Yadda Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hari kan Iran

Lokacin karatu: Minti 3

Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hari kan Iran.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana hare-haren a matsayin “babban aiki” sannan ya yi kira ga gwamnatin Iran ta watsar da makamanta.

Tun farko, ministan tsaro na Isra’ila ya bayyana cewa Isra’ila ta kaddamar da “hari kan Iran”, inda aka ji karar fashewar abubuwa a fadin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan makonni ana yi wa juna barazana da kuma kokarin cimma yarjejeniya kan aikin nukiliyar Iran.

Ga abubuwan da muka sani:

Me ya faru a Iran?

Jim kadan bayan ƙarfe 9:30 agogon Iran, kafofin yada labarai a Tehran suka bayar da rahoton jin fashewar abubuwa a babban birnin kasar.

BBC ta nuna yadda hayaki ya turnuke a saman dandalin Jomhouri Square da kuma Hassan Abas Square.

Haka nan an samu rahotannin fashewar abubuwa a wasu biranen kasar, kamar Isfaham da Qom da Karaj da kuma Kermanshah. Har yanzu ba san wace illa hare-haren suka yi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Iran, Tasnim ya ce an rufe sararin samaniyar Iran tun daga lokacin da aka fara jin saukar harr-haren.

Trump ya bayyana lamarin a matsayin “babba kuma mai ci gaba.”

Wane martani Iran ta mayar?

Isra'ila ta ce ta gano cewa Iran ta harbo makamai masu linzami zuwa kasarta, amma ta ce tana aiki "wajen ganin ta kakkabo su tare kuma da kai farmaki a wuraren da take ganin barazana ce".

An ji karara fashewar abubuwa a birnin Haifa na Isra'ila da kuma wasu yankunan kaaar, sai dai babu tabbas ko makaman ne suka fada kan biranen ko kuma karar kakkabo su ne.

A yankin Gabas ta tsakiya kuwa, kamfanin dillancin labarai na Bahrain ya bayar da rahoton ya bayar da rahoton cewa "an kai harin makamai mai linzami" kan cibiyar gudanar da lamurra ta tawaga ta biyar ta sojin ruwan Amurka da ke kasar.

Hakan na zuwa ne bayan ma'aikatar harkokin cikin ta kasar ta ce an kunna karar ankararwar faruwar bala'i, sannan ta bukaci mazauna birnin su kwantar da hankalinsu amma su garzaya wuraren boyo mafi kusa.

Ma'ikatar tsaron Qatar ta ce ta yi "nasarar dakike hare-hare da aka yi niyyar kai mata", kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ruwaito bayan an ji kararrakin fashe-fashe a Doha, babban birnin kasar.

Kasar ce ke kunshe da sansanin sojin saman Amurka na Al Udeida, wanda shi ne mafi girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

An gargadi Isra'ilawa daga yin dandazo a wuri daya kuma an gargade su kan zuwa makarantu ko ayyuka har sai idan hakan ya zama dole.

Hukumomi sun ce wadannan sharudda za su ci gaba da aiki har zuwa karfe takwas na dare a ranar Litinin.

Kafofin yada labarai a Isra'ila sun kuma ce an rufe tashi da saukar jiragen sufuri a fadin kasar.

An dakatar da sufuri a yankin

Wasu manyan kamfanonin sufurin jiragen sama na duniya sun dakatar da zirga-zirga a wasu sassan Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Lufthansa na kasar Jamus ya ce ya dakatar da sufuri zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa a tsawon karshen mako, da kuma zuwa manyan biranen Isra'ila da Lebanon da Oman, har zuwa 7 ga watan Maris.

Haka nan ma kamfanin sufurin jiragen sama na Wizz Air shi ma ya dakatar da sufuri a Isra'ila da Dubai da Abu Dhabi da kuma Amman a Jordan har nan da 7 ga watan Maris.

Kamfanin sufurin jirage na Virgin Atlantic ma ya ce zai dakatar da sufuri ta sararin samaniyar kasar Iraqi na wucin-gadi, kuma ya soke tafiyarsa daga London zuwa Dubai a ranar Asabar.

Hukumar sufurin jiragen sama ta Kuwait ta ce za ta dakatar da dukkanin zirga-zirga zuwa Iran har sai abin da hali ya yi.

Wasu kasashen yankin - kamar Iraqi da Jordan su ma sun rufe sararin samaniyarsu. Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta "rufe wani bangare na sararin samaniyarta na wucin-gadi" domin yin kandagarki, kamar yadda kafar yada labarai ta gwamnatin kasar ta ruwaito.

Za mu ci gaba da sabunta muku wannan labari.