'Dole a kauce wa amfani da kuɗi a harkar shari’ar Najeriya'

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci alƙalan ƙasar da su tashi haiƙan wajen kare mutuncin sharia, yana mai cewa al'umma na dogaro da kotuna ne, idan har kotunan suna adalci da bin tanadin tsarin mulki.

Shugaba Tinubun na waɗannan kalamai ne yayin da ake zargin ɓangaren sharia a Najeriya da katsalandan, inda masu suka ke zargin jiga-jigan ƴan siyasa da wasu manya da amfani da kuɗi wajen sauya akalar sharia – a yi hukunci na son-rai.

Shugaban ƙasar Najeriyar ya yi wannan kiran ne a taron shekara-shekara na alƙalan ƙasar na bana.

''Ba ta yadda za mu iya gina ingantaciyyar ƙasa ba tare da ɓangaren sharia mai adalci ba, mu sani cewa fa , ba wani gyara da zai yi nasara, ba tare da gaskiya ba''

''Dole ne a kaucewa amfani da kuɗi a harkar sharia, dole ne kotuna su kaucewa zama wata mafaka ta rashin adalci, cin hancin ko wane iri ne shi, kuma a kowane ɓangare na gwamnati yana raunana ƙasa, to amma a ɓangaren sharia yana rusa ƙasar ne baki ɗayanta''

''Idan aka rasa adalci gwamnati na rasa kimarta kuma dimokraɗiyya na rasa tushenta'' in ji shi

Masana irinsu Farfesa Nasiru Adamu Aliyu wanda babban lauya ne a Najeriya ya yi bayani a kan yadda hukunce -hukuncen alkalai da ke cin karo da juna ke damun wasu lauyoyin ƙasar.

''Abu ne wanda ya ke da girma, wanda kuma ya ke damun mutane, hatta lauyoyi waɗanda suke son su ga an yi adalci yana damunsu''.

''Domin za ka ga wasu abubuwa, waɗanda a zahiri ka san a doka da sharia bai kamata a yi su ba amma sai ka ga ana yi, kamar alƙali ya ɗauki hukunci ya ba oda wanda ya san bai kamata ya bayar ba''.

''Kusan alƙalan sun koma suna tsoro su yi hukunci wanda yake da alaƙa da gwamnati''.

Farfesa ya kuma dora alhaki kan ƴan siyasa inda ya yi misali da abinda da ke faruwa da babbar jam'iyyar hammaya ta PDP.

'' Ƴan siyasa su ne lamba ɗaya a kan karya ƙa'ida da kuma ƙoƙari su sa kotuna su yi abinda ba daidai ba'' .

''Dole ka san akwai matsala idan ka kalli matsalar PDP, nan na bada oda, can an ce a je a yi, me yasa a alƙali a can zai ga cewa ba ka kamata su yi ba, a can kuma ya ce ya kamata su yi'' in ji shi

Farfesa ya ce kiran da shugaban ƙasa ya yi bai isa ba, a ganinsa ya kamata a ɗauki matakin ladabtar da aƙalai masu karya ka'ida.

''Ya faɗawa alƙalan cewa daga yanzu kada su yadda wata gwamnati ko wani ɗan gwamanti ko ma'aikacin gwamnati ku bada hukunci ya ƙi bi, ku ƙyale shi, ya kamata a ɗauki mataki a kansa''.

Farfesan ya kuma ce dole ne a aiwatar da wasu sauye sauye masu tsauri idan ana son ayi gyara a ɓangaren sharia na ƙasar waɗanda suka haɗa da ɗaukar alƙalai waɗanda suka cancanta kuma su kasance masu tsoron Allah da kare mutuncin kansu.