Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 27 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Alƙalin da ke sauraron shari'ar El-Rufai ya ɗauki hutu

    Mai shari’a Justice Belgore, wanda ke sauraron ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El‑Rufai ya shigar na tauye masa haƙƙinsa ya sanar da cewa zai tafi hutu, lamarin da ya sa ya mayar da ƙundin shari’ar ga babban alƙalin babban birnin tarayya domin a sake ba wani alƙali daban ya ci gaba da sauraron ƙarar.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar

    Tun a ranar Laraba 25 ga Fabrairu ne kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa yau, 27 ga watan Fabrairu domin sauraron ƙarar wanda ke neman kotu ta tilasta kare masa haƙƙoƙinsa da yake zargin an tauye.

    Shari’ar na neman a ɗauki mataki kan hukumomin tsaro da suka haɗa da ICPC da EFCC da DSS da kuma Babban Lauyan Tarayya, bisa zargin take masa haƙƙinsa.

    An tsare El-Rufai ne tun bayan da ya kai kansa ofishin EFCC da kansa domin amsa gayyatar da aka yi masaa ranar Litinin 16 ga Fabrairu 2026, kafin daga bisani a daren 18 ga watan aka sauya masa wuri zuwa hannun ICPC.

  2. An kashe ƴan Ghana 55 a yaƙin Rasha da Ukraine

    Ministan harkokin wajen Ghana ya bayyana cewa ƴan Ghana 55 ne aka kashe a lokacin da suke faɗa a Ukraine, daga cikin ɗaruruwan ƴan Afirka da aka ce an yaudare su don su taya Rasha yaƙi.

    Ministan Sam Okudzeto Ablakwa ya ce "An sanar da mu cewa ƴan Ghana 272 da ake kyautata zaton yaƙin ya rutsa da su tun daga shekarar 2022, inda aka kashe 55, an kuma kama 2 a matsayin fursunonin yaƙi," in ji shi a shafinsa na X.

    Ya bayyan lamarin a matsayin "abin takaici da ban tsoro", yayin da ya ke magana bayan ganawa da takwaransa na Ukraine a Kyiv. Ablakwa ya rubuta cewa "Ba za mu iya rufe ido kan wadannan alƙaluman masu ratsa zuciya ba. Waɗannan ba lambobi ba ne kaɗai, suna wakiltar rayukan mutane ne," Ablakwa ya rubuta.

    Ukraine ta faɗa a ranar Laraba cewa sama da ƴan Afirka 1,780 daga ƙasashen Afirka 36 ne aka gano suna taya Rasha yaƙi.

    Ablakwa ya ce gwamnati ta himmatu wajen bin diddigi tare da wargaza duk wata makarkashiyar ɗaukar ma'aikata ba bisa ƙa'ida ba ta intanet.

  3. An gano manyan kaburbura biyu shaƙe da gawawwaki a Gabashin DR Congo

    Hukumomi a ƙasar Jamhuriyar Dimokraɗiyar Kongo sun ce sun gano maka-makan kaburbura biyu ɗauke da tarin gawawwaki a kusa da birnin Uvira da ke gabashin ƙasar.

    A baya bayan nan dai yankin ya kasance a ƙarƙashin ikon mayaƙan M23.

    Gwamnan lardin Kivu ta kudu ya ce aƙalla gawawwaki 171 aka gano a kaburburan.

    Ya ƙara da cewa ana zargin an kashe mutanen ne saboda zaton cewa suna goyon bayan sojojin gwamnati ko ƙungiyoyin mayaƙan da ke mara mata baya, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi ba.

    Ƙungiyar M-23 ba ta fitar da wata sanarwa ba har yanzu dangane da zarge-zargen.

    A baya dai an taɓa zargin ɓangarorin da ke rikici da juna da aikata kashe-kashe mutane da dama.

    Rahotanni sun ce mayaƙan da ake zargin na samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace Uvira na ɗan lokaci a wani farmaki na bazata a watan Disamba, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 1000 tare da raba kusan mutane 250,000 da muhallansu.

