Addini?
Sashe na 109 na kundin tsarin mulkin Iran ya zayyana ƙwarewa da abubuwan da ake buƙata sabon Jagora ya kasance yana da su, kamar ilimin da zai iya bayar da fatawa a ɓangarori daban-daban na shari'a, da siyasa, da hangen nesa da ƙalailaicewa, da juriya, da iya tafiyar da al'amura da kuma izza ta mulki.
Majalisa za ta duba ƴan takarar da suka cancanta
Majalisar Masana tana da wani ɓangare wanda aikinsa shi ne duba cancantar mutanen da ake ganin za su iya maye gurbin Jagora.
A halin yanzu wakilan ɓangare su ne:
1- Ahmad Hosseini Khorasani (wakilin Majalisar Magabata, ɓangaren shari'a)
2- Alireza Aarafi (wakilin Majalisar Magabata, babban shugaban ƙungiyar Al-Mustafa, wadda ke yaɗa aƙidar Shia a faɗin duniya, wadrundunar juyin juya hali da kuma ɗaukar sojoji ga rundunar Quds Force)
3- Mohammad Reza Modarresi Yazdi (wakilin Majalisar Magabata wanda ke da tsattsauran ra'ayi kan amfani da hijabi ga mata, da mabiya Baha'i)
4- Hashem Hosseini Bushehri (Mataimaki na farko na Majalisar Masana)
5- Mohsen Mohammadi Araki (tsohon shugaban ƙungiyar lura da addinan duniya, shugaban kotun tarayya ta Abadan da Khorramshahr)
6- Abolhasan Mahdavi (Limamin Juma'a riƙo na Isfahan)
7- Abbas Kaabi (wakilin sashen shari'a na Majalisar Magabata wanda ke yin wa'adi na biyar, ya taka rawa wajen samar da ƙungiyar Hezbollah)
8- Hassan Ameli (Limamin juma'a na Ardabil, wanda ya yi wa'adi uku a Majalisar Masana)
9- Ahmad Daneshzadeh Momen (Wakilin majalisar masa ta mataki na biyar)
10- Abolghasem Wafi (Wakilin Majalisar tuntuɓa ta Musulunci)
11- Ghorbanali Dari Najafabadi (Wakilin Jagoran Addini a lardin Markazi, tsohon babban mai shari'a kuma tsohon ministan tattar bayanan sirri)
Ba a bayyana ayyukan wannan hukuma sannan rahotonta kan kasance sirri ne na gwamnati.
Tsawon wane lokaci ake zaɓen Jagoran Addini?
Babu ƙayyadadden lokacin da aka ɗiba wa Majalisar Masana wajen zaɓen sabon Jagoran Addini, kuma tunda tsarin zaɓen majalisar mutum uku abu ne da yake a tsare da zaran aka samu tangarɗa, ba za a samu giɓi ba a harkar shugabanci.
To sai dai, idan aka yi la'akari da abin da ya faru a lokacin rasuwar jagoran addinin Iran na farko, Ayatollah Ruhollah Khomeini, an ga yadda Majalisar Masana ta hanzarta wajen ganin an zaɓi sabon jagora.
Ruhollah Khomeini ya rasu ne kimanin ƙarfe 10 na dare a ranar 4 ga watan Yunin 1989, inda Majalisar Masana ta kira zama washegari domin zaɓen magajinsa, kuma aka samu matsaya cikin sa'o'i.
Sai dai daga baya an yi sauye-sauye ga wasu ɓangarori da suka shafi zaɓen sabon jagoran addinin.