Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ƙungiyoyin ƙawancen Iran za su iya shigar mata a yaƙi da Amurka?
- Marubuci, Saeed Jafari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Iran analyst
- Lokacin karatu: Minti 7
Yayin da yaƙi ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran da kuma Isra'ila a ɗaya gefen, ana fargabar ɓarkewar yaƙi a ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya.
Da safiyar ranar Asabar ne ha din gwiwar Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare a wasu biranen Iran, ciki har da Tehran, babban birnin ƙasar.
To sai dai nan take Iran din ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa cikin Isra'ila da kuma kan sansanonin sojin Amurka a wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
A tsawon gomman shekaru, Iran ta ɗauki aniyar faɗaɗa tsaronta ta hanyar mallakar makaman linzami, na'urorin kakkaɓe hari ta sama da kuma tsaron cikin gida, har ma da samun ƙarfi na yanki.
Ƙawance da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a Lebanon da Iraqi da Syria da kuma Yemen, ya kasance ɗaya daga cikin tsarin tsaronta - wanda aka bayyana a matsayin wani salo na yaƙi.
Wannan ba wani yaƙi bane na kai-tsaye ba kuma na zaman lafiya ba, illa ta matsin lamba, barazana da kuma musanta hare-hare da aka kai waɗanda ke lahani ga abokan gaba amma ba tare da ta janyo wani gagarumin rikici ba.
Sai dai, tun ranar 7 ga Oktoban 2023, Isra'ila ta afka wa yawancin waɗannan ƙungiyoyi - musamman waɗanda ke alaƙa da Iran, sannan ta zarce kan wuraren Iran a faɗin yankin har ma da cikin ƙasar - a wani yunkuri na fitar da Tehran daga "wurin da ba a so" zuwa cikin wani yanayi mai wahala da zai saka su zaɓi miƙa wuya ko kuma shiga yaƙi.
A wannan lokaci, an yi wa ƙungiyoyin da ke ƙawance da Iran a yankin mummunan lahani.
Sai dai ba a kai ga ƙarya lagon waɗannan ƙungiyoyi gaba-ɗaya ba.
A nan, mun yi duba kan wasu ƙungiyoyi uku da ke ƙawance da Iran - Hezbollah a Lebanon, Shia a Iraqi da kuma ƴan Houthi a Yemen - da kuma irin rawar da za su taka a rikicin Iran da Amurka.
Hezbollah a Lebanon: Har yanzu tana da tasiri duk da rage ƙarfinta
A tarihi, Hezbollah ta kasance babbar ƙawar Tehran a Gabas ta Tsakiya, saboda ƙarfin soji da kuma makaman da take da shi, da kuma irin rawar da ta taka a siyasar Lebanon a tsawon shekaru.
Sai dai, yanayin da Hezbollah ke ciki a yanzu ya sha bamban da na baya.
Da alama yaƙi da Isra'ila da kuma bayanan sirri sun janyo rugujewar tsarin gudanar da ƙungiyar da kuma rage ƙarfinta.
Kisan Hassan Nasrallah, ya jawo giɓin shugabanci kuma hakan ya sa dole a sake zama don ganin irin matakai da ƙungiyar za ta riƙa ɗauka.
A lokaci guda, yanayin da Lebanon ke ciki - rugujewar tattalin arziki, matsin lambar al'umma,
A sa'i daya kuma, halin da ake ciki na cikin gida na kasar Labanon - tabarbarewar tattalin arziki, matsin lamba na al'umma, da kuma yadda al'ummomin da ba 'yan Shi'a ke kallon idan wani sabon yaƙi ya ɓarke - sun ƙara dagula wa kungiyar Hezbollah damar shiga wani yaƙi.
'A Lebanon, duk wani yunkuri na taimakawa Iran ba zai kasance abu mai sauki ba," kamart yadda wani jami'i a wata cibiya a Gabas ta Tsakiya, Michael Young ya faɗa wa BBC.
"Ƙarfin da Hezbollah ke da shi yana da iyaka. Tana cikin wani yanayi na ita kaɗai, kuma mutane da dama a yankin na adawa kan shiga wani yaƙi."
Ya ƙara da cewa idan Hezbollah za ta ɗauki matakai masu zafi, na amfani da makaman linzami kan Isra'ila, martanin ƙasar ba zai yi kyau ba - abin da zai janyo babbar matsala a Lebanon.
Sai dai Hezbollah ba za ta so shiga dumu-dumu ba idan yaƙi ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, aƙalla ba kwanakin farko na fara yaƙi ba kuma ba ta hanyar da zai jawo mamaya a Lebanon ba.
Har yanzu ƙungiyar na da ƙarfi kan abin da za ta iya aikatawa, musamman na amfani da jirage marasa matuki da kuma makaman linzami. Amma shiga cikin yaƙin dumu-dumi zai janyo barazana ga ɗorewar ƙungiyar da kuma jefa Lebanon cikin babbar barazana.
Wani ƙwararren mai sharhi a wata cibiya a Brussels, Kawa Hassan, ya shaida wa BBC cewa Hezbollha za ta iya amfani da wata hanya ta daban idan ta ga cewa hare-haren Amurka na barazana ga ɗorewar Jamhuriyar Musulunci.
"Babban batu shi ne idan suka ga cewa gwamnatin Iran na fuskantar barazanar ɗorewa, to za su iya kawo ɗauki yadda ya kamata, a nawa ra'ayi," in ji shi.
