Man Utd da Man City na hamayya kan Anderson, ina Griezmann zai tafi?

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City da Manchester United na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson daga Nottingham Forest yayin da ɗanwasan ya kasance wanda ƙungiyoyin biyu ke son ɗaukowa a bazara. (Mirror)

Inter Milan ta nuna buƙatar ɗanwasan tsakiya na Liverpool Curtis Jones, mai shekara 25 a Janairu, inda ɗanwasan ke shiga shekararsa ta ƙarshe a Anfield. (Corriere dello Sport - in Italian)

Aston Villa ce kan gaba wajen farautar golan Manchester City James Trafford, kamar yadda Leeds United da Newcastle United da Tottenham da West Ham ke sa ido kan golan ɗan Ingila. (Teamtalk)

Kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Michael Carrick ya nuna cewa ɗanwasan baya na Ingila Harry Maguire, da kwangilar shi za ta kawo ƙarshe a bazara, za a ma shi tayin sabuwar yarjejeniya. (Guardian)

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya ce bai san abin da zai faru ba kan makomar ɗanwasan gaba na Faransa Antoine Griezmann, yayin da ake alaƙanta ɗanwasan mai shekara 34 da ƙungiyar Orlando City. (ESPN)

Daraktan wasanni na Barcelona Deco ya ce babu wata tattaunawa kan ɗanwasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, wanda kuma ake alaƙantawa da Arsenal. (Mirror)

Liverpool ba ta son sayar da golanta Alisson a bazara duk da buƙatarsa da Juventus ta nuna. (Football Insider)

Chelsea tana da yaƙinin ba za ta sayar da ɗanwasanta na Ingila Cole Palmer mai shekara 23 da wasu manyan ƴanwasanta ba duk da hasarar da ta yi ta fam miliyan 355 a kakar 2024-25. (Standard)