  4. Kotu ta ba da belin Malami

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da belin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami tare da ɗansa Abdulaziz Malami, kan kuɗin naira miliyan 200,

    Sai dai kotun ta umarce su da a tsare su a gidan yarin Kuje har sai sun cika sharuddan belin da aka gindaya musu.

    Mai shari’ar ta bayar da belin ne bayan ta saurari hujjojin neman beli da lauyansu, Joseph Daudu ya gabatar.

    Kotun ta ce dole ne kowannensu ya gabatar da mutane biyu a matsayin masu tsaya musu, inda ɗaya daga cikinsu dole ne yana da fili a unguwar Maitama ko Asokoro.

    Haka kuma sai an ajiye takardun mallakar filin tare da fasfo din masuntsaya musu a wurin Mataimakin Magatakardan kotu.

    Kotun ta kuma umarci Malami da ɗansa su miƙa fasfonsu da hotunansu ga kotu.

    An sanya ranar 4 ga Maris domin fara shari’ar.

    Hukumar tsaro ta farin kaya,DSS ce ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin tallafawa ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

  5. 'Rashin lantarkin Najeriya na da nasaba da ƙarancin isar gas a tashoshin samarwa'

    Hukumar kula da sauye-sauyen gwamnati kan samar da lantarki a Najeriya, NISO ta bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a ƙasar na da nasaba da ƙarancin isar gas zuwa tashoshin samar da wuta.

    A cewar hukumar, matsakaicin ƙarfin samar da wuta a yanzu na kusan megawatt 4,300 ya dogara ne da ƙarancin gas da ake samu a tashoshin samarwa.

    Hukumar ta ce tashoshin ne ke suke samar da mafi yawan wutar lantarki a ƙasar, don haka duk wani tangarda ko ƙaranci a isar gas yana tasiri kai tsaye kan ƙarfin samar da wuta da kuma yawan wutar da ke shiga kamfanin rarraba wutar.

    Hukumar ta yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki don ganin an dawo da cikakken isar wuta da zarar isar gas ta inganta kuma ƙarfin samarwa ya dawo yadda ya kamata.

    Duk da cewa wannan yanayi na iya haifar da matsala ga masu amfani da wuta, NISO ta yi kira ga jama’a da su fahimci halin da ake ciki a yanzu.

  6. Fadar shugaban Najeriya ta yi wa Atiku shaguɓe kan komawar Fintiri APC

    Fadar shugaban ƙasa ta yi wa tsoho mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar shaguɓe bayan sauya sheƙar gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, zuwa jam’iyyar APC, tana mai cewa matakin babbar koma baya ne ga burinsa na takarar shugaban ƙasa.

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta nsa na X ranar Juma’a.

    Ya ce sauya sheƙar Fintiri na nuna cewa Atiku ba shi da cikakken farin jini a jiharsa ta asali.

    Sanarwa ya ƙara da cewa "gwamna Finitri ya ɗauke wa Atiku duk wata ƙarfinsa ta jiharsa zuwa jam’iyyar shugaba Bola Tinubu ta APC.

    A cewar sanarwar, "ɗan takarar da ba shi da ƙarfi a garinsa ba zai iya tallata kansa ga sauran yankuna ba."

    Fadar shugaban ƙasar ta kuma shawarci Atiku da ya yi tunanin yin ritaya daga siyasar jam’iyya, tare da komawa “gidansa na biyu” da ke hadaddiyar Daular Larabawa musamman a birnin Dubai.

    Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin ƙasa da shekara guda, sauya sheƙar Fintiri na daga cikin manyan matsalolin da ka iya shafar shirin Atiku na sake tsayawa takara, tana mai cewa wannan lamari babbar barazana ce ga burinsa na siyasa.

  7. Tinubu ya amince da sabunta wasu manyan titunan ƙasar uku

    Shugaba Najeriya, Bola Tinubu ya amince da sabunta wasu manyan titunan tarayya a jihar Neja.

    Titunan da za a sabunta sun haɗa da itin Mokwa–Bida mai tsawon kilomita 120 da na Mokwa–Makera mai tsawon kilomita 63, da kuma titin Bida–Lanbata mai tsawon kilomita 123.5 wanda idan aka hada Jimillar tsawo da nisan titunan guda uku zai kai kilomita 306.5.

