Tinubu ya tsawaita hana fitar da ƙwallon kaɗanya zuwa ƙasashen waje
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tsawaita hana fitar da ɗanyen ƙwallayen kaɗanya zuwa ƙasashen waje da tsawon shekara ɗaya, daga 26 ga Fabrairu 2026 zuwa 25 ga Fabrairu 2027.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce matakin na nuna ƙudirin gwamnati wajen bunƙasa masana’antu da ƙara darajar kayayyakin cikin gida, da kuma cimma manufofin shirin sabunta fata.
Sanarwar ta ce manufar tsawaita haramcin ita ce ƙarfafa sarrafa ƙwallon kaɗanya a cikin ƙasa da inganta rayuwar al’ummomin da ke noma ta.
Domin tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata, shugaban ƙasar ya ba da umarni ga ma’aikatu da hukumomi su haɗa kai wajen samar da tsari na ƙasa da zai daidaita manufofin masana’antu da kasuwanci da zuba jari a dukkan sassan harkar kaɗanya.
Gwamnatin tarayya ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke tallafa wa masana’antu na cikin gid tare da samar da ayyukan yi da ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar kayayyakin noma ta duniya.