Dalilan ADC na watsi da sabon jadawalin INEC

Lokacin karatu: Minti 2

Jam'iyyun adawa a Najeriya, sun fara mayar da martani kan sabon jadawalin da hukumar zaben kasar ta fitar dangane da babban zaben 2027.

Jam'iyyar adawa ta ADC ta bayyana rashin amincewarta inda ta koka cewa an tsara sabon jadawalin ne kawai don a mayar da 'yan'adawa saniyar ware a zaben da ke tafe.

Daya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC Faisal Kabir, ya shaida wa BBC cewa, sabon jadawalin da INEC ta fitar, kamar wani tarko ne gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ta dala wa 'yan'adawa domin kada su samu damar fitar da 'yan takarkari.

"Misali sashi na 77, ya ce dukkannin jam'iyyun Najeriya ba za su tsayar da dantakara ba har sai sun tura wa Hukumar Zabe sunayen mambobin jam'iyyarsu da aka yi wa rijista ta hanyar intanet,"

"Abin damuwar a nan shi ne wata guda ya rage a rufe karbar sunayen 'yan jam'iyyar, yanzu ya za a yi jam'iyyun adawa su samu damar yi wa magoya bayansu rijista a cikin wata guda?''In ji shi.

Ya ce," Sai da jam'iyyar APC mai mulki ita kanta ta kwashi fiye da shekara ba ta kammala yi wa mambobinta rijista ta intanet ba, ya za a yi 'yan'adawa su yi a cikin wasu takaitattun kwanaki.?''

Mai magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya ce,"mu kawai muna gani kamar wani tarko ne aka dana wa jam'iyyun adawa don kada su samu damar fitar da 'yan takara."

" Sai bangare na biyu, shi ne sashi 82 na sabon kundin zabe, abin da yake nuna wa bai kai wata biyu ba zuwa uku ya rage a kammala fitar da 'yan takara tun daga matakin jiha har zuwa shugaban kasa, to ita jam'iyya mai mulki na da damar fitar da 'yan takararta a wannan lokaci da ya rage, ina ga mu 'yan adawa?"

"Muna ganin kawai an shirya hakan ne don kada jam'iyyun adawa su fitar da 'yan takara, dole majalisa ta koma ta bibiyi sabon kundin zaben da shugaban kasa ya sanya wa hannu don a ba wa kowacce jam'iyya dama don haka dimokradiyya ta ke babu wanda ya fi wani." In ji Faisal.