Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙi ya ɓarke tsakanin Pakistan da Taliban
Jiragen yaƙin Pakistan sun kai hare-hare cikin ƙasar Afganistan, inda suka yi ruwan bama-bamai a wasu sassan Kabul da Kandahar da Paktia, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa tsakaninsu.
Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama da ƙasa kan yankunan Taliban da hedkwatar soji da wata cibiyar adana makamai.
Wani saƙon da ministan tsaron Pakistan, Kwaja Asif ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce yanzu sun fara yaƙi da Afghanistan yana mai cewa haƙurinsu ya ƙare. Tun da farko Taliban ta ce dakarunta sun kai hari kan jami'an tsaron kan iyakar Pakistan.
Wasu majiyoyi na Taliban sun ce aƙalla sojojin Pakistan 10 aka kashe, Pakistan kuma ta ce ta kashe dakarun Afgahnistan sama da 70.
Za a iya kwatanta ƙarfin ƙasashen biyu?
Akawai giɓi mai yawan gaske tsakinin ƙarfin sojin Pakistan da Taliban da ke Afghanistan.
Runsundar sojin Pakistan - mai makamanin nukiliya - na daga cikin rundunonin ƙasashe 15 mafiya ƙarfin soji a duniya.
Yayin da ita kuwa Aghanistan da Taliban ke mulkinta, ba ta da wannan makami, kuma tana fama da matsaloli nan da can.
Makaman da Taliban ke amfani da su galibi sun samu ne ta hanyoyi uku:
Na farko makaman da rundunar sojin Afghanistan ta bari, da na dakarun ƙasashen waje da suka fice daga ƙasar, da sabbin makaman da suka saya da wasu ciki har da ta haramtattun hanyoyi.
Masana sun ce bidiyoyin arangamar da aka samua a kan iyakokin ƙasashen biyu sun nuna cewa galibi dakarun Taliban sun yi amfani da ƙananan makamai.
To sai dai masana sun yi gargaɗin cewa mayaƙan Taliban na da ƙwarewa da yaƙin sari-ka-noƙe.
Ƴan Afghanistan za su kare ƙasarsu - Hamid Karzai
Tsohon shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, wanda ya mulki ƙasar daga 2002 zuwa 2014, ya ce ƴan ƙasar za su kare ƙarsarsu.
Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin na Pakistan, Mr Karzai ya ce ''Ƴan Afghanistan za su kare ƙasarsu ta hanyar cikakken haɗin kai a amkowane fanni, kuma za su mayar da martani kan duk wani hari da aka kai musu cikin ƙwarin gwiwa',, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
''Dole ne P{akistan ta sauya ƙudirinta, sanna ta rungumi makwabtanta da mutuntawa da girmamawa tare da mu'amala kyau'', kamar yadda ya bayana.
Karzai ya kasance cikin manyan ƴansiyasar Afghanistan ƙalilan da suka ci gaba da zama a ƙasar, tun bayan da Taliban ta ƙwace mulkin ƙasar a 2021.
China da Iran sun yi kiran shiga tsakani
Ƙasashen China da Iran sun yi tayin shiga tsakanin domin kawo sasanci a sabon rikicin.
China ta ce ta yi matuƙar ''damuwa'' game da tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu''.
Cikin wani saƙo da ma'aikatar harkokin wajen China ta fitar ta yi kira ga duka ɓangarotrin biyu ''su kai zuciya nesa tare da warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar tattauanwa''.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa China na yin duk mai yiwa domin shiga tsakani ta hanyoyin da suka dace, kuma za ta ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin ta hanyar sasanci.
"A matsayin makwabciya kuma ƙawa ga duka ƙasashen, mun yi matuƙar damuwa da wannan rikici da har ya janyo rasa rayuka'', kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Chinan, Mao Ning ya bayyana.
A nata ɓangare Iran - wadda ake yi wa kallon giwar ƙasashen Larabawa - ta ce a shirye take ta shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin.
Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wajen "sauƙaƙa tattaunawa" tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da rikici ya barke tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma yi kira ga ƙasashen biyu da su "warware bambance-bambancensu ta hanyar kyakkyawar makwabtaka da tattaunawa."
A baya, Iran ta riga ta yi tayin shiga tsakanin ƙasashen biyu a matsayin mai shiga tsakani yayin da zaman ɗar-ɗar kan iyakar ƙasahen ke ƙaruwa