Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa bakwai da za su iya faruwa idan Amurka ta kai wa Iran hari
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Security correspondent
- Lokacin karatu: Minti 6
Bisa dukkan alamu take-taken Amurka na nuna cewa tana shirin kai wa Iran hari.
Sai dai, ba a san abin da sakamakon harin zai janyo ba, duk da cewa an san wuraren da za ta iya far mawa.
Don haka, idan har ba a cimma yarjejeniya da Tehran ba sannan Trump ya yanke shawarar kai hari, me zai iya faruwa bayan harin?
1. Hari kan shingaye, jikkatar fararen hula da komawa tsarin dimokuraɗiyya
Sojojin sama da kuma na ruwan Amurka na kai hare-hare, inda suke far wa shingayen dakarun juyin juya-hali na Iran da kuma ƴan sa-kai na Basij - waɗanda ke karkashin dakarun - ta hanyar amfani da muggan makamai masu linzami don wargaza shirin nukiliyar Iran.
Hakan zai iya janyo faduwar gwamnati da yiwuwar komawa tsarin dimokuraɗiyya inda Iran za ta sake haɗuwa da sauran ƙasashen duniya.
Sai dai ba lallai ba ne hakan ya faru. Mamaya da sojojin ƙasashen yamma suka yi a Iraqi da Libya bai sanya an koma mulkin dimokuraɗiyya ba. Duk da cewa an kawo karshen gwamnatocin kama-karya, da kuma shiga ruɗani da zubar da jini na tsawon shekaru.
Amma Syria, wadda ta gudanar da sauyi a baya baya-nan, ta hanyar kifar da gwamnatin Bashar al-Assad ba tare da taimakon sojojin yamma ba a 2024, na ɗan farfaɗowa a yanzu.
2. Gwamnati ba ta faɗi ba, amma ta sauya tsare-tsarenta
Wani abu da zai iya faruwa kuma shi ne, gwamnatin ba za ta faɗi ba duk da irin farmakin da Amurka za ta kai, amma za ta yi garambawul a tsare-tsarenta.
A batun Iran, wannan na nufin cewa gwamnatin Jamhuriyar Musulunci za ta tsira, wanda abu ne da Iraniyawa da yawa ba za su so ba, amma za a tilasta mata rage taimakon da take bai wa ƙungiyoyin mayaƙa a Gabas Ta Tsakiya, ragewa ko watsar da shirinta na nukiliya da makamai masu linzami da kuma rage gallaza wa masu zanga-zanga.
Wannan zai iya kasancewa ne a karshen farmakin.
Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta ci gaba da nuna turjiya da kuma kafiya na yin sauyi tsawon shekaru 47 da suka wuce.
3. Faɗuwar gwamnati, tare da maye gurbinta da mulkin soji
Mutane da dama na tunanin cewa wannan shi ne abin da zai iya faruwa.
Ƴan Iran da yawa na nuna cewa ba sa son gwamnatin, sannan duk zanga-zangar da aka yi tana ƙara rage farin jinin gwamnati.
Abin da ya sa zanga-zangar ta kasa tumɓuke gwamnati shi ne babu masu sauya ɓangare zuwa wajen ƴan boren, yayin da waɗanda ke iko kuma ke amfani da ƙarfin da suke da shi da kuma ƙarfin tuwo wajen ci gaba da zama a mulki.
Ruɗanin da zai biyo bayan harin Amurka a Iran shi ne, ƙasar za ta koma karkashin ikon mulkin soji mai ƙarfi wadda manyan jiga-jigan gwamnatin Jamhuriyar ta Musulunci za su kasance cikinta.
4. Iran za ta yi martani ta hanyar far wa Amurka da ƙawayenta
Iran ta sha alwashin mayar da martani kan duk wani hari da Amurka ta kai mata, inda ta ce "mun shirya mayar da mummunan martani".
Duk da cewa sojojin sama da kuma na ruwan Amurka sun fi ƙarfin Iran, amma hakan ba zai hana su kai hare-hare ba da muggan makamanta da kuma jirage marasa matuki, wanda yawanci suke ɓoye a ƙarkashin ƙasa ko kuma cikin manyan tsaunuka.
Amurka na da sansanonin soji a yankin Gulf, musamman ma a Bahrain da Qatar, amma Iran za ta iya zaben kaddamar da hari kan duk wata ƙasa da ta san tana ɗauke da muhimman kayakin Amurka, kamar Jordan.
Mummunan hari da makami mai linzami da aka kai wa kamfanin man ƙasar Saudiyya Aramco a shekarar 2019, wanda aka ɗora laifi kan mayaƙa da ke samun goyon bayan Iran , ya nuna yadda Saudiyya ke cikin barazana daga Iran.
Bisa ga alamu ƙawayen Iran Larabawa da kuma abokan Amurka na cikin fargabar cewa duk wani hari da Amurka za ta kai wa Iran, zai iya waiwayowa ya shafe su.
5. Iran za ta yi martani ta hanyar dasa nakiyoyi a yankin Gulf
An daɗe ana tunanin afkuwar haka a matsayin barazana ga fitarwa da kuma samar da mai a duniya tun lokcin yaƙin Iran da Iraqi a shekara ta 1980 zuwa 1988, lokacin da Iran ta dasa nakiyoyi kan hanyoyin kai man fetur - inda sojojin ruwa ne suka taimaka wajen cire su.
Mashigar Hormuz tsakanin Iran da Oman, mashiga ce mai muhimmanci.
Kusan kashi 20 na iskar gas da kuma kashi 25 na mai da sauran abubuwa na bi ta mashigar a kowace shekara.
Iran ta gudanar da atisaye cikin sauri na dasa nakiyoyi cikin teku. Idan ta yi haka to lallai lamarin zai iya shafar kasuwanci a duniya da kuma farashin man fetur.
6. Iran za ta yi martani, ta hanyar nutsar da jirgin ruwan yaƙin Amurka
Wani kyaftin ɗin sojojin ruwan Amurka da ke cikin wani jirgin ruwan yaƙi a yankin Gulf, ya taɓa faɗa min cewa wata barazana da yake tsoro daga wajen Iran ita ce "far wa jiragen ruwa".
A nan ne Iran za ta kaddamar da hare-haren abubuwan fashewa cikin sauri ta hanyar amfani da ƙananan jiragen ruwa masu yawa wanda zai yi wahala ga sojojin ruwan Amurka su lalata su cikin lokaci.
Rundunar sojojin ruwan gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta daɗe da sauya sojojin ruwan kasar da ke yankin Gulf, waɗanda aka horar da kwamandojinsu a birnin Dartmouth da ke Ingila lokacin mulkin Shah.
Nustar da jirgin ruwan yaƙin Amurkar, tare da yiwuwar kama ma'aikatan jirgin, zai zama wani babban abin kunya ga Amurka.
Yayin da hakan zai iya zama mai wahala, amma Al-Qaeda ta taɓa kai wa jirgin ruwan yakin Amurka hari a tashar jiragen ruwa na Yemen a shekara ta 2000, inda aka kashe ma'aikatan jirgin 17.
Kafin nan, a 1987 wani matukin jirgi mai saukar ungulu mallakin Iraqi ya harba makamai masu linzami biyu bisa kuskure kan jirgin ruwan yaƙin Amurka, inda ya kashe ma'aikata 37.
7. Faɗuwar gwamnati da shiga ruɗani
Wannan babban bala'i ne kuma yana ɗaya daga cikin abin damuwa da makwabtan Iran kamar Qatar da Saudiyya ke nunawa.
Yayin da akwai yiwuwar afkawa cikin yaƙin basasa, kamar wanda Siriya, Yemen da Libya suka fuskanta, akwai kuma barazanar cewa ruɗani da rashin tabbas ɗin da za a shiga, zai janyo rikicin kabilanci inda Kurdawa da Baluchis da kuma sauran kabilu marasa rinjaye za su yi koƙarin kare mutanensu a daidai lokacin da babu wani shugaba da ke iko a ƙasar.
Yawancin Gabas Ta Tsakiya za su ji daɗin ganin bayan Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci, musamman ma Isra'ila wadda tuni ta nakasar da ƙawayen Iran a faɗin yankin.
Sai dai, babu wanda zai so ganin ƙasa mafi girma a Gabas Ta Tsakiya - mai al'umma kusan miliyan 93 - ta faɗa cikin ruɗani, abin da zai janyo rikicin jin-ƙai da kuma matsalar ƴan gudun hijira.
Babban bala'i a yanzu shi ne shugaba Donald Trump, bayan girke sojoji masu ƙarfi zuwa kusa da iyakar Iran, zai yi tunanin ya ɗauki mataki ko kuma ya ji kunya a duniya, a yaƙin da ba a san karshensa ba da kuma abin da zai biyo baya.