Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran ta tabbatar da kisan Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila
Gwamnatin Iran ta tabbatar da mutuwar Ayatollah Khamenei, bayan ikirarin farko da shugaba Donald Trump ya yi na kisan jagoran addinin a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai a sassan kasar Iran.
A sanarwar da kafar yada labaran Iran ta sanar, ba a bayyana yadda aka kashe jagoran addinin ba da kuma wanda zai gaje shi.
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce ta tabbatar da mutuwar Khamenei tana mai zargin Amurka da Isra'ila, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ce shahadar Khamenei za ta kasance mafarin "yaki da azzalumai".
Sanarwar ta kara da cewa an kashe Ayatollah Khamenei ne da safiyar Asabar a ofishinsa.
Tun da farko kafar yada labaran kasar ta tabbatar da mutuwar yarsa da surikinsa da kuma jika a hare-haren na Amurka da Isra'ila.
A cewar kamfanin dillacin labarai na Fars da ke kusanci da dakarun juyin juya hali na Iran, akwai rahotannin da ke cewa akwai surukar Khamenei cikin wadanda aka kashe.
Kafar talabijin ta Iran ta bayar da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki a Iran da kwana bakwai na hutu domin jimamin mutuwar jagoran na Iran Ali Khamenei
Iran ta sanar da cewa shugaban kasa da shugaban harakokin shari'a, - za su jagoranci nada sabon jagora bayan rasuwar Ayatullah Ali Khamenei.
An zabi Khamenei ne a ranar da Ruhollah Ayatollah Khomeini ya rasu.
Wane ne Ayatollah Khamenei?
Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.
Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.
Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.
Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).
An haife shi ne a garin Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran a shekarar 1939.
Shi ne na biyu a wurin mahaifansa masu ƴaƴa takwas, kuma mahaifinsa ya kasance malamin Shi'a.
Ya fara karatu ne da koyon karatun Ƙur'ani tun yana ƙarami, inda ya zama malami yana da shekara 11.
Duk da cewa yana daga cikin masu bayar da fatawa kan al'amura, a yanzu haka za a iya cewa aikinsa ya fi tasiri a siyasance.
Khamenei mutum ne da Allah ya yi wa baiwar iya tsara magana sosai, kuma ya kasance kan gaba wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran, sarkin da aka hamɓarar a juyin juya-halin ƙasar.
Yawancin rayuwar Khamenei ta kasance a ƙarƙashin ƙasa ne ko a gidan yari. Sau shida ana kama shi a zamanin mulkin Shah, inda ya fuskanci uƙuba.
Shekara ɗaya bayan juyin juya-hali a 1979, sai Ayatollah Ruhollah Khomeini ya naɗa shi babban limamin Juma'a na birnin Tehran.
Daga baya sai aka zaɓe shi a matayin shugaban ƙasa a 1981, kafin shugabannin addinin ƙasar suka zaɓe shi a shekarar 1989 domin ya maye gurbin Ayatollah Khomeini, wanda ya rasu yana da shekara 86.