Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da NSCIA ta ce kan shawarar Amurka na soke dokar Shari'ar Musulunci a Najeriya
Majalisar ƙoli ta tabbatar da shari'a a Najeriya, (Supreme council for shari'a) ta mayar da martani inda ta soki shawarwarin da wani kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya bayar, wanda ya nemi a soke dokar Shari'ar Musulunci da kuma dokar hukunta yin ɓatanci a Najeriya.
Majalisar ta ce babu gudu ba ja da baya wajen yin duk mai yiwuwa na ganin an tabbatar da ɗorewar shari'ar musulunci a ƙasar.
Nafiu Baba Ahmad, babban sakatare na majalisar ƙolin ya shaida wa BBC cewa al'amari na shari'a hakki ne na musulmi.
"Babu wanda zai tursasa mu ya ce wai mu bar addininmu, ba gudu ba ja da baya komai za su yi sai dai su yi." In ji shi.
Ya yi zargin cewar,"dama Amurka da kasashen Turai da ma Isra'ila, abin da suke so ke nan wato duk inda musulmi suke sai aje a rusa su, sai kuwa suka samu abokan zamanmu."
" Idan batun kisa suke magana a kai, sau nawa ake kashe musulmi? Sannan wace kasa ce ta fito ta ce ana kashe musulmin? to tura ta kai bango don haka ba za mu lamunta ba." In ji shi.
Nafiu Baba Ahmad, ya ce matsayarsu ita ce a kan wadannan shawarwari na majalisar dokokin Amurka - "ba gudu ba ja da baya, kuma na fadawa Amurka da ma shi shugaban kasarmu ta Najeriya ya fadawa Amurka da ma su kansu abokan zaman namu su je su fadawa Amurka cewa musulmin Najeriya ba gudu ba ja da baya."
"Shari'a ita ce rayuwarmu duk inda masu rinjaye suke, su ne suke da ra'ayinsu da fahimtarsu da muradunsu, don haka dole suke zama abin da zai tafe da kasa."
"Su kuwa wadanda ba su da rinjaye, sai su yi hakuri da irin tsarin da suka tsinci kansu a ciki," in ji shi.