Ta yaya sauya ranar zaɓen 2027 zai shafi shirin jam'iyyu da ƴantakara?

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Alhamis ne hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta sanya sabbin ranakun gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da na gwamnoni da kuma na majalisun jihohi na 2027.

Tun da farko lokacin da hukumar zaɓen sanar ya gamu da suka, da kiraye-kirayen sauya shi, kasancewar ya zo daidai da lokacin azumin watan Ramadan na 2027.

Sa dai a cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabarairun 2025, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ta ce: "bayan yin gyara ga dokar zaɓe ta 2022, da kuma amincewa da dokar zaɓe ta 2026, hukumar ta yi gyara tare da sauye-sauye ga lokutan shirye-shiryen zaɓe da kuma na zaɓukan domin ya yi daidai da tsarin sabuwar doka".

A yanzu hukumar ta saka ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2027 a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin tarayya.

Sai kuma ranar Asabar, 6 ga watan Fabarairun 2027 a matsayin ranar zaɓen gwamnoni da na ƴanmajalisun jihohi.

Hakan na nufin saura ƙasa da shekara ɗaya kenan a gudanar da duka zaɓukan.

Abin da ya sa INEC ta sauya ranar zaɓe

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce ta sauya ranakun zaɓen ne sakamakon ƙorafe-korafen jama'a game da jadawalin da ta fitar tun da farko.

Yayin wata hira da BBC, ɗaya daga cikin masu magana da yawun hukumar zaɓen, Zainab Aminu ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne sakamakon yadda jama'a suka yi ta kiraye-kirayen sauya ranar.

''Hukumar zaɓen Najeriya, hukuma ce da ke sauraron ƙorafe-ƙorafen jama'a, don haka ne ta zauna da kuma sauya ranakun'', in ji Zainab Aminu.

Lokacin ya dace?

Dr Kabiru Sa'idu Sufi, Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai shairhi kan al'amuran siyasar Najeriya, ya ce sabon lokacin da INEC ta saka zai iya kasancewa mafi dacewa, duba da irin ƙorafe-ƙorafen da aka yi a baya.

''Idan aka yi la'akari da ƙorafe-ƙorafen da mutane suka riƙa yi a baya na saka zaɓen cikin watan azumin 2027, to yanzu za a iya cewa an magance waccan matsala, kuma za a kammala zaɓukan kafin azumin'', in ji shi.

Ya ce hukumar ta yi ƙoƙarin samar da wannan rana ce wataƙila saboda zama masalaha ga al'umma, kuma domin ganin ba ta saɓa wa kwanakin da aka ƙaddaye kafin ranar rantsuwa ba.

''Matsar da ranar gaba wataƙila ka iya shafar ranakun da doka ta tanada kafin rantsarwa'', kamar yadda ya yi karin haske.

Sauyin lokacin zai shafi shirin jam'iyyun?

Wasu na ganin wannan sauyi da aka samu na lokacin zaɓe ka iya shafar shirye-shiryen jam'iyyun siyasa da ƴantakara waɗanda ke ƙoƙarin tallata kansu ga masu zaɓe.

Musamman ganin yanzu saura ƙasa da shekara ɗaya a gudanar da zaɓukan.

Iƙirarin da Dr Sufi ya jaddada yana mai cewa dole zai shafi shirye-shiryen jam'iyyu da ƴantakara.

''A duk lokacin da aka sanya ranar zaɓen shirin ƴantakara da jam'iyyu kan fara daga wannan lokaci, don haka dole wannan ya shafin shirin nasu'', in ji masanin siyasar.

Ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da aka sauya ranakun zaɓe ba a Najeriya.

''Ko a 2015 ma an ɗage zaɓen shugaban ƙasa daga watan Fabrairu zuwa Maris, kodayake wancan ba ragi aka samu ba, mutane ba su yi ƙorafin sosai ba, amma tabbatar ya shafi shirinsu'', in ji shi.

To sai dai Dr Yakubu Haruna Ja'e, shugaban sashen koyar da kimiyyar siyasa na Jami'ar Jihar Kaduna cewa ya yi ga jam'iyya mai mulki, wannan abin yabawa ne domin a cewarsa jam'iyyar ta shirya wa zaɓen.

''Jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu a shirye suke game da wannan zaɓe, tun daga naɗa shugaban INEC, da irin sukar da aka nuna kan naɗin nasa, amma shugaban ya ƙi cire shi'', in ji shi.

Amma ga jam'iyu adawa malamin jami'ar ya ce babban aiki ne a gabansu.

Me ya kamata jam'iyyu da ƴantakara su yi?

Dr Sufi ya ce abin da ya kamata jam'iyyu da ƴantakara su yi a yanzu shi ne zage dantse da ƙarin ɗamara domin tunkarar babban aikin da ke gabansau na tallata kansu.

''Su yi ƙoƙari don tabbatar da cewa canjin bai haifar musu wani naƙasu ba, ta fuskar shirinsu, domin duk lokacin da aka samu irin wannan yakan zo da matsaloli musamman na ƙurewar lokaci'', in ji shi.

Ya ce kusanto da lokacin zai ba su damar farkawa su kuma tunkari babban aikin da ke gabansu.

''Batu ne da abubuwan da ake buƙata domin tunkarar zaɓen, yana da kyau su zauna su sauya shiri domin fuskantar abin da ke gabansu'', in ji masanin siyasar Najeriyar.

Shi ma Dr Ja'e ya ce da dama ƴan Najeriya na ganin zaɓen na da barazana mai yawa a cikinsa.

''Don haka yana da kyau jami'iyyun adawa su haɗa kai tare da ɗinke duk wata ɓaraka da ke tsakaninsu, don tunkarar illar da wasu ke ganin APC ta yi musu na zargin haifar musu da rikicin cikin gida'', in ji shi.

Sai dai jam'iyyar APC ta sha musanta zargin kitsa rikice-rikice a cikin jam'iyyun hamayya.