'Abin da ya sa ba za mu amince da duk wani sakamakon zaɓen da Shugaban INEC ya sanar ba’

Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake sabunta kiran da ta yi na a tsige Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC), Joash Amupitan, gabanin babban zaɓen 2027, inda ta bayyana shi a matsayin barazana ga amincin tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.

A wata hira da ya yi da BBC, shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya bayyana matsayarta kan shugban hukumar inda ya yi gargadin cewa Musulmin Najeriya ba za su amince ko halasta duk wani sakamakon zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Amupitan ba.

Sheikh Umar ya ce matsayar majalisar ta samo asali ne a kan abin da ta bayyana a matsayin abubuwan da shugaban hukumar ta INEC ya aikata a baya, musamman ma wani takaitaccen bayani na shari'a da ake zargin ya rubuta wanda ke nuna cewa ya amince da batun cewa ana yi wa Kirista kisan kiyashi a Najeriya – ikirarin da gwamnatin tarayya ta sha yin watsi da shi.

''Har yanzu muna kan bakarmu, saboda shi shugaban hukumar zaɓe bai fito ya musanta cewa wannan abun ba haka ba ne. Ya na nan kan iƙirarinsa, bai ma ga cewa wannan wani abu ne da zai fito ya yi magana a kai ba,'' in ji shi Sheikh Umar.

A cewarsa, matsayin da shugaban hukumar ta INEC ya ɗauka tamkar farfaganda ne mai raba kan jama'a tare da sanya shakku sosai kan ko zai iya adalci a matsayinsa na shugaban hukumar zaɓen Najeriya.

Shugaban majalisar ƙolin kan harkokin Shari'ar Musulunci a Najeriya ya ce: "Mu muna ganin duk wanda yake da irin wannan matsayi, ya kamata gwamnati ta sake nazari, saboda matsayi ne wanda yake da matuƙar muhimmanci, ana son a samu wanda babu ruwansa da ɓangaranci, mai adalci kuma wanda ke nuna ba sani ba sabo a kan abin da zai yi.''

Sheikh Bashir Umar ya ƙara da cewa "Abin da ya dace shi ne ya yi murabus, idan kuma bai yi ba ya kamata gwamnati ta yi masa murabus saboda duk abin da za a yi na zaɓen nan, wannan zai sanya rashin aminci a cikin zukatan mutane.''

A ranar Alhamis ne 23 ga watan Oktoba shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta inda ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya yi shekara 10 yana jagorantar hukumar.

A wajen bikin rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya buƙaci Amuputan ya yi aiki da gaskiya tare da kare tsarin zaɓe da mutuncin zaɓukan Najeriya da kuma ƙara ƙarfafa hukumar INEC.

Babban aikin da ke gabansa a halin yanzu dai shi ne shiryawa da kuma gudanar da babban zaɓen ƙasa na shekarar 2027.

Sai dai jim kadan bayan nada shi, muhawara ta kaure bayan da wasu kungiyoyi suka nuna shakku kan nagartarsa, bayan bankado wasu bayanansa a cikin wani korafi kan rikice-rikice a Najeriya, wadanda ya yi a lokacin da yake aiki a Jami’ar Jos.

Sai dai duk da zarge-zargen babu wani maryani takamaimai game daga hukumar ta Inec.

Wane ne Farfesa Amupitan?

An haifi Farfesa Amupitan ranar 25 ga watan Afrilun 1967 a garin Ayetoro Gbede da ke yankin ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Ya yi karatunsa na furamare da sakandire a Kwara, sannan ya halarci Kwalejin Fasaha da ke Ilorin daga 1982 zuwa 1984, sannan ya zarce jami'ar Jos inda ya karanta fannin shari'a daga 1984 zuwa 1987, inda ya zama lauya a 1988.

Ya samu digirinsa na biyu a fannin shari'a a jami'ar Jos a shekarar 1993, sannan ya kammala digirinsa na uku a dai jami'ar a 2007.

Ya fara koyarwa a hukumar wallafa ta jihar Bauchi bayan kammala yi wa ƙasa hidima a shekarun 1988 zuwa 1989.

A yanzu haka shi ne mataimakin shugaban Jami'ar Jos, kuma shugaban hukumar gudanarwar jami'ar Joseph Ayo Babalola da ke jihar Osun.

A yanzu haka Farfesa ne a fannin shari'a a Jami'ar Jos da ke jihar Filato.

A shekarar 2014 ne ya samu babban muƙamin lauyoyi na SAN.