Yadda Nijar ta zargi Faransa, Benin da Ivory Coast da hannu a kai mata hari

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta jinjinawa dakarunta da takwarorinsu na Rasha a bisa daƙile harin da aka kai wani filin jirgin saman ƙasar a ranar Alhamis.

An dai ɗora alhakin kai harin a kan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi, amma Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi Faransa da Ivory Coast da kuma Jamhuriyar Benin da mara masu baya.

An shafe sa'oi ana jin ƙarar fashewa da kuma musayar harbi a wajen da aka kai harin.

Ma'aikatar tsaron Nijar ta ce an kashe 20 daga cikin maharan, an kuma kama wasu 11, yayin da aka kashe sojojin Nijar hudu.

Wata kafar talabijin a ƙasar ta ce daga cikin waɗanda aka kashe harda wani ɗan ƙasar Faransa.

Ƙungiyoyi masu iƙirarin jihardi sun kai hare-hare a Nijar, tun bayan da Janar Tchiani ya ƙwace Mulki a 2023.

Janar ɗin ya yanke alaƙa da Faransa, wani lamarin da ya buɗe sabon babin ƙawance tsakanin Nijar da Rasha, amma har yanzu ƙasar ba ta iya cin galabar ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadin ba.

A wani jawabi da ya yi ta rediyo, Janar Tchiani ya zargi Faransa da Ivory Coast da kuma Benin da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin da ke kai hare-haren, duk da cewa bai bayyana hujjojin da za su tabbatar da hakan ba.

Dama dai gwamnatin mulkin sojin ta sha zargin Faransa da Benin da neman tarwatsa Nijar, zargin da ƙasashen biyu suka musanta.

Me masana tsaro ke cewa a kai?

Masana harkar tsaro a yankin Sahel irin su Dr Audu Bulama Bukarti na ganin cewa wannan hari manuniya ce kan yadda harkar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Nijar da kuma Sahel, kuma abin tashin hankali ne.

Dr Bulama Bukarti ya yi waiwaye kan yadda irin waɗannan nan hare-hare suka kusa durƙusar da ƙasar Mali a baya-bayan nan, inda aka riƙa kai hari kan motoci masu dakon mai, har abin ya shafi rayuwar yau da kullum.

Ya ce ''To gashi kuma an hari shi wannan filin jirgin sama na birnin Niamey ɗin, kuma ya kamat mu gane cewa wannan fa ba iya tashar jirgin sama bane. Akwai wani ɓangare da rahotanni ke nuna cewa kamar sansani ne na sojoji kuma akwai kayan aikin sojoji a wurin.

Sannan akwai wurin da aka ware a tashar, wanda wuri ne na ajiye jirage marasa matuƙa da aka saya, sannan kuma akwai makamashin Uranium da aka ajiye a wurin.''

Duk waɗannan abubuwa da ke cikin filin jirgin saman na birnin Niamey, abubuwa ne da Dr Bukarti ya ce taɓa su zai kawo babbar illa ga Nijar ta fuskar tsaro da kuma tattalin arziki.

Dangane da ƙungiyoyin da ake zargi da kai harin kuwa, sai Dr Bulama ya ce ''To ya zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai harin, ko itama gwamnatin Nijar duk da ta ce ƙungiyoyin ƴan ta'adda ne suka kai harin, ba ta faɗi ko su wane ne ba.

Amma mun san cewa ƙungiyoyin ƴan ta'adda da suke aika-aika a Nijar ko kuma ɓangaren Sahel, manya-manya guda biyu ne - Akwai JNIM wadda ke da alaƙa da Al-ƙa'ida sannan akwai kuma ƙungiyar da ke da alaƙa da ISIS da suke kiran kansu ISIS Greater Sahara Province.''

Masanin tsaron ya ce idan har ƙungiyoyin ta'adda ne suka kai harin to lallai ɗaya daga cikin waɗannan ƙungiyoyi da ya lissafa ne, kuma a bisa al'ada suna fitar da sanarwa mai tabbatar da su suka kai hari.

Ya ƙara da cewa wannan hari yana ƙara nuni da buƙatar yin hadin gwaiwa tsakanin gwamnatin Nijar da sauran ƙasashen Sahel domin tunkarar matsalar tsaro a yankin, domin kuwa a yanzu mayaƙan da ke addabar yankin suna amfana da wannan hali na rashin hadin gwiwa don yaƙi da su.