Yadda jadawalin zaɓukan 2027 zai shafi azumin shekara mai zuwa

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da jadawalin zaɓukan shekarar 2027 mai zuwa.

Sanarwar na zuwa ne ƴan kwanaki bayan dambarwar da aka samu kan amincewa da sabuwar dokar zaɓen da aka samu a majalisar dattawan ƙasar.

Wannan ne karon farko da hukumar INEC za ta gudanar da babban zaɓen Najeriya ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan da aka naɗa shekarar da ta gabata.

2027 ta kasance shekarar zaɓe a Najeriya, wadda ta fi kowace ƙasa yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Me jadawalin zaɓen ya ƙunsa?

Cikin sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Juma'a ta ce za a gudanar da:

  • Zaɓen shugaban ƙasa da na ƴanmajalisun tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar mai kamawa.
  • Sai kuma zaɓukan gwamnoni da na ƴanmajalisun jihohi za su biyo baya, makonni biyu bayan nan, wato ranar 6 ga Maris, 2027.

A tsarin dokokin Najeriya shugaban ƙasa da mataimakinsa da gwamnoni da kuma mataimakansu na da damar tsawaita mulkinsu zuwa wa'adi biyu na shekara huɗu kowane.

Dama a dokar zaɓen ƙasar, akan fara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, kafin na gwamnoni.

Kodayake wasu sun yi yunƙurin kiran sauya wannan dokar, ta yadda za a fara da zaɓukan gwamna kafin na shugaban ƙasar, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

Yaushe za a yi zaɓukan fitar da gwani?

Hukumar zaɓen Najeriya ta kuma sanar da ranakun da jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaɓukan fitar da gwani na ƴantakararsu.

INEC ta ce jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fitar da gwani tsakanin 1 ga Yuli da 30 ga Satumbar 2026.

Sannan hukumar ta ce ƴantakarar za su miƙa sunayen ƴantakararsu daga ranakun 1 zuwa 31 ga Oktoban 2026.

Hukumar ta kuma ce za ta fitar da jerin sunayen ƴantakara na ƙarshe ranar 15 ga Nuwambar 2026.

Tsawon lokaci za a ɗauka ana yaƙin neman zaɓe

Hukumar zaɓen Najeriya ta kuma ƙayyade tsawon lokacin da jam'iyyu da ƴantakara za su ɗauka suna gudanar da yaƙin neman zaɓe.

INEC ta ce ƴantakarar shugaban ƙasa da ƴanmajalisun dokoki na tarayya za su fara yaƙin neman zaɓensu a hukumance daga ranar 18 ga watan Nuwamban 2026, zuwa 19 ga watan Fabrairun 2027, kwana guda kafin zaɓen.

Haka ma dangane da ƴantakarar gwamnoni da ƴanmajalisun dokoki na jihohi za su fara yaƙin neman zaɓensu daga 15 ga watan Disamban 2026 zuwa ranar 5 ga watan Maris ɗin 2027.

Ya batun rajistar masu zaɓe?

A tsarin dokar Najeriya sai wanda ya kai shekara 18 ne ke da damar kaɗa ƙuri'a.

Don haka ne hukumar zaɓen ƙasar ke gudanar da rajistar masu zaɓe a duk lokacin da kakar zaɓe ta gabato, domin bayar da dama ga waɗanda suka cika shekara 18 da waɗanda suka rasa katunansu don su sake mallakar wani katin zaɓen.

Tuni dai hukumar ta fara shirye-shiryen rajistar zaɓen ta hanyar amfani da yanar gizo.

INEC ta ce a ranar 6 ga watan Afrilun 2026 ne za a ci gaba da rajistar masu zaɓen, wanda za a ci gaba da hakan har zuwa watan Janairun 2027.

'Cikin azumi za a yi zaɓukan 2027'

Wani abu da ya ɗauki hankali game da ranakun zaɓukan 2027 shi ne gudanar da su a cikin watan Ramadan na 2027.

Bisa lissafin Kalandar Musulunci za a fara azumin 2027 tsakanin ranakun 8 da 9 ga watan Fabrairun 2027, sannan a yi Ƙaramar Sallah tsakanin 10 da 11 ga watan Maris na shekarar mai kamawa.

Sai dai wasu na ganin da yiwuwar a samu kiraye-kirayen ɗage zaɓukan zuwa bayan salla, saboda wahalhalun da ake fuskanta musamman a ranakun zaɓe.