Hakan kuma ya yi daidai da irin martanin da wani jami'in Hezbollah ya yi a tattaunawa da AFP rana Laraba, inda ya ce ƙungiyar ba za ta yi martani ba idan harin Amurka a Iran ya kasance ba shi da yawa, amma za su ɗauki duk wani hari kan jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei a matsayin keta layi na karshe.
Ƴan Shia a Iraqi: Masu ƙarfi da jajircewa
Tsarin ƙungiyoyi da Iran ke ƙawance da su a Iraqi ya sha bamban da na Hezbollah a Lebanon, musamman ma a wuraren ɗaukar mataki - kuma suna da jajircewa wajen faɗa.
Ana damawa da wasu ƙungiyoyi irinsu Popular Mobilization Forces, musamman ma a haɗakar siyasa yayin da wasu kuma ke kasancewa masu zaman kansu.
A tsawon shekaru, waɗannan ƙungiyoyi sun saka buri kan abubuwa biyu ne: Ci gaba da ɗaɓbaka manufarsu a yankin na "Ƙawancen gwagwarmaya" da kuma ƙara ƙarfafa matsayarsu a siyasar Iraqi.
Yayin da goyon bayansu ga Tehran ya ci gaba da wanzuwa kuma jami'an Iran suka ci gaba da ziyara ga shugabanninsu lokaci zuwa lokaci, wasu mayaƙan Shia sun mayar da hankali kan samun iko a cikin gida, samun matsaya a tsarin siyasar Iraqi da kuma cimma wasu manufofin zaɓe.
Ƙungiyoyi da dama da ke alaƙa da Iran sun samu nasara a zaɓen ƴan majalisa a 2025, kuma yanzu da su ake damawa a tsarin ikon Iraqi. Wannan zai janyo su yi sako-sako da shiga duk wani rikici, saboda suna ga za su iya rasa kujeru a majalisa da kuma mukaman gwamnati.
Ƙwararre Michael Young ya bayyana cewa Iraqi da Lebanon sun bambanta saboda kasancewar sansanonin sojin Amurka a Iraqi, kuma a duk wani mataki na wucin gadi da Amurka za ta ɗauka, Tehran ba za ta samu damar haɗa ƙawancenta duka ba.
Kawa Hassan ya ce akwai yiwuwar far wa yankin Kurdistan na Iraki, wanda yanki da wasu ƙungiyoyi ke ganin yana da saukin afkawa - wadda a baya suke far wa don aika sako ga Washington.
Ƴan Houthi: Jajirtattu kuma babu tsoro
Masu sa ido da dama na ganin cewa ƴan Houthi na gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba fiye da sauran ƙungiyoyin biyu, ba wai saboda suna da ƴanci daga Tehran ba, illa saboda ba su fuskantar irin matsalolin da Lebanon ke ciki ko kuma irin na Iraki.
Tsarin Yemen ya bai wa Houthi damar shafar kasuwanci da kuma makamashi a duniya a shekarun baya-bayan nan. Ƙungiyar ta kama jiragen ruwan dakon kaya da kuma janyo cikas na harkar tafiye-tafiye a Bahar Maliya da kuma mashigar Bab al-Mandab, wata hanya mai tsawon kilomita 32 da ta raba arewa maso gabashin Afirka da yankin Larabawa.
Houthi za su kasance waɗanda za su fi bayar da gudummawa ga Iran idan yaƙi ya ɓarke tsakaninta da Amurka saboda ba su fuskantar matsin lambar siyasa a cikin gida. Da wuya a iya hana su aiwatar da abin da suke so kamar yadda aka sha gani a baya - ko da za a kai musu hari ta sama ne - kuma damar su na hana jiragen ruwa tafiye-tafiye ya ƙara ba su wani iko a duniya.
"Ƴan Houthi na da zaɓi daban-daban," a cewar Michael Young. "Tuni suka fara janyo tasiri a katsalandar da suke yi wa zirga-zigar jiragen ruwa kuma za su yi koƙarin toshe mashigar Bab al-Mandab."
Iran za ta duba yiwuwar rufe mashigar Hormuz, a cewar Young, inda ya ƙara da cewa abin da Iran za ta yi zai danganci yadda ta ɗauki yaƙin.
Idan Tehran ta ga cewa burin Washington (har ma da Isra'ila) shi ne kifar da gwamnati, to ba za ta yi wata-wata ba wajen haɗa dukkan ƙawayenta domin mayar da martani.
Idan aka kai ga matakin, akwai yiwuwar rufe mashigar Hormuz da kuma yunkurin Houthi na toshe mashigar Bab al-Mandab.
Tunani kan ɗorewa
Masu sa ido da dama na ganin cewa ƙungiyoyi da Iran ke ƙawance su za su iya mayar da martani nan take bayan far wa Tehran.
Sai dai Kawa Hassan ya ce za a mayar da martani ne kaɗai idan aka ga ana barazana ga ɗorewar ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa a wannan yanayi, wasu ƙungiyoyi za su iya far wa Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ko kuma Kuwait, abin da zai janyo saɓani tsakanin Iran da ƙasashen na yankin Gulf.
Michael Young ya karkare da cewa babban burin gwamnatin Iran ita ce samun tsira.
Duk wani yunkuri na yin barazana ga ɗorewarta zai janyo babban martani mara kyau, amma idan babu wata barazana kan haka, Iran da ƙawancenta ba su mayar da wani martani na a zo a gani ba.