Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙalubalen da ke gaban sabon babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya
A ranar Talata, 24 ga watan Fabrairu ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da naɗa Olatunji Rilwan Disu a matsayin muƙaddashin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, bayan ajiye aikin tsohon mai riƙe da muƙamin Kayode Egbetokun.
A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Tinubu ya ce ya amince da ajiye aikin Sufeta-Janar Kayode Egbetokun "bayan ya miƙa takardar ajiye aiki bisa dalilai na iyali", sannan ya gode masa "bisa gomman shekaru da ya kwashe yana hidimta wa rundunar ƴansandan da kuma Najeriya".
A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, da sa ran zai yi jagoranci na tsawon shekara huɗu, zuwa watan Yunin 2027.
Sai dai tun bayan sanar da sabon naɗin aka fara tafka muhawara kan ƙalubalen da gaban sabon shugaban ƴansandan, musamman bayan ganin akwai wasu manyan hafsoshi da suke gaban shi.
Manyan ƙalubale
Zaɓen Najeriya na 2027
Tafiyar da lamurran tsaro a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2027 shi ne babban ƙalubalen da ke gaban Tunji Disu a matsayinsa na babban sufetan ƴansanda.
Wannan babban aiki ne, kasancewar abu ne da ya shafi ɗaukacin ƙasar.
Wajibi ne sufetan ƴansandan ya tabbatar cewa na tura jami'na ƴansanda a faɗin ƙasar domin tabbatar da doka a lokacin zaɓen, ta yadda za a hana ɓata-gari cin karensu babu babbaka, musamman abin da ya shafi tayar da rigingimu da kuma masu son yin magudin zaɓe.
Sai dai kafin babban zaɓen na Najeriya, akwai zaɓukan gwamna a jihohin Osun da Ekiti, waɗanda za a yi a 2026, inda a nan ne za a fara gwada ƙwarewar Disu.
Albashin ƴansanda da walwala
A shekarar 2018 tsohon shugaban Najeriya Muahammadu Buhari ya sanar da ƙarin albashin ƴansanda. To amma har yanzu ana kiraye-kirayen yin ƙarin albashi ga ƴansanda ta yadda zai wadace su, su iya buƙatunsu nay au da kullum ba tare da sanya ido kana bin hannun wasu ba.
Ya kamata Tunji Disu ya yi koƙarin ganin an biya ƴansanda albashi mai tsoka tare da tabbatar da walwalarsu.
Sauya yadda ake kallon ƴansanda
Mutane da dama a Najeriya na zargin cewa ƴansanda ba su tafiyar da ayyukansu bisa adalci da bin ƙa'ida.
Ya kamata Disu ya kawo sauyin da ya dace, ta yadda al'umma za su riƙa girmama ƴansanda da aikinsu fiye da halin da ake ciki a yanzu
Wani masani kan harkar ƴansanda, Dennis Amachree ya ce ɗaya daga cikin manyan ayyukan da suka rataya a wuyan Disu shi ne y asa ƴan Najeriya su riƙa kallon ƴansanda a matsayin abokansu.
Wannan ya sa muka zanta da Dr , wanda ya ce akwai manyan ƙalubale da Disu zai fuskanta idan ya fara aiki.
Sauran ƙalubalen
Da yake tattaunawa kan batun, Kabiru Adamu, masanin harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya lissafa wasu ƙalubale da ya ce sabon babban sufeton zai ci karo da su, kamar haka:
- Daidaita aikin ƴansanda da buƙatun ƴansiyasa. "Lokuta da dama ana samun bambanci da rashin fahimta kan yadda ƴansanda za su gudanar da aikinsu ba tare da katsalanda daga ƴansiyasa ba.
- Ƴansanda jihohi: "Tuni dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa yana so a kafa ƴansandan jihohi. Ke nan ya amince sannan ya fahimtar da ƴansanda su amince saboda umarni ne na shugaban ƙasa."
- Zargin cin zarafi: "An daɗe ana ƙorafi da zargin ƴansanda da cin zarafi da tauye haƙƙin ƴan ƙasa. Wannan aiki ne babba domin dole ya fahimtar da al'umma cewa ƴansanda abokansu ne."
- Makarantun horar da ƴansada: "Tuni Tinubu ya kafa kwamiti a ƙarƙashin gwamnan Enugu domin duba hanyoyin inganta wuraren horar da ƴansanda. Yana da kyau ya ba kwamitin goyon baya."
- Amfani da kimiyya: "Tun tuni majalisar ministocin Najeriya ta amince ayyuka 18 na ƴansanda su koma ta na'ura, amma har yanzu ba a fara ba. Ya kamata ya tabbatar an ɗabbaƙa."
- Sabuwar doka: "A shekarar 2020 an yi sabuwar dokar gudanar da aikin ɗansanda, amma akwai abubuwa da yawa da ba a duba ba. Ya kamata ya karkaɗe sabudar dokar, ya fara amfani da ita."
Ritayar manyan hafsoshi
A wani rahoto da jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito, aƙalla manyan hafsoshi guda 29 ne za su yi ritaya saboda naɗa Tunji Disu.
Daga ciki akwai muƙaddashin sufeto janar guda 28, da mataimakin sufeto guda 21 da suka riga Disu samun babban muƙami.
A game da wannan, masanin tsaron ya ce ba ƴansanda ba ne kaɗai suke da wannan tsaron.
"Kusan duk jami'an tsaro ne suka haɗa domin tabbatar da an ba sabon shugaban damar ya gudanar da aiki ba tare da tsaiko ba. Ana tunanin idan akwai wanda ya wuce shi, idan ya ba shi umarni ba dole ya ɗauka ba."
Sai dai Kabiru Adamu ya ce yana shawartar sabon babban sufeton da ya janyo kusa, "misali batun da ake yi na ƴansandan jihohi, zai iya ba su aikin kula da harkar domin a amfana da ƙwarewarsu.
Wane ne sabon sufeton
An haifi Olatunji Rilwan Disu ne a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Najeriya ranar 13 ga watan Afurilun 1966.
Ya shiga aikin ɗansanda ne a ranar 18 ga watan Mayun 1992, inda ake sa ran zai yi ritaya daga aiki a wannan shekara ta 2026.
Tunji Disu shi ne ya shugabanci sashen kai ɗauki da tattara bayanan sirri na rundunar ƴansandan Najeriya bayan sauke wanda ya gabace shi, Abba Kyari.
Haka nan ya riƙe muƙamin kwamandan Rundunar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Legas.
Ya kuma taɓa zama mataimakin kwamishinan ƴansanda a sashen tafiyar da lamurra na shalkwatar ƴansandan Najeriya da ke Abuja.
Ya taɓa zama mataimakin shugaban sashen binciken manyan laifuka a oishin ƴansandan Najeriya, a jihar Rivers.
Haka nan ya taɓa zama kwamandan tawagar ƴansandan Najeriya da aka tura yankin Darfur naƙasar Sudan ƙarƙashin shirin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
A ɓangaren karatu, Disu ya yi digirinsa na farko a harshen Ingilishi a Jami'ar Jihar Legas (LASU), sai ya yi digiri na biyu a harkar gudanar da mulki a jami'ar Adekunle Ajasin da ke jihar Ondo.
Ya kuma halarci kwasa-kwasai a Najeriya da ƙasashen ƙetare, kamar: Horo kan yaƙi da safarar ƙananan makamai a ƙasar Botswana, Horo kan zamba ta intanet a jami'ar Cambridge da ke Birtaniya, Kwas kan dabarun shugabanci a kwalejin horas da jami'an ƴansanda da ke Jos, Binciken ƙwaƙwaf da zaƙulo bayanai kan manyan laifuka a Jami'ar Legas, da dai sauran su.