Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sola na iya haifar da gobara?
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, wanda aka fi sani da 'solar' na ci gaba da samun karɓuwa a ƙasashen Afirka masu tasowa, inda ake fama da ƙarancin lantarki.
A Najeriya lamarin ya zama ruwan dare a sassan Najeriya sakamakon rashin tabbas ɗin samun lantarki daga babban layin wuta na ƙasar.
Fiye da mutane miliyan 80 na fuskantar rashin wutar lantarki a sassan Najeriya, kuma ko waɗanda ke da wutar ma suna fuskantar katsewarta akai-akai.
Wani bincike na Energy Tracker a shekarar 2024 ya ce Najeriya na da kusan megawatt 385.7 na makamashin hasken rana, bayan da ta ƙara da megawatt 63.5 a shekarar, abin da ya sa ƙasar ta zama ta huɗu a nahiyar Afirka wajen amfani da makamashin hasken rana.
Amma a tatare da wannan ci gaba da ake samu akwai bukatar samun ingantattun bayanai kan irin matakan kiyayewa hadurra da za a iya amfani da su domin kare kai daga bala'o'i da kan iya tasowa sanadiyyar amfani da tsarin, wanda ke ci gaba da samun karɓuwa.
A baya-bayan nan an riƙa zargin akwai yiwuwar wutar sola ce ta haifar da gobara a kasuwar Singa da ke Kano, inda aka yi asarar dukiya mai ɗimbin yawa, duk da dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.
Ko da gaske gobara na iya tashi sanadiyyar sola?
Abubuwan da ka iya haifar da gobarar Solar ?
Masanin harkar makamashi a Najeriya Injiniya Mustapha Habu Ringim ya ce 'solar' na iya yin sanadin tashin gobara, sai dai ba haka nan kawai take kamawa da wuta ba sai dai idan an samu tangarɗa wurin aikin haɗa solar tun farko. Ya kuma zayyano abubuwan da ke iya janyo gobarar solar da suka haɗa da:
Amfani da kayan aiki marasa inganci: Masanin ya yi nuni da cewa rashin amfani da ingantattun kayan aiki shi ne ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke janyo gobarar sola, inda ya ce ''Akwai kayan aiki kamar su batura marasa kyau waɗanda ka iya fashewa yayin da ake aiki da su, saboda yana yiwuwa sun riga sun wuce lokacin aikinsu.''
Ya ƙara da cewa, baya ga batur, su kansu allunan solar da ake ɗorawa a rufin gida na iya janyo gobara idan ba a sanya masu inganci ba, musamman idan aka bi arha aka yi amfani da allunan da aka riga aka yi amfani da su a ƙasashen waje waɗanda akwai yiwuwar wa'adin aikinsu ya riga ya wuce.
Rashin amfani da ƙwararrun ma'aikata: Injiniya Habu Ringim ya yi bayanin cewa dole ne sai ma'aikaci ya samu ƙwarewa kafin ya iya sanin yadda zai haɗa kayan aikin ta yadda ba za su haifar da hadari ba.
''Akwai wasu kayan kariya da ake haɗawa da kayan solar, waɗanda ke taimakawa wurin kiyaye aukuwar gobara da sauran munanan abubuwa, dole sai ya san dokokin da wannan aiki ya ƙunsa ta hanyar samun horo daga wani ƙwararre na wani lokaci.''
Masanin ya ƙara da cewa ko da kayan da aka yi amfani da su na da inganci ana iya samun matsala sakamkon rashin ƙwarewa wajen haɗa su.
Yanayi: Masanin ya yi bayanin cewa,na'urorin sola, musammamn batura na buƙatar su kasance a wuri da za su riƙa samun iska domin zafin da suke yi na iya janyowa su kama da wuta ko kuma su fashe kai-tsaye.
''Batura da ake amfani da su na buƙatar iska, don haka idan aka ce an sanya shi a cikin ɗakin da iska ba ya shiga, akwai yiwuwar za su iya kamawa da wuta. Kuma babu abin da mu ke kira 'maintenance' a turance, ba a duba yanayin waɗannan na'urorin domin a tabbatar cewa suna aiki yadda ya kamata an kuma sanya su a wuraren da suka dace ba,'' in ji shi
Bugu da ƙari Injiniya Mustapha Habu Ringim ya yi watsi da iƙirarin da ake yi cewa ƙurar da ke taruwa kan allon sola na iya haifar da gobara, inda ya ce wannan iƙirari ba shi da tushe a kimiyance. ''Ƙura ba makamashi ba ce, ba ta kama wuta, babu yadda za a yi a ce gilas ɗin allon ne zai yi zafi ya kuma sa ƙura ta kama wuta. Asali ma ita kurar takan hana allon samar da isasshiyar wuta ne, saboda haka ban san inda suka samu wannan ilimin ba.''
Yadda za a kauce wa aukuwar gobarar sola
Masana dai sun tabbatar da cewa fahimtar abubuwan da ke haifar da gobarar sola da bin matakan kariya na iya matuƙar rage haɗarin gobara. Kuma injiniya Habu Ringim ya bayyana wasu hanyoyin da za a bi domin guje wa aukuwar gobarar sola:
- Amfani da ingantattun kayan aiki.
- Samun ƙwararrun ma'aikata da ke aikin haɗa sola.
- Amfani da na'urorin da ke iya kiyaye karfin wutar da ake samarwa.
- A tabbatar da cewa an sanya batura a wurin da za su iya samun iska.
- A tanadi kayan kashe gobara a kusa da inda na'urorin suke.
- A samar da hukumar da za ta kula da harkar sola a ƙasa.
- A riƙa duba nu'urori ana yi musu gyara akai-akai.