Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ke fama da cutar da ke sanya mutane tsukewa
- Marubuci, James Diamond
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, West of England
- Lokacin karatu: Minti 2
Rayuwar wata mata da ta ce ya kusa zuwa ƙarshe jim kaɗan bayan gano tana ɗauke da wani nau'in ciwon hanta, ta faɗi labarinta don ƙarfafa wa mutane gwiwar cewa kada su sare.
Lokacin da Caroline mai shekara 63, daga birnin Wiltshire ta je wurin likita don duba ta sakamakon kaikayin ido da take fama da shi, ba ta taɓa tsammanin cewa alama ce ta na'uin cutar hanta mai haɗari.
Albarkacin ranar irin wannan nau'in cuta, a yanzu ta fito tana magana kan yadda ta yi fama da cutar domin wayar da kan al'umma yadda za su kare kansu da kuma tasirin da za su iya yi.
"Idan na duba baya, ba zan iya misalta abin da ya faru ba kasancewa har yanzu ina nan," in ji ta.
Kafin a yi mata aikin dashen hanta, alamominta sun yi tsanani har ta kai ta koma amfani da keken guragu bayan fama da tarin gajiya, kasala da kuma matsalar kwakwalwa, amma ta ce tana bayar da labarinta ne domin karfafawa sauran mutane da ke cikin yanayin da ta taɓa tsintar kanta cewa kada su karaya.
'Sau ɗaya a cikin shekara 10'
Labarin Caroline ya fara ne a shekara ta 2018 a gida lokacin da take kallon talabijin, lokacin da gefen idonta ya fara mugun kaikayi.
"Ban taɓa jin haka ba," in ji ta, inda daga baya aka gano tana ɗauke da wata cuta da ya shafi wani ɓangare na idonta.
Sai dai a 2019 idonta da kuma fatarta sun koma ruwan ɗorawa, wato wani na'ui na cutar hanta wanda likitoci suka ce sau ɗaya ake samun irinsa a cikin shekara goma.
An ɗauki tsawon watanni shida kafin a yi wa Caroline aikin dashen, inda matsala da ta samu a lakarta saboda magani ya janyo tsayinta ya ragu daga kafa 5.4 zuwa kafa 4.6.
Shekaru shida bayan nan, yanzu idanunta da kuma hantar ta sun koma aiki yadda ya kamata, har ma tsawonta ya koma kafa 5.
Ta faɗa wa BBC cewa sakonta ga mutane shi ne kada su taɓa "sare wa".
"Jikin ɗan'adam na da alfanun gaske," in ji ta.
A cewar asusun tallafawa masu cutar hanta ta Birtaniya, ta ce dubban mutane a ƙasar na rayuwa da na'uin cutar hantar da ba a saba gani ba, wanda yawanci kan ɗauki shekaru saboda rashin wayar da kai da kuma ƙarancin bincike a ɓangaren.
Shugara asusun, Pamela Healy, ta ce yayin da nau'in cutar ya kasance ba shi da yawa, amma zai iya yin tasiri mara kyau ga rayuwar mutum.
"Yawanci rashin wayar da kai na janyo cikas wajen yin gwaji da kuma samun kulawar da ta kamata," in ji ta.
"Muna buƙatar ƙarin sanayya, gwaji da wuri da kuma ɗimbin bincike don tabbatar da cewa babu mai fama da na'uin cutar hantar da aka bari a baya."
Ana bikin tunawa da ranar irin wannan na'uin cutar ce a kowane ƙarshen watan Fabrairu, don wayar da kan mutum sama da miliyan 300 a faɗin duniya da ke fama da matsalar.