Mece ce makomar mataimakin gwamnan Kano?

Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da aka ci gaba da tattaunawa kan dambarwar siyasar Kano, yanzu haka hankali ya koma kan makomar mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam, wanda har yanzu bai fito ya sanar da komawa jam'iyyar APC ba.

Tuni dai jam'iyyar NNPP ta yi Allah-wadai da kiran da wasu suke yi ga mataimakin gwamnan ya sauka daga muƙaminsa, inda ta bayyana cewa tikiti ɗaya ne ya kai su kujerar da gwamna.

Tun farko, an ruwaito kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya yana shawartar mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon rashin bin gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce tafiyar da mulki na buƙatar cikakken aminci da fahimtar juna tsakanin shugabanni.

Ya bayyana cewa "Ci gaba da halartar tarukan majalisar zartarwa daga wanda ba ya tare da gwamnati a siyasance na iya zama barazana ga sirrin gwamnati."

Sai dai ya ce ra'yin mataimakin gwamnan bin gwamna Abba zuwa APC ko ya ƙi, amma ya ƙara da cewa "babu yadda za a yi wanda ba ya tare da kai ya ci gaba da halartar tarukan majalisar zartarwa," in ji kwamishinan.

"Wa ya san wanda zai iya bayyana wa muhimman bayanan gwamnati? Mulki yana tafiya ne bisa amana, kuma ba za ka iya yarda da wanda ba ya tare da kai ba," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa da shi ne da ya yi murabus.

Sai dai jam'iyyar NNPP, a wata sanarwa da kakakin jam'iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe mukaminsa.

Jam'iyyar ta buƙaci ɓangaren zartaswa a jihar da ya daina shiga al'amuran siyasa, ya tsaya kan ayyukan da kundin mulki ya ba shi damar aiwatarwa.

"Ci gaba da aikin mataimaikin gwamna yana da muhimmanci wajen ɗorewar shugabanci a jihar Kano," in ji sanarwar NNPP.

Jam'iyyar ta ƙara da cewa kwamishinan yaɗa labaran ba ya nan lokacin da ake gwagwarmayar kafa gwamnati, don haka ya ja bakinsa ya yi shiru.

'Zaman doya da manja'

Kabiru Sufi, wanda masanin harkokin siyasa ne a jihar ta Kano, ya ce ba yau aka fara samun irin wannan saɓanin ba a siyasar Najeriya.

Sufi ya ce a doka da ƙa'idojin siyasa, tikitin gwamnan da mataimaki tikiti ɗaya ne, "don haka mataimakin gwamnan yana da dama da ƴancin ci gaba da zama a kujerarsa, kuma ya ci gaba da zama a jam'iyyar da yake so," in ji shi.

Sai dai masanin siyasar ya ce lura da yanayin siyasar Najeriya, da ma yadda ƴan siyasar ƙasar suka mayar da lamarin a yanzu, "aiki tare yana da matuƙar wahala idan ya kasance gwamna da mataimakinsa ba jam'iyyarsu ɗaya ba."

Ya ce wasu daga cikin dalilan da kwamishinan yaɗa labaran Kano ya bayyana suna cikin dalilan da aka daɗe ana bayyanawa a matsayin hujjoji a baya.

"Ka ga kamar zaman majalisar zartarwa na jiha, shi ne babban wajen tattauna abubuwan gwamnati, kuma wataƙila akwai wasu bayanan da ba a so su fita ko makamancin haka. Irin waɗannan dalilan ne suka jawo matsala a lokutan baya," a cewar Sufi.

Masanin na siyasa ya yi waiwaye, inda ya ce a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, an samu rabuwar kai tsakanin shugaban da mataimakinsa, "amma sai rashin aminci da yarda suka shiga tsakani."

Ya ce a ƙarshe wasu ministocin lokacin sai da suka buƙaci mataimakin shugaban ya fita daga taron majalisar zartarwa.

"Domin kauce wa haka ne wasu lokutan ake ba mataimaki shawara ya sauka, ko kuma a bijiro da batun tsige shi, saboda matuƙar zai je taron, babu yadda za a iya hana shi shiga taron majalisar a matsayinsa na mataimakin gwamna."

Sufi ya ce matsalar kawai ita ce duk da kundin tsarin mulki ya amince da mataimakin zai iya ci gaba da riƙe kujerarsa ko da jam'iyyarsa daban ce, "shi kansa ba zai ji daɗin mulkin ba saboda ba zai samu damar gudanar da aikinsa da kyau ba."

Ya ce dalilai na siyasa ne suke jawo tankiyar, saboda a cewarsa zama za a riƙa na doya da manja, "za ka zaman babu daɗi sosai. Don haka ne idan ɓangaren gwamnan suka ji ba su gamsu ba, sai su bijiro da maganar tsigewa su tura wa majalisar dokokin jihar."

Masanin ya ƙara da cewa da zarar an fara batun tsigewa kuma, lamarin dole zai ɗauki sabon salo.

"Wannan kuma ya danganta ne irin yadda mataimakin ya ɗauki lamarin. Idan ya amince ya sauka shi ke nan, idan kuma sai da aka je batun tsigewa, sannan ya je kotu domin dakatar da su, to wannan ma zai ƙara jan lamarin. Wannan ne kuma zai ƙara rura rikicin siyasa."

Sufi ya ce wasu da zarar sun samu labarin matakin da ake so a ɗauka ne sai su haƙura su ajiye aiki.

"Ai a lokacin Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Hafeez ajiye kujerar ya yi kawai ya sauka da kansa," in ji Kabiru Sufi.

A ƙarshe masanin ya ƙara da cewa zaman tankiya za a riƙa yi da rashin amana a tsakanin "inda za ka ga ana samun tsangwama da rashin amana, ta yadda za ka ko da gwamna zai yi tafiya ba zai ba mataimakinsa riƙo ba saboda rashin aminci."

Lokutan da aka samu gwamna da mataimaki a jam'iyyu daban

  • Sokoto: A Sokoto, Alhaji Mukhtari Shagari ya ƙi bin gwamnan jihar, Magatakarda Wamako zuwa APC, inda ya tsaya a PDP ya nemi takara, amma ya faɗi a zaɓen fitar da ƴantakara.
  • Adamawa: A Adamawa ma haka aka yi, lokacin da gwamna Murtala Nyako ya koma APC, mataimakinsa James Bala Ngilari bai bi shi ba, amma suka ci gaba da aiki tare.
  • Kano: A Kano an samu irin haka a baya, inda lokacin da Abdullahi Umar Ganduje ya koma APC, Farfesa Hafeez Abubakar ya ƙi bin shi ya tsaya tare da Kwankwaso.
  • Legas: A Legas an samu shigen haka, inda Bola Tinubu da mataimakiyarsa ta farko Kofo Bucknor Akerele suka samu saɓani. Daga baya ta ajiye aiki bayan samun labarin yunƙurin tsige ta, inda ta koma PDP ta yi takara, amma aka doke ta a zaɓen fitar da gwani.
  • Sokoto: Aliyu Magatakarda Wamakko ma ya samu saɓani da Attahiru Bafarawa inda ya yi murabus ya koma PDP daga ANPP.