Trump ya ce an kashe jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa an kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

A cikin saƙon, Trump ya ce "wannan adalci ne ba ga al'ummar Iran kawai ba, har da Amurkawa, da kuma al'ummar ƙasashen duniya waɗanda Khamenei da ƴan korensa suka kashe ko suka azbtar.

"Ya gaza zulle wa bayanan sirrinmu da kuma fasaharmu ta bibiya, tare da aiki kafaɗa da kafaɗa da Isra'ila, babu wani abu da shi, ko sauran jagororin da aka kashe tare da shi suka iya yi.

"Wannan ce babbar dama ga al'ummar Iran su sake karɓe iko da ƙasarsu.

"Amma gagarumin luguden wuta na ɗauki ɗaiɗai zai ci gaba, ba tare da ƙaƙƙautawa ba a tsawon mako ko kuma har zuwa lokacin da ya kamata domin cimma manufarmu ta zaman lafiya a faɗin Gabas ta Tsakiya da duniya baki ɗaya."

Babu wani bayani daga hukumomin Iran da ya tabbatar da kashe Kahmenei, inda wasu kamfanonin dillancin labaru na kasar suka ce yana ”cikin koshin lafiya” bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar.

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa Isra’ila da kuma kasashe hudu na yankin Gulf wadanda akwai sansanonin sojin Amurka a cikinsu: Bahrain, Kuwait, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wane ne Ayatollah Khamenei?

Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.

Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.

Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.

Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Haihuwa da yaruntar Khamenei

An haife shi ne a garin Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran a shekarar 1939.

Shi ne na biyu a wurin mahaifansa masu ƴaƴa takwas, kuma mahaifinsa ya kasance malamin Shi'a.

Ya fara karatu ne da koyon karatun Ƙur'ani tun yana ƙarami, inda ya zama malami yana da shekara 11.

Duk da cewa yana daga cikin masu bayar da fatawa kan al'amura, a yanzu haka za a iya cewa aikinsa ya fi tasiri a siyasance.

Khamenei mutum ne da Allah ya yi wa baiwar iya tsara magana sosai, kuma ya kasance kan gaba wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran, sarkin da aka hamɓarar a juyin juya-halin ƙasar.

Yawancin rayuwar Khamenei ta kasance a ƙarƙashin ƙasa ne ko a gidan yari. Sau shida ana kama shi a zamanin mulkin Shah, inda ya fuskanci uƙuba.

Shekara ɗaya bayan juyin juya-hali a 1979, sai Ayatollah Ruhollah Khomeini ya naɗa shi babban limamin Juma'a na birnin Tehran.

Daga baya sai aka zaɓe shi a matayin shugaban ƙasa a 1981, kafin shugabannin addinin ƙasar suka zaɓe shi a shekarar 1989 domin ya maye gurbin Ayatollah Khomeini, wanda ya rasu yana da shekara 86.

Iyali

Ali Khamenei bai cika fita ƙasashen waje ba - yana gudanar da ƙaramar rayuwa ne a tsakiyar Tehran tare da maiɗakinsa.

An ce yana son rubutacciyar waƙa da lambu. Khamenei ya samu matsala a hannunsa na dama a wani yunƙurin kashe shi da ya tsallake a shekarun 1980s.

Shi da maiɗakinsa, Mansoureh Khojasteh Baqerzadeh suna da yara shida - maza huɗu da mata biyu.

Ba kasafai ake ganin iyalan Khamenei ba, kuma babu takamaimen bayani game da rayuwarsu.

A cikin yaransa, akwai Mojtaba, wanda shi ne na biyu, wanda ya fi fice, kuma ya fi taka rawar gani a harkokin jagoran.

Ƴaƴansa mata biyu

Babu bayanai sosai game da ƴaƴansa mata biyu.

Bushra da Hoda ne ƙanana a cikin yaran, kuma duk an haife su ne bayan juyin juya-hali na 1979.

An haifa Bushra a 1980 kuma tana auren Mohammad-Javad Mohammadi Golpayegani, ɗan Gholamhossein (Mohammad) Mohammadi Golpayegani, wanda shi ne shugaban ma'aikatan ofishin Khamenei.

Hoda, wadda ita ce autar gidan baki ɗaya an haife ta ne a 1981. Tana auren Mesbah al-Hoda Bagheri Kani, wanda ya karanci kasuwanci kuma yake koyarwa a Jami'ar Imam Sadiq University.