Mene ne hukuncin mai yin ƙorafi saboda azumi?

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da azumin watan Ramadana ke ƙara nisa, watan da Musulmai ke ƙaurace wa ci da sha da abubuwan da aka haramta daga alfijir zuwa faduwar rana.

Lokaci ne da al'ummar Musulmi ke zage damtse wajen ibada domin samun rabo.

Wasu daga cikin masu bibiyar shafin facebook na BBC Hausa sun turo da tambayoyi waɗanda muka miƙa ga malamai domin amsawa.

Tambaya:

Daga Abdul Ahmed Suraj: Mene ne matsayin irin waɗannan maganganu da wasu mutane ke yi a lokacin azumin Ramadana:

  • Yau azumi babu sauƙi
  • Da ma a ce na manta na sha ruwa
  • Lokaci ba ya gudu

Amsa:

Sheikh Aminu Daurawa, malamin addini a Najeriya ya ce irin waɗannan kalamai ba su dace ga mai yin azumi ba.

"Wadannan maganganu ba su dace ga mai yin ibada ba, ya dinga nuna raki ko gajiya ko gazawa ta hanyar faɗar irin waɗannan maganganu. Mai bauta wa Allah dole sai ya yi haƙuri," a cewar Sheikh Daurawa.

Malamain ya ce kamata ya yi Ramadana ya zama watan da ake farin ciki da murna, da jin daɗi da zuwan sa.

"Allah na son ya tabbatar kai bawansa ne na gaskiya," saboda haka bai kamata a samu mai azumi da yin hakan ba.

Malamin ya bayyana wasu abubuwa biyar da ya ce Allah na yi wa ɗan'adam domin ganin yadda zai mayar da martani:

  • Ya (Allah) ce mu yi, saboda ya ga wane zai yi?
  • Ya hana mu, saboda ya ga ko za mu hanu?
  • Ya ba mu, saboda ya ga wane ne zai gode masa?
  • Ya hana wasu, saboda ya ga ko za su su yi hakuri?
  • Idan mun yi laifi, yana son mu tuba mu gyara.

A lokacin da mutum ke yin azumi, jarrabawa ce daga Allah domin ya tabbatar da imanin mutum.

Bai kamata a riƙa nuna raki da gajiyawa, a cewar malamin.

Kalamai na nuna gajiyawa ko ƙosawa "za su iya shafar ladan azumi, ko su tauye azumin ko kuma su rushe azumin," a cewar Malam Daurawa.

Sai dai malamain ya ce "babu laifi idan mai azumi ya ce 'ana rana', idan akwai zafin rana sosai, ko kuma mutum zai iya cewa 'ya gaji', idan ya yi wani aikin gajiya.