Ƴan ƙwallo Musulmai da ke taka leda suna azumin Ramadan

Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da azumi ke cigaba da tafiya a sassan duniya, inda Musulmai ke ƙaurace wa cin abinci ko shan ruwa daga hudowar alfijir zuwa faɗuwar rana.

Wani abu da ya ɗauki hankali shi ne canjin da aka samu a duniyar ƙwallon ƙafa, inda ake ɗan dakatawa ana tsaka da wasa domin ba ƴan ƙwallo Musulmai dama su sha ruwa idan rana ta faɗi.

Wannan ya sa muka yi nazari kan wasu ƴan ƙwallo Musulmai da ke azumi a wannan watan na Ramadan a nahiyar Turai.

Mohamed Salah - Liverpool

Salah mai shekara 33 ɗan asalin Masar ne da ya kasance ginshiƙin Liverpool kuma ɗan wasan da ya kafa tarihi da dama a gasar Premier.

William Saliba - Arsenal

Ɗan wasan na Faransa mai shekara 24 na cikin ƴan wasan baya da suka fi ƙwazo a halin yanzu a duniya kuma Arsenal ta dogara da shi a ɓangaren tsaron baya.

Hugo Ekitike - Liverpool

Matashin ɗan wasan na Faransa da aka haifa a 2002, ya koma Liverpool bayan barin Frankfurt a 2025.

Amad Diallo - Man United

Ɗan wasan na Ivory Coast ya samu gurbi a ƙungiyar tun kakar 2024/2025. Mai shekara 23 ya kasance cikin ƴan wasan da United ke alfahari da su a yanzu.

Ousmane Dembele - PSG

Masour Ousmane Dembélé ɗan wasan ƙasar Faransa ne da aka haifa a ranar 15 ga watan Mayun 1997.

Ɗan wasan ƙasar Faransa a yanzu yake cikin gwarazan ƴanƙwallon da suka fi tashe a duniya.

Shi ne yake riƙe da kambun gwarzon ɗanƙwallon ƙafa na duniya wato Ballon d'Or.

Paul Pogba - Monaco

Paul Labile Pogba ma ɗan wasan ƙasar Faransa ne da aka haifa a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1993.

Yanzu ɗan wasan yana taka leda ne a ƙungiyar Monaco da ke fafatawa a gasar Ligue 1 ta Faransa.

Lamine Yamal - Barcelona

Lamine Yamal Nasraoui Ebana ɗan wasan tawagar Spain ne da aka haifa a ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2007.

Yanzu haka matashin ɗanwasan yana murza leda ne a ƙungiyar Barcelona da ke ƙwallo a gasar La Liga, kuma yana cikin zaratan ƴanƙwallon ke alfahari da su a harkar tamaula.

Antonio Rüdiger - Real Madrid

Antonio Rüdiger ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Jamus da aka haifa a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1993.

Yanzu yana taka leda ne a ƙungiyar Real Madrid da ke Spain, kuma take fafatawa a gasar La Liga.

Hakan Çalhanoğlu - Inter Milan

Hakan Çalhanoğlu ɗan wasan tawagar ƙasar Turkiyya ne da aka haifa a ranar 8 ga Fabrairun 1994.

Yanzu ɗan wasan yana buga ƙwallo ne a ƙungiyar Inter Milan da ke fafatawa a gasar Seria A ta Italiya.

Yunus Musah - Atalanta

Yunus Dimoara Musah ɗan wasan ƙasar Amurka ne da aka haifa a ranar 29 ga watan Nuwamban 2002.

Yanzu ɗan wasan yana buga ƙwallo ne a ƙungiyar Atalanta da ke fafatawa a gasar Serie A, a matsayin ɗan aro daga ƙungiyar AC Milan.