Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 30 ga watan Janairun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Mayaƙan Iswap sun kashe sojojin Najeriya a harin jirage marasa matuƙa

    Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa mayaƙan Iswap sun kai hari kan sojojinta a garin Sabon Gari da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.

    Rundunar ta ce an kai harin ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, kuma ta ƙara da cewa mayaƙan sun yi amfani ne da jirage marasa matuƙa.

    A sanarwar da rundunar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji da ba ta bayyana adadinsu ba.

    Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba, ya ce an kai harin ne a wani sansanin soji da ke yankin, amma ya ce, "sojojin sun daƙile harin, sannan komai ya lafa."

    A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Mr Uba ya ce kafin harin, sojojin na Najeriya sun kai hare-hare a yankin Bulo Dalo, inda a cewarsa suka kashe mayaƙa 12, sannan suka kai wani harin a garin Garno shi ma na jihar ta Borno duka a ranar Laraba, inda a cewarsa a can ma suka kashe mayaƙan guda shida.

    Ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwace makamai da alburusai.

  2. Venezuela ta amince da dokar amincewa da masu zuba hannun jari a ɓangaren fetur

    Shugabar rikon Ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodriguez, ta sanya hannu kan wata doka da ta ba wa masu sha'awar zuba jari na kasashen waje damar shiga a dama da su, wani abu da canza tsarin gwamnati na shekaru da dama.

    Ana zargin dai Amurka ce ta tilasta yin hakan, bayan ta kama Shugaba Nicolas Maduro a farkon wannan watan, inda yanzu haka yake fuskantar shari'a a ƙasar.

    Shugaba Rodríguez ta bayyana wannan sauyi a matsayin mai cike da tarihi. Yayin da take sanar da matakin ga ƴan ƙasar a wani jawabi da ta gabatar ta talabijin, ta nuna dama can wanda ta gada Nicolas Moduro ya tsara yin hakan kafin a kama shi.

    Tun da farko, Mista Trump ya ba da umarnin bude sararin samaniyar kasar ga jiragen saman yan kasuwa.

  3. Gwamnatin Burkina Faso ta rushe jam'iyyun siyasa a ƙasar

    Gwamnatin sojin Burkina Faso ta rushe jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyi a ƙasar. Dama can tun a shekarar 2022 ne aka dakatar su, sannan kuma za a miƙa duka ƙadarorinsu zuwa ga gwamnatin ƙasar, kamar yadda kafar gwamnatin ƙasar RTB TV ta ruwaito.

    An amince da dokar rushe jam'iyyun ne a zaman majalisar zartarwar ƙasar, wanda shugaban sojin ƙasar, Ibrahim Traore ya jagoranta.

    Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Pingdwende Gilbert Ouedraogo ya ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin da aka yi kan rahoton binciken da aka gudanar domin inganta harkokin gwamnatin ƙasar, kamar yadda kafar Lefaso.net mai zaman kanta ta ruwaito.

    Kafin juyin mulkin watan Satumban 2022 a ƙasar, akwai jam'iyyun siyasa kusan 100 a ƙasar, inda guda 15 a ciki suke da wakilai a majalisar.

  4. Za mu mayar da martani idan aka kai mana hari - Iran

    Shugaba Trump ya ce yana son kauce wa ƙaddamar da harin soja a kan Iran, ko da yake al'amura na iya sauyawa idan har Tehran din ta ci gaba da shirinta na Nukiliya.

    Ya shaida wa 'yan jarida a birnin Washington cewa zai yi magana da Iran din. Tehran dai ta yi barazanar duk wanda ya ce kule, za ta ce masa cas.

    Wani babban jami'in sojan kasar Birgediya Janar Mohammad Akraminia, ya ce karfin sojinsu, ta kai su iya kai hari kan duk wani sansanin sojin Amurkar da ke gabas ta tsakiya.

    Da farko Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa sojojin Amurkar za su kai hari idan Tehran ta kashe fararen hula da ke zanga-zangar adawa da gwamnati ne, kafin daga bisani ya sauya tunani.

  5. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.