    A cikin wata sanarwa da ministan ayyuka David Umahi ya fitar ta hannu mai taimaka masa a harkokin yada labarai, shugaba Tinubu ya amince har da tsawaita titin Bodo–Bonny domin haɗawa da Titin Gabashin kasar zuwa amma

    Sanarwar ta ce za a kuma sanya fitilun tituna masu amfani da hasken rana a titunan.

    Minista David Umahi a sanarwar ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na sake gina irin waɗannan titunan da suke cikin muhimman hanyoyin tattalin arziki na ƙasa, waɗanda za su ƙara haɗin kai da kasuwanci, da ci gaban ƙasa.

  8. Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin satar mutane a hanyar Enugu zuwa Otukpo

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun daƙile wani yunƙurin satar mutane a hanyar Enugu–Otukpo, inda suka ceto mutum uku ba tare da wani rauni ba.

    A cikin sanarwar da ta fitar a shafina na X, rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Fabrairun 2026, lokacin da sojoji ƙarkashin Operation WHIRL STROKE suke gudanar da sintirinsu na dare daga sansaninsu da ke Otukpo.

    A yayin sintirin ne sojojin suka samu sahihan bayanai kan motar fasinjoji da ta saci mutanen inda sojojin suka tafi wurin nan take, suka bi sawun motar inda suka kama masu satar mutanen a hanyarsu ta tserewa.

    Sanarwar ta ce ba a samu wata arrangama tsakanin sojojin da masu garkuwa da mutanen ba saboda sun tsere inda suka bar mutanen da suka sace.

    Kakakin rundunar ya shawarci direbobi da su lura da rashin motsin motoci a tazara mai kimanin kilomita biyu da kuma dakata wa don tantance yanayi idan akwai abin da bai dace ba.

  9. China ta buƙaci a shiga tattaunawa kan yaƙin Afghanistan da Pakistan

    Ma’aikatar harkokin wajen China ta bayyana matuƙar damuwa kan tashin hankalin da ke ƙaruwa a kan iyakar Afghanistan da Pakistan inda ta buƙaci ƙasashen biyu su “warware duk wata matsala da bambance-bambance da nufin kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawa da sulhu.

    Ma’aikatar ta ce China tana “ƙoƙarin shiga tsakani wajen sasanta rikicin ta hanyoyi nata, kuma a shirye take ci gaba da taka rawar gani don rage tashin hankali da inganta dangantakar ƙasashen biyu.”

    Mai magana da yawun ma’aikatar, Mao Ning, ya ce "samun ƙaruwa a rikicin zai haifar da lahani da asara ga kasashen biyu."

    China ta nuna cewa kawo ƙarshen rikicin “yana cikin muhimman muradun ƙasashen biyu da al’ummominsu, kuma zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”

  10. Ani yi zanga-zanga kan hukuncin gwamnatin Habasha na cire wasu yankuna daga ikon Tigray

    Manyan zanga-zanga sun ɓarke a yankin Tigray na Habasha bayan gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin cire wasu ƙananan yankuna guda biyar daga ƙarƙashin ikon gudanarwar Tigray a zaɓukan ƙasa masu zuwa.

    Masu zanga-zangar sun taru a Mekelle da sauran birane, suna sukar matakin a matsayin “hukunci mai haɗari” da kuma “sanarwar shiga yaki.”

    Majalisar Tarayya ta yanke hukunci cewa yankunan da ake taƙaddama a kansu da suka hada da Korem Ofla, Raya Alamata, Humera, Adi Remets, da Tselemti ba za su kasance ƙarƙashin ikon Tigray ba.

    Hukuncin ya haifar da ƙiyayya daga yankin Tigray da jam’iyyun siyasa, da ƙungiyoyin farar hula, waɗanda suka bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba da sabawa yarjejeniyar Pretoria da ta kawo ƙarshen yakin Tigray a 2022.

    A gefe guda kuma jam’iyyar adawa ta NaMA ta yi maraba da hukuncin, tana cewa tana goyon bayan matsayar Majalisar Tarayya.

  11. Amurka ta yanke wa ɗan ƙasar hukuncin ɗaurin rai da rai kan lalata da yara a Burkina Faso

    Amurka ta yanke wa wani ɗan ƙasar mai suna Fode Sitafa Mara da ke da shekara 41 hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an same shi da laifin lalata da wasu ’yan mata biyu ƙanana yayin da yake aiki a ofishin jakadancin Amurka da ke Burkina Faso.

    Ma’aikatar shari’ar Amurka ta ce an yanke masa hukuncin ne ranar Laraba bayan shari’ar makonni biyu da aka gudanar a watan Oktoban 2025 a wata kotun tarayya da ke Maryland.

    Alƙalai sun same shi da laifuka huɗu na cin zarafin ƙananan yara mata ta hanyar lalata da kuma yunƙurin jan hankalinsu tare da yunƙurin hana gudanar da bincike.

    Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa laifukan sun faru ne tsakanin shekarun 2022 da 2023 a Ouagadougou, inda yake aiki a ofishin jakadancin Amruka a Ouagadougou.

    Shaidu sun nuna cewa an aikata laifukan ne a wani gida da aka tanada domin ma’aikatan diflomasiyya na Amurka.

    Rahotanni sun ce waɗanda aka cutar sun kasance ’yan mata masu shekaru 13 da 15 a lokacin da lamarin ya fara, kuma sun fito daga marasa galihu. ne

    Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin ya yi amfani da halin da suke ciki wajen cin zarafinsu tsawon kusan shekara guda.

  12. Shugabannin MDD sun yi tsokaci kan rikicin Afghanistan da Pakistan

    Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da shugaban hukumar kare haƙƙin bil’adama, Volker Türk, sun yi tsokaci kan halin da ake ciki a rikicin da ya barke tsakanin Afghanistan da Pakistan.

    Guterres ya yi kira ga ƙasashen biyu da su bi doka da ƙa’idojin kasa da kasa ba tare da tangarda ba, musamman ma dokokin jin ƙai na kasa da kasa.

    A nasa bangaren kum, Türk ya yi kira ga Afghanistan da Pakistan da su shiga tattaunawa don shawo kan rikice-rikicen kan iyaka da harin jiragen saman da ke kashe mutane,

  13. Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC

    Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance.

    A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha a ranar Juma’a, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

    Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin sauya sheƙar wasu gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria.

    Har yanzu dai babu cikakken martani daga shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa dangane da matakin gwamnan.

    A baya-bayan nan ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar, tare da ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan ya gabatar, matakin da wasu ke ganin tamkar zawarcin gwamnan ne.

    Matakin gwamnan na zuwa ne kwana biyu bayan kakakin majalisar dokokin jihar, Bathiya Wesley, ya fice daga PDP tare da wasu mambobin majalisar 13.

  14. Iran ta yi tayin shiga tsakanin rikicin Pakistan da Taliban

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wajen “sauƙaƙa tattaunawa” tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da rikici ya barke tsakanin kasashen biyu..

    Ya kuma yi kira ga ƙasashen biyu da su “warware bambance-bambancensu ta hanyar kyakkyawar makwabtaka da tattaunawa.”

    A baya, Iran ta riga ta ba da tayin shiga tsakanin ƙasashen biyu a matsayin mai shiga tsakani yayin da zaman dar-dar kan iyakar ƙasahen ke ƙaruwa

  15. Yaƙi ya ɓarke tsakanin Pakistan da Taliban

    Jiragen yaƙin Pakistan sun kai hare-hare cikin ƙasar Afganistan, inda suka yi ruwan bama-bamai a wasu sassan Kabul da Kandahar da Paktia, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa tsakaninsu.

    Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama da ƙasa kan yankunan Taliban da hedkwatar soji da wata cibiyar adana makamai.

    Wani saƙon da ministan tsaron Pakistan, Kwaja Asif ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce yanzu sun fara yaƙi da Afghanistan yana mai cewa haƙurinsu ya ƙare. Tun da farko Taliban ta ce dakarunta sun kai hari kan jami'an tsaron kan iyakar Pakistan.

    Wasu majiyoyi na Taliban sun ce aƙalla sojojin Pakistan 10 aka kashe, Pakistan kuma ta ce ta kashe dakarun Afgahnistan sama da 70.

  16. Yadda dajin Kainji ke neman zama maɓoyar ƙungiyoyin ƴanbindiga a Najeriya

    A farkon watan Fabrairun shekarar 2026 ne mahara sama da 100 suka yi dirar mikiya sanye da kayan sojoji a ƙauyukan Woro da Nuku da ke jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, inda suka kashe sama da mutum 75.

    Sun dira a ƙauyukan ne da yammacin ranar Talata a daidai lokacin da manoman ƙauyukan suke komawa gida daga gonakinsu.

    Babban abin da ya ja hankali shi ne yadda maharan suka aika da wasiƙar zuwa garin domin "wa'azi", sannan suka shiga, suka yi aika-aikarsu, sannan suke fice ba tare da fuskantar matsala ba.

    Bayan harin ne gwamnatin Najeriya ta zargi mayaƙan Boko Haram da kai harin, duk da cewa ƙungiyar ba ta ɗauki alhaki ba, duk da cewa ta fi gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya.

    A lokacin ne mutane suka fara tambayar wai daga ina maharan suka taso, kuma su wane ne su?

  17. Jam'iyyun adawa sun yi watsi da sabuwar dokar zaɓe

    Jagororin manyan jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi watsi da sabuwar dokar zaɓe ta 2026 da aka yi wa gyara wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu kwanan nan.

    Sun buƙaci majalisar Najeriya ta gaggauta fara sabon tsarin gyara dokar, suna zargin jam’iyyar APC da shirin amfani da gyaran wajen yin magudi a zaɓen 2027.

    Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar ne bayan majalisar dokoki ta yi mata gyara, amma tun kafin hakan ake ta ce-ce-ku-ce da zanga-zanga daga ɓangaren adawa da ƙungiyoyin farar hula.

    Waɗannan ɓangarori sun dage cewa wajibi ne a riƙa tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta na’ura maimakon tanadin amfani da tsarin takarda da ’yan majalisa suka saka.

    A wata sanarwa bayan wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce "shi da sauran shugabannin adawa ba su amince da sabuwar dokar ba saboda an gaggauta amincewa da ita ba tare da la’akari da muradun jama’a ba.:

    Ya kuma nuna goyon baya ga shugaban jam’iyyar NNPP, Dr Ajuji Ahmed, wanda ya soki sashe na 60(3) da ke bai wa hukumar INEC damar amfani da tsarin takarda maimakon nuna sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura idan aka ce an samu tangardar na'ura.

    A cewarsu, sabuwar dokar ta sabawa dimokuraɗiyya kuma yunƙuri ne na rage gaskiya da sahihancin zaɓe..

  18. Inec ta sauya ranar zaɓen shugaban Najeriya na 2027

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta sanya sabbin ranakun gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma na ’yan majalisun tarayya da na jihohi na kasar na 2027.

    Hakan na zuwa ne mako biyu bayan hukumar ta fitar da jadawalin zaben na farko, wanda ya sha suka daga bangarori da dama kasancewar ranakun da hukumar ta sanar za su iya fadawa cikin watan azumin Ramadana na shekarar 2027.

    Lamarin ya kai ga cewa majalisar dokokin kasar ta yi gyara ga dokar zaben kasar game da lokaci mafi kankanta na sanar da ranar gudanar da zabe.

    A jadawalin farko da hukumar ta fitar, ta sanya ranar 20 ga watan Fabarairun 2027 a matsayin ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, sai kuma 6 ga watan Maris 2027 a matsayin ranar zaben gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

    Sa dai a cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabarairun 2025, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a Mohammed Kudu Haruna, ta ce: “bayan yin gyara ga dokar zabe ta 2022, da kuma amincewa da dokar zabe ta 2026, hukumar ta yi gyara tare da sauye-sauye ga lokutan shirye-shiryen zabe da kuma na zabukan domin ya yi daidai da tsarin sabuwar doka”.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da ake kira da juma'atu babban rana